Babi na arba'in da biyar

8.9K 915 53
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa asa an takrahu shai'an wa huwa khairul lakum,wa'asa an tuhibbu shai'an wa huwa sharrul lakum,wallahu ya'alamu wa antum la ta'alamun*

*_SAU DA YAWA ZAKU QI ABU AMMA ALKHAIRI NE A GURINKU,SAU DA YAWA ZAKU SO ABU AMMA SHARRI NE A GURINKU,HAQIQA ALLAH SHINE YA SANI AMMA KU BAKU SANI BA_*

______________________________

*ZAINAB*

Kamar yadda suka tsara ita da zinatu hakan ce ta kasance,qarfe goma na safiyar washe gari a gidan malam ta yi musu,duk da dan uban ciwon da jikinta ke mata amma sam bata kula ba,burinta kawai ta ganta gaban malam din,da yake safiya ce bata taras da mutane da yawa ba a gidan mutum daya ne ya fito suka shiga.

Kamar ko yaushe mutumin da suke kira da malam ya kuma shiga rigar malamai yayi bake bake yana zaune kan buzu,yaci babbar riga da rawani gefe litattafan addini jere wadanda ko zaka kasheshi layi guda bazai iya karantawa ba balle har ya iya gane me ya karanta din.

"Zainabu abu,ina fata buqata ta biya don na ina nan ina ta kewarki,ban manta daren mu ba na......"
"Dakata dalla malam,ni zaka yaudara?,kayimin aikin banza lalataccen aiki da tunda na fara yawon bin malamai ba'a taba min matsiyacin aiki irinsa ba,to wallahi da sake bazai yiwu ba"turbune fuska yayi ainun yana dubanta
" ke kisan fa agaban wa kike,bana son tsiya"sake harzuqa tayi tana cewa
"Eh dole mana ka fadi haka,bayan ka gama amfana da albakatun jikina ko?"
"Ke sha shashasha,ai ba kanki farau ba,kuma ke kika kawo kanki,dama tunda kika rabu da Allah babu irin qazantar da ba zaki fada ba,kinga ki fadamin abinda ke tafe dake kada ki batamin lokaci customers na tafe a hanya kada ki bata min aiki" cikin masifa ta sake takowa gabansa tana dubansa
"Amma malam bansan kai ba qaramin dan akuya bane sai yau,to wallahi baka isa kaci bulus ba,ni babu wanda ya isa ya takani wallahi na qyaleshi ban dau fansa ba ko uban waye kuwa" dariya ya barke da ita ya dinga qyaqyatawa har suka saki baki suna kallonsa
"Saidai cin bulus na gaba,bulus kuma ai na gama cinta tunda na hadaki da CUTA MAI KARYA GARKUWAR JIKI?" wata saukar guduma sukaji bisa kawunansu,ba zainab kadai ba hatta da zinatu
"Cuta mai karya garkuwar jiki!" Zainab ta tambayeshi cikin qaraji,dariyarsa ya ci gaba da yi yana kada kai
"Qwarai kuwa,wannan tsaraba ce da muke baiwa dukkan macen data bijirewa Allah,ta zabi biyan buqatar duniyarta akan ta lahira" sulalewa kawai tayi a gun,zinatu ta fasa kuka tayi kanta,ganin suna neman tara masa jama'a ya sanyashi samo mai adaidata sahu ya dorasu ya saita musu hanyar asibiti.

*MUKHTAR*

Tun ranar da sirrin ya yaye masa baki daya ya sauya,tamkar ba mukhtar ba,hatta da abdallah sai da ya samu sauyi da naqasu wajen kulawar da yake samu,ya kusa wata bai zuwa ko ina yana gida,sai abdallah ya matsa da rigima yake fita waje ya dan tattaka da shi a qafa ya dawo,babu abinda ke bijiro masa sai tausayin sumayya da tunanin da wanne ido zai kalleta?,ko wane minti daya tana dawo masa ne da irin abubuwan da ya aikatawa sumayyan,tun daga auren zainab zuwa ranar rabuwarsu,wasu abubuwan gani yake tamkar a mafarki suka faru ba a zahiri ba,kuka kam ya yishi sau babu adadi,baisan iyaka ba,yana so yaje ya warwarewa su malam komai amma yana jin wata 'yar banzan kunya da nauyinsu wadda a da bai jita ba,kusan ya mance kwanansa nawa rabonshi da gidan,saidai ya zame masa dole yaje gidan don sauke nauyin dake kansa.

**** ****** *****

Zaune take gefan gado sanye da hijabinta tana ci gaba da sharce hawaye,tsahon kwana biyu da faruwar lamarin amma ta kasa tsaida hawaye a idanuwanta wanda ita kanta ta rasa dalilin haka,kukan nata ya dadu ne tun bayan gama wayarsu da anty dije wadda kejin tamkar a kanta hakan ya faru.

Halima ce ta shigo dakin
"Yaya sumayya kije inji malam" jikinta ya qara sanyi a zatonta magana a kanta ne bata qare ba,duk da cewa babu abinda ya fada face yi mata addu'a bayan ya gama saurarar rayuwarta a gidan mukhtar,fada daya yayi mata na rashin neman taimako daga wanda tasan ya fita gogewa da sani kan irin wadan nan lamuran,al'amura ne da kake buqatar addu'a koda daga wajen iyayenka ne daga bakunansu,tunda addu'ar tasu karbabbiya ce a wajen ubangiji.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now