Babi na casa'in da uku

16.2K 1.3K 348
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya Allah ka sanya farinciki a zukatan musulmai,ya Allah ka wadatar da talakawan cikinsu,ya Allah ka qosar da duk wanda ke cikin halin yunwa,ya Allah ka dawo da matafiyanmu lafiya,ya Allah wanda bashi ya masa yawa ka biya masa,ya Allah ka tufatar da wanda ke cikin tsiraici,ya Allah duk wanda ke da mummunan hali cikin musulmi ka gyara mana halayyarsa,ya ubangiji dukka wanda yake cikin tsananin baqinciki ka yaye masa*

*ya Allah*

*ka fada cikin qur'aninka mai girma*

*idan bayina suka tambayeka game da ni kace musu lallai ni makusanci ne*

*ya Allah*

*kai kayi umarni da mu roqeka(zaka amsa mana),ka kallafawa kanka amsawa(addu'ar bayinka),ya ubangiji ka amsa mana,ka biya mana dukkanin buqatunmu,ka cika mana burikanmu ya ARHAMAR RAHIMIN*
_____________________________________




         Ya jima zaune saman table din office din yana duba yadda ta shigar da komai a tsare,wani abun ma da shi bai taba yunqurin dubashi ko shigar da shi ba,murmushi ne keta fita a fuskarshi,ya dauke idanunshi sanda ta fito daga bandaki bayan ta daura alwala zata tada sallah,da kallo yake binta,yana jin cewa ya samu wata babbar kyauta ne daga Allah,cikin watanni Allah ya sauya rayuwarshi sauyin da bai taba zaton akwaishi ba.

        Har ta sallame sallar yana zaune yana dubanta,sai ya miqe ganin ta gama yana daukan hularshi wadda tun dazun yake cireta yana riqeta a hannu saboda rashin sabo
"Lets go,muje muyi lunch" ya fada yana dubanta,ta shafa addu'an ta waiwayo,cikin shagwaba tace
"Kashe kudi ko?,muna da komai a gida muje na dafa maka wani abun" kai ya girgiza
"Gida?,ba yanzu ba,ba yanzu zamu koma ba",bata sake tankawa ba juya ta janyo jakarta ta bude,ta fidda qaramar hoda ta gyara fuskanta,ta ciro turarenta ta matsa a hannunta ta goge jikinta da shi,yana daga tsaye qamshin ke dukanshi,sai ya tako ya tsaya a bayanta,ya riqe hannunta dake riqe da turaren yakai hancinsa,lumshe idanu yayi
"I love iy,ina son wannan qamshin" murmushi ta saka,ta maida turaren jaka suka jera suka fito.

        Tafiya ta wasu mintuna suka qaraso qofar katafaren wajen cin abincin,wajen cin abinci ne da kusan duk wanda ke garin yasan da zamansa,domin yana dacewa da duk yanayin da kake so,kaman almustapha da baisom cin abincin cikin jama'a,yakan kama waje na musamman wanda yake kaman VIP,saidai yana da tsada fiye da sauran guraren,qofar shigar wajen ma na musamman ne kamar yadda kujeru da teburan wajen suma suke na daban.

         Daya daga cikin ma'aikatan wajen ne ya qaraso cikin rawar jiki,don ya tabbata yau sunyi babban kami,cikin girmamawa ya rusuna ya gaidashi,ya amsa sanda ya miqa hannu yana amsar na'urar dake hannunshi ya soma duba abubuwan da yau suke da shi,bayan ya zaba yawa can kitchen din sending na abinda yake buqata da number sit dinsu kamar yadda tsarin wajen yake sai ya tura na'urar gabanta,dubanshi tayi ya mata alama da idanu ta zabi abinda take so,maida idanuwanta tayi kai ba tare data taba ba tana qarewa list din kallo,haka kawai taji babu abinda ya bata sha'awa a ciki,hannunta yakai kan irin abinda yayi order itama ta dannan kawai ta daga wayan da niyyar miqawa ma'aikacin,almustaphan yahi saurin karba daga hannunshi ya miqa masa ya karba ya juya ya bar wajen,ya motsa bakinshi da niyyat cewa wani abu wayarshi ta soma ringing,sai ya fasa fadin abinda zaya ce din ya soma laluban wayarsa dake aljihun wandonshi duk da bai dauke idanunshi daga kanta ba,ta rasa wane irin kallo ke wannan duk sa'ad da suke tare,duk yadda taso ga yawaiya dubanshi idan suna tare ita kasawa take saboda nauyi da kunya,yana soma amsa wayar kamar hadin baki tata wayar ta dauki ringing,ta cirota a jakarta tana dubawa,halima amarya ce,murmushi ta saka cikin nutsuwa ta daga suka soma gaisawa,daga bisani ta miqawa abdallah dake kusa da ita,aifa nan ya dinga zuba yana bata labarai kala kala,harda labarin ya gama nursery one zai shiga nursery two,idanunta ta lumshe tana tasbihi ga Allah,ba shakka shekara kwana,a yanzu a qalla abdallah ya tasamma shekara biyar kenan,tun tana daurewa har ta biye masa ta dinga sakin qaramar dariya,abdallah badai wayo ba,hatta cikin halima sai da yace cikin mummy ta zama qato yace baby zata siyo mana sabuwa,sai data gaji sannan tace
"Baiwa mummyn to wayar,duka ka cinye mata credit" haliman ya miqawa sukayi sallama,ta kashe ta soma qoqarin maida wayar jaka
"Ummu abdallah" taji ya ambata a tausashe,daga kanta tayi tana dubanshi,sai yanzu ta lura,tunda ta fara wayan idanunshi na kanta,kunya ta dan kamata ta janye idanunta,qasa qasa yayi da murya tare da matsowa dab da ita
"Ya kamata nima a bani nawa abdallah haka.....i need him tunda an hanani wannan ko?" Kai ta sunne tana murmushi,ya bata kunya ba kadan ba salon yadda yayi maganar,dai dai da isowar ma'aikata biyu dauke da abincin nasu,suka ajjiye gabansu suka jiya suka wuce,ba bata lokaci ya warware spoon dake nannade ya sanya cikin abincin ya soma ci a nutse kuma a yangance,itama cokalin ta sanya saidai ta kasa kai koda loma daya bakinta,gaba daya abincin taji bai mata ba kuma,duk da yadda yayi kyau tun a ido balle a kai baki,yana ankare da ita,naman dake gefan abincin ta jawo ta cinyeshi tas,suna hada ido ta kau da kai,take kunya ta kamata,batasab me yasa ta yin haka ba,hannu ya daga ya kira wani ma'aikacin wajen da yazo kawowa wasu mata da miji da suka shigo yanzu wajen nasu order din
"Kuna da meat haka,gasashshe?" Cikin rusunawa yace
"Eh amma ranka ya dade ya qare saidai ko zata jira,amma akwai farfesun kayan ciki"
"Jeka kawo" ya fada yana yagar tissue ya gige bakinsa,komawa yayi ya jingina da kujera yana dubanta,duk sai kunya ta dabaibayeta
"Nifa bana ci" ta fada a dake
"Bake dama nace a kawowa ba" ya bata amsa yana ci gaba da nazarinta,mintina qalilan ya dawo dauke da bowl na tangaran mau kyau ya ajjiye sannan ya juya ya tafi
"Bude wannan bowl din ki dauka kici,bance kuma kice wani abu ba" ya qarashe maganarsa yana jan wayarshi yana dannawa cokalin ta ajjiye ta jawo bowl din ta bude,habawa wani yawu ta hadiya kaman mayya,farfesun kayan ciki ne hanta tumbi qoda sai zuciya,ajjiye murfin tayi ta saka cokali ta soma kaiwa baka,wani dadi ya ratsata,kaman ta dauka ta juye a cikinta ta huta da tauna haka ta dinga ji,ci kawai take ba kama hannun yaro,bata ankara ba sai ganim kwanon tayi babu komai saura romo,sai a sannan ta tuna da wanda ke gabanta,ta daga kai kamar munafuka ta saci kallonsa qasa qasa,ita kuwa yake kallo,mamakin yadda take cin abinci haka yau a gabanshi a sake yake yi,yayin da ita kuma take zaton naman da yaga tana ci ne,sai ta bata fuska ta janyo tissue din itama tana goge bakinta,kanshi ya dauke yana murmushi qasan ranshi
"Wai itama lallai bata son raini" ya fada a zuciyarshi yana miqewa,ma'aikacin ne ya sake dawowa,almustapha ya miqa masa atm card dinshi yace su cira kudinsu su kawo masa card din mota.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now