Babi na saba'in da biyu

13.8K 1.2K 490
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ALLAH YANA GAFARTAWA WANDA YASO YA KUMA AZABTAR DA WANDA YASO*

YA ALLAH KA GAFARTA MANA
___________________________________

*TAB,BIGI SAI BIGI,BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE,IDAN KAJI WANE BA BANZA BA,INA MA'ABOTA KARATUN LITATTAFAN HAUSA,KAMA DAGA NA QUNGIYAR HASKE HARMA WANDA BA NA HASKE BA,SHIN KUNA DA BUQATAR JIN WANI SABON KUNDI WANDA YA TATTARE LABARAI NAU'IN DABAN DABAN WADANDA SUKA SHAFI AL'AMURA NA ZAHIRI DAKE FARUWA CIKIN RAYUWARMU TA YAU DA KULLUM?.......TO MAZA KU GARZAYA KU NEMI LITTAFIN KUNDIN HASKE,WANDA KE QUNSHE DA LABARAI DAKE DAUKE DA NAU'IN RAYUWA IRI DABAN DABAN,LABARAI NE WANDA KE DAUKE DA DIMBIN DARUSSA MASU RATSA ZUKATA,DUMBIN ILIMI MAI JAWO HANKALIN DAN ADAM ZUWA SAKE LURA DA GYARAN RAYUWARSHI,MAZA KA/KI GARZAYA KADA A BAKI LABARI,BA SHAKKA ZA'A CI DA RABONKI MATAUQAR KIKA BARI YA WUCEKI,AKWAI SHI A WATSAPP DA APP DIN WATTPAD BAKI DAYA*

BABBAR GODIYA DA BABBAR MURYA GAREKU 'YAN WATPADD,BA SHAKKA KO WANNE COMMENT NA DAYANKU YANA DA MUHIMMANCI A GARENI,YANA QARAMIN QAIMI DA NISHADI QWARAI,RABBI YA BAR QAUNA.



       Kyawawan idanuwanshi wanda suka wadatu da gashin idanu kamar yadda girarsa take masu kama da na wanda ke jin bacci suke kan ta,shi daya ne tak sanye cikin qananun kaya sabanin dukka sauran wadanda suke tsaye tare,baki dayansu shadda ce jikinsu dinkin tazarce kaloli daban daban,kusan tare suka janye idanuwansa,gabanta ya shiga faduwa,kasa zaman wajen tayi,batasan ana iya gajin mutum ba,gashi ko mayafi babu a jikinta,sai ta miqe jikinta na rawa gabanta na faduwa ta bar wajen,ta tura qofar ta kulle ta dawo cikin bedroom din anty dijen.

      Gefan gado ta kwanta rub da ciki tana sauke numfashi,maganganun baabaa suka soma dawo mata,har yau ta kasa gane me yake nufi,tana da buqatar qarin bayani,tana buqatar taimako wajen wanu ko zata fahimci me yake nufi,amma ta taimaka masa wajen gyara rayuwarsa kamar yaya kenan,wanu mummunan abu yake mara kyau yakeso ta saka baki?,amma ita a wa?,bata da wannaj power din,ganin qwaqwalwarta na neman daurewa yasa ta kada kai tare da yin watsi da maganar,maimakon ci gaba da tunani sai ta sake daukan wayarta ta lalubi zainab ta kirata,din jiya suna wajen dinner taga misscall dinta baya kuma samu ta bita ba.

        Bayan sun gama gaisawa da mama ta musu Allah ya sanya alkhairi zainab ta karba,nan take gaya mata jiya aka kawo lefe sati uku kuma aka sanya,murmushu sumayya ta saki tana tsokanarta
"Kice mu fara shirin tahowa kano ko?"
"Wallahi yaya,kizo ayi tsare tsare masu kyau"
"Insha Allah,ina huce gajiyar wannan bikin zaki ganni,Allah ya nuna mana da rai da lafiya"
"Amin yaya,ina abdallah na"
"Uhmm,ni kaina bansan ina yake ba,yana gidan biki"
"Ki gaisheshi tunda ya manta da mu" dariya ta danyi
"Zaiji,ki gaidan halimaty,wayarta bata shiga"
"Zata ji" suka katse wayar.

       Tana sauke wayar ta jiyo muryar abdallah yana karadi daga qasa shi da sh hafiz,sauka tayi daga gadon ta sauko qasa,yayi masifar kyau cikin wata arniyar shadda ash wadda batasan inda ya samota ba,hulace kanshi zanna wanda sau faman zuba qyalli take,qafafunshi saye da takalmi sau ciki,abinka da uwa da da,yana ganinta ya tako da gudu ya daneta,murmushu tayi ta zube saman kujera yana faman zuba mata surutu da bata labari.

        Ganin sha daya tayi ga gidan babu kowa sai ita ya sanyata yin shahada ta yafa mayafinta ta fito,kamar zata nutse haka ta dinga ratsa mutane a darare tana wucewa har ta kai ga cikin gidan bayan ta kira humaida ta gaya mata inda suke,ko ina harabar gidan 'yan uwa da abokan arziqi ke kai kawo,kowa ka ganshi cikin kwalliya da walwala,daga gefe guda ta hango mahmoud da tarin abokansu ciki har da alqasim,suma sun ganta saboda haka ta qara sauri don kada su rusketa.

       Batayi aune ba sukayi karo kanta ya daki qirjinsa,tayi taga taga ta komo ta fada qirjinsa,zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro,tayi yunqurin janyewa,ta samu nasara saidai hannunta na cikin nashi hannun yana duban qwayar idanuwanta,sai yanzu ya samu amsar inda ya samu qamshin da ya buwayeshi tun shekaran jiya,wanda har kuka su'adah tayi sabida jin qamshin,don ta tabbatar hadin humra ce ta mata ta musamman ba turaren namiji bane,gaba ta tusashu tana tambayarsa ina ya samu turaren,baki daya zuciyarta ta gama zayyana mata yana neman wata ne,idan banda haka ina zai samo turaren mace a hannunshi?baya ga haka ta lura wannan karon sam baya marmarinta,baya nemanta idan ba ita ta buqata ba,bayan a baya ta sani cewa duk sanda suka hadu har sai ta gaji ta hada kayanta ta gudu yake qyaleta,amma wannan karon sam ba haka bane,yana jinta yayi mata banza ya gama shirin baccinsa ya kwanta tare sa juya mata baya,don bashi da amsar bata,shi kansa yana jin qamshin cikin hancinsa amma baisan inda ya sameshi ba,baijin zai iya bata lokacinsa ya mata wannan bayanin tunda har tana zarginsa,to ta dauki duj hukuncin da take gani zata iya dauka,hakan ya sake hassala zuciyarta,itama ta shiga fushi da shi gadan gadan miqe ta fice ta sauya dakin kwana,bata san cewa ba shi ta yiwa ba kanta ta yiwa,tunda ba yau farau ba da yake kwana shi daya tamkar gauro,idan da sabo ai ya saba.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now