Babi na saba'in da tara

14.8K 1.3K 225
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*RANAR DA WASU FUSKOKI ZASUYI HASKE,WASU FUSKOKI KUMA SUYI BAQI(RANAR QIYAMA)*

___________________________________

sai la'asar sannan sumayyan ta koma bangarenta,sosai taji dadin zama wajen,sunyi hira mai muhimmanci da ummee,wanda tun tana jin kunya da d'ari d'ari har ta soma sakin jiki,ta sake qwarai cikin ma'aikatan gidan,wucewa tayi bangarenta tana tunanin me zata tanadar masa,kasancewar baison cin abun mai nauyi da daddare,yayin da itama ummee ta shiga tata sabgar tana tunanin yadda zata bullowa mustaphan matuqar ya tada maganar tafiya dubai,wanda tasan mawuyacine bai ambaceta ba.

Qarfe takwas na dare da mintuna ashirin ya tako cikin falon wanda babu motsin kowa sai na na'urori da kuma hasken qwayaye,samanshi ya nufa kai tsaye yana furzar da hucin iska daga bakinsa,shi daya yake tuno gamonsa da su'ad lamarin na sake bata ranshi,ya tabbatar da cewa ta tafin kamar yadda ta fadi,hakanan shima yana kan nashi qudurin na baiga abinda zai sanya shi nemanta ba koda zasu shekara dubu a haka,turus ya danyi yana mamakin yadda dakin ya dawo hayyacinshi bayan yasan me gayaran dakinshi baya nan,don bai gaya mishi zuwanshi abuja ba,da yake idan ba kowa a sashin sallamarsu yake har sai randa suka zo,a hankali tamkar mai ciwon qafa yake takawa yana duban yadda komai ya zama neat kamar ba'a yi waccar barnar ba ciki,a haka har yaqarasa bakin gado ya soma fidda kayan jikinsa yana mamakin wanda ya aikata hakan,bandaki ya shige yana niyyar hada ruwan wanka,tsayawa yayi cike da shakku yana tunani ta ina aka samu ruwan wanka haka?,mai dumi da qamshi,cikin kokwanto ya sanya hannunshi cikin ruwan,anya ba jinnu ke neman yi masa wasa da hankali ba,take sha'awar yin wankan ta sake kamashi,saboda ruwan yayi masa dai dai irin yadda yake so,bai bata lokaci ba kuwa ya shige kwamin wankan abunshi,ya kwanta luf a ciki gajiya na warwarewa daga jikinsa yana zaton anya ba ummee bace tayi masa duka wannan hidiman,yasani cewa ita kadai duk duniya tafi kowa sanin abunda yake so,saidai a iya sanshi ummen bata taba takowa sashen nasu ba,a hankali zuciyarsa ta shiga masa tariyar awannin da suka shude dazu,sanda ya cimmata tana tattare kwalaben dakin,anya ba ita tayi wannan aikin ba
"Ba ita bace,me zata iya wannan,bai tunanin tana da fikirar da zata iya duka wannan aikin,ita dinma bata ma yi masa kwata kwata kalar masu kuzari a jikinsu da zasu iya wannan aikin ba daga safe zuwa yanzu(nace lol saboda baka saba gani cikin gidanka ba)" hannunshi ya daga ya kalla inda yankan yake yana kallo,har yanzu wajen jazur yake abinka da farar fata,yayi mamakin yadda wajen ya kame haka da wuri,sannan zugin ya ragu sosai,ya tuna yadda tayi masa treating hannun,bai taba dauka ana irin hakan ba a gaske,yasan dai a fina finai hakan na faruwa,ko kuma ga matan turawa wa mazajensu ko samarinsu,tunanin ya dauka ya ajiye gefe,yana da buqatar barin qasar nan a gobe ko zai samu nutsuwar zuciya,yana jin bai da wani abunyi a cikinta,wannan tunanin ya sanyashi miqewa daga cikin ruwan wankan ba don ya gama awannin da ya sabayi ciki ba,ya saba kunfa ya qarasa wanke jikinsa ya daura towel ya fito.

Bakin madubinsa ya tsaya da niyyar yin shafa,sai a sannan ya lura madubin nashi ya koma babu komai a kai saboda haukar daya fuskanta a daren jiya,wani mugun tsaki ya ja,yana sake jin zafinta da haushinta,tana kuma sake fice masa a ka,wani dan abu ya danna gefan gadonsa ya janyo wata qaramar locker,take dukkan wasu kayan shafe shafensa suka bayyana,ya kwasosu ya watsa saman madubin yana dauka daya da daya yana amfani da kowanne a muhallinshi,bayan ya kammala ya fitar da qananun kaya ya saka sanann ya sanya takalmi wanda ya dace da kayan.

A nutse yake saukowa qasa,har yanzu falon shiru yake
"Me taci tun safe zuwa yanzu bayan lawal yace ba wanda yayi kiransa" yake rayawa cikin ranshi,mutum ne mai qoqarin sauke haqqin da ya rataya wuyanshi,hakan ya sanya ya taka a hankali ya isa cikin corridor da dakunanta suke,ya murde qofar ya tura,tsaye take cikin nutsuwa saman abun sallah,sanye da yalwataccen farin hijabi wanda ya saukar mata har saman qafafunta,hannayenta na hade saman qirjinta kanta a sunkuye tana karatun sallah murya qasa qasa,sakin qofar yayi ya koma da baya idanunsa a kanta kafin ya juya baki daya ya fice,idanunsa ya lumshe kana ya budesu yana ficewa daga sashen ba tare da ya iya tuna komai ba.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now