Babi na dari da biyu

17K 1.3K 172
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya zul jabarutu wal malakutu wal kibriya'i wal'azmati*
_____________________________________


       Tunda ta fito ta fuskanci maganar dai kusan kan shiga kitchen ne,ita kanta ta gaji da wannan jeka ka dawo magana daya tak mai sauqi amma ta rasa dalilin su'ad na qin yarda da maganar tashi,har zata rabe ta wuce sai kuma ta fasa sakamakon tuna fadar Allah da tayi
"Haqiqa muminai 'yan uwa ne kuyi sulhu tsakanin 'yan uwanku", a nutse ta qarasa wajen da suke tsaye,ta sanya hannunta ta riqe hannun almustapha ta gefe ta yadda su'ad din na zata gani ba ta soma matsawa a hankali idanunta cikin nashi,cikin 'yan kwanakin nan su'ad tasa ta ga halinshi da bata taba gani ba,ta fuskanci yana da fushi saidai yakan jima ba'a ga fushinsa ba,barshi dai da miskilanci wannan tambarinshi ne,sai data fuskanci hankalinshi ya soma dawowa gareta yayin da su'ad rayi carko atsaye tana jiran kota kwana
"maan" karon farko ta kirashi da sunan da mutane ke yawan kiranshi,saidai yaji sunan ya zama wani sabi na musamman daga bakinta,a tausashe hadi da karyar da wuya tace
"Bai kamata ba....." Dakatar da ita yayi da hanzari ra hanyar daga mata hannu sannan ya waiwaya ya dubi su'ad
"Option ne na baki,na kuna rantse yau ko zaki kwanta asibiti sai kin dafa tea din nan,naga wanda zaya sake min order din abinci cikin gida na" yana fadin haka ya zame hannunshi daga nata ya wuce zuwa sashensa,da kallo suka bishi,yayin da gaban su'ad ke faduwa,ta tabbatar da cewa yau din matuqar bata yi abinda yace ba babu abinda bazqi iya faruwa ba,saidai ta yaya zata ta ina zata soma tunkarar kitchen?,sai kawai ta wuce fuuu kaman guguwa ta shige kitchen dinta,sam abun baiwa sumayya dadi ba,hakan ya sanya batayi qasa a gwiwa ba ta bishi zuwa dakinsa.

      Yana tsaye gaban window,hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi,qoqari yake yayi controlling kansa tare da hana zuciyarsa aikata abinda take raya masa,so yake yaga ta ina ya gazawa su'ad,ci?,sha?,sutura?,kudin kashewa?,walwala ko adalci,duka babu,babu ko daya daga ciki,hasalima ta wani bangaren tafi sumayyan samun wasu abubuwa,tunda suka fara tarayya da sumayya bazai iya tuna rana qwaya daya tak da ta tambayeshi wani abu ba,saidai shi don gashin kansa ya bata,ko idan su'ad din ta tambaya yayi adalci itama ya bata duk da bata tambaya ba,abinda ya lura ma shine tara su take,ba abinda take da su,shi kansa yasan babu wani anu qwaya daya da na kusa da shi bama iyalinshi ba da zasuyi kukan basu da shi ko yafi qarfinsu,shi a ganinsa babban abun kunya ne ma ace kai din wani je,ko Allah ya maka rufin asiri,ana maka kallon mai rufim asiri,a ganka cikin kama kai kyau amma iyalinka a wahale ko cikin mummunar kama,wannan shine babban abin kunyar da magidanci zai aikata wanda zai jawo masa tur da ala wadai a bakunan al'umma.

       "Abu abdallah" ta furta a nutse,tunda yaji sunan yasan itace,amma hakan bai sanyashi ya waiwayo ba,sai ya nutsu yana jin yadda take takowa zuwa inda yake tsaye,bata dakata ba sai data sha gabanshi,ta tsaya tana dubanshi idanunta cikin nashi kaman yadda nashi yake,duk da cewa a cikin hijabi take,duk da cewa daga bacci ta tashi batai wanka ba,duk da cewa ba ko digon kwalli cikin idanunta amma bata fasa yin kyau ba cikin idanunshi,kyanta cikarta da kamalarta sun fito muraran,ta jima tana kallonshi wanda sannu a hankali dumin da zuciyarsa tayi ya soma sauka,da wannan damar tayi amfani ta soma cewa
"Ina ganin bata haka ya kamata ka bullowa anty ba....bazaiyiwu dare daya kace sai ta maka girki ba bayan can bata saba ba,a mata haquri a bata dama ta koya tukunna...."
"Wacce damar?,wacce dama za'a bata ne sumayya?" Ya furta cikin sanyi,saidai daga yanayin yadda yake maganar kawai kasan ranshi akwai sauran damuwa a ciki
"Akwai damar data wuce na sai mata rana guda cikin ranakun makaranta catering school?,ta koya ita kadai?,cikin gida ko a can duk wanda take so?......daga yau bana son ki sake sanya baki cikin wannan matsalar...ki barmu" ya fada cikin salon dakatarwa,yawu ta hadiye kafin ta sake lanqwasa murya
"Kayi haquri idan hakan ya bata maka,banyi ba da niyyar shishshige...rayuwarka rayuwata ce,haka nan rayuwarka rayuwar su'ad ce,hakan na nuni da cewa dukkaninmu abu guda ne...kwanciyar hankali nutsuwa da zaman lafiyar dayanmu yana da amfani a garemu baki daya,bazanso ace kullum kai da ita ba kwanciyar hankali ba....hakan zai iya shafata zai iya shafar iyalin da muke son samarwa nan gaba,tunda dai muna tare da ku"idanu ya zuba mata yana karantar tsantsar gaskiyar dake cikin zuciyarta da takeson fadi,hankali nutsuwa da karamci ne zallah cikin kalamanta,don me yasa ta samu dama irin wannan maimakon tayi qoqarin tarwatsa zamansu da su'ad ta mallakeshi ita daya saima take qoqarin gyarawa?,kyakkyawar zuciya ce itace amsa,wadda ba kowanne bawa Allah yake wa baiwarta ba,sai 'yan baiwa daga cikin bayin nasa,maimakon ya bata amsa kawai sai ji tayi ya janyota cikin jikinsa ya juyata da hanzari ya rungumeta ta baya yana shinshinarta,duk da cewa batayi wanka ba amma hakan bai hana wannan qamshin nata mai sanyi fita daga jikinta ba,dumin fatarta ya dinga ratsawa cikin tashi,hannunshi ya dora saman cikinta yana yawo da shi,wani farinciki na maye gurbin bacin ranshi,duk sanda ya farka da shi yaje farkawa cikin ranshi,kullum yana lissafe da ranar da zaya iso cikin duniya
"Wannan ne abu mafi muhimmanci da ya kamata ace kinyi zaki tsaya kina wani tsarani" dariya ce ta kubce mata ta soma qoqarin boyeta
"Au tsara ka ma nake yaya?"
"Waye yayan naki,yau kuma yaya na zama?" Girarta ta dage sanda yake leqo fuskarta
"Eh....ko nayi laifi?"
"A'ah....bakiyi ba" ya fada yana cikata tare da durqusawa gabanta,tasan me zayayi tunda ya fara kware mata hijabi,ba dama su tsaya inuwa daya sai ya fara lalubar cikinta,baya ta ja tana ware ido tare da kada masa yatsa alamar a'ah,sosai idanun nata suka fito sun sake wani fari tas da su,hakan yaso shagaltar da shi
"Sulhu nazo nema ba gaidaka muka zo yi ba" sai ya miqe daga durquson da yayi yana ci gaba da kallonta tare da nuna kanshi da yatsa
"Ni kuka yiwa haka?,zamu hadu,awa ashirin cif suka rage" dariya ta saki ganin yadda yake kwatantawa da hannunshi,ta juya taba niyyar ficewa,duk da yadda tayi kewar lafiyayyar fatarsa amma hakan bazaisa ta bashi dama suyi wani anu sq zai sosa ran su'a din ba,abinda ko ita aka yiwa ba zata taba jin dadi ba
"Amma kaman zazzabi naji jikinki ko?" Waiwayowa tayi tana dubanshi
"Ina jin hakan idan na tashi da safe,amma da nayi wanka shikenan bana sake ji"
"Ko nazo na dubaki?" Ta gane sarai wayo yake son yi mata sai ta saki qaramar dariya sannan ta juya ta fice tana cewa
"Mun yafe".

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now