Babi na ashirin da hudu

9.7K 855 66
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Man ja'a bil hasanati falahu ashru amsaaluha,wa man ja'a bis sayyi'ati fala yujza illa musluha*

           Bata gayyaci kowa ba baya ga mutanen da suka mata rakiya suka ga gida suka kama gabansu,hakan ga sanya randa za'a kawo amarya ita daya ce qwal,cikin dakinta tayi zamanta saboda falon nasu cike yake da 'yan kawo amarya,wadanda tun daga motsinsu ta karanci yanayinsu,su din ma dukkan alamau sun nuna babu arziqi,saboda haka tayi musu aji guda ta sanya su.

       Bata fito ba sai da taji motsin 'yan uwan mukhtar wadanda da su aka dauko amarya,fuska sake ta fito falon tana musu maraba,saidai kowanne wanu irin kallo yake binta da shu,ganin babu dole ya sanya ta juya ta koma dakinta tun kafin su yarfata cikin jama'a,yanzun kam ba da bace da quruciya ke dibarta balle ta nace sai an kula ta ko ta faranta ran wanda bai damu da nata farincikin ba.

            Ganin tara na dare yayi hayaniyar ta sarara da alama sun watse sun bar masu gidan da gidansu,sai ta miqe ta sanya turaran wuta cikin dakinta zuwa corridor dinta a burner din da anty dije ta siya mata guda biyu kyauta,take qamshin ya karade ko ina har zuwa falon nasu,wanka ta shiga ta tsala ado cikin wani marron material wanda aka yiwa ado da golden din zare,sosai ya fidda salsalar farar fatarta wanda jan lallen da tayi ya sake bada gudun mawa,baga wani cika kwalliya ba ta dai yiwa kanta barin turare kama daga humra,body spray body mist zuwa perfume na kaya.ta yane kanta da mayafi golden ba tare data buqaci daura dankwali ba ta kame gefab gadonta tare da janyo wayarta ta soma 'yan danne danne don ta dauke mata abinda take ji cikin zuciyarta.

          Qarfe goma taji sallamar mukhtar din cikin falonsu,burus tayi tamkar bata jishi ba,wani kishi da matsananciyat faduwar gaba suka ziyarceta,sai ta dakata da abinda takeyi din tayi shiru tana sauraron motsinsa da kuma bugun zuciyarta.

         A hankali ya yaye labulen yayi sallama,ta amsa ba tare da ta dubeshi ba,idanu ya zuba mata,ta masa kyau sosai tamkar yau take amaryarsa,wanu qaunarta ke taso masa ta wani lungu can dake saqon zuciyarsa wanda wani abu da baisan ko meye ba ke qoqarin fatali da abinda yake ji din,ya rasa me yaje ji cikin zuciyarsa a yau din,koda zaka ritsashi da bindiga ha zaya iya gaya maka ainihin me yake ji ba,farinciki koko baqinciki,ya jima cikin wannan yanayin wanda baisan sanda ya shige shi ba,da yayi yunqurin wani tunani kuma sai ya shagala,tunanin ya qwace masa.

        Ganin bata da niyyar cewa komai ya sanyashi qarasowa gefanta ya zauna yana zube ledojin hannunshi a qasa
"My sumy.....yau kan arziqin sannu da zuwan ma ban samu ba" ya fada cikin marairaicewa,a hankali ta dago kai ta kafeshi da idanunta wanda suka sanya yaji wata fargaba da kamashi,yayi kyau cikin shadda butter colour dinkin babbar riga,yasha askin saisaye da gyarab fuska wanda ya sakw fidda shape sin kyakkyawar fuskarsa.

       Tamkar an dorawa zuciyarta dutse haka taji saboda tsabar kishi,yau nukhtar dinta zai sake zama na wata a karo na biyu,me yasa yaya yahanasu taqi barinsu su huta,me yasa ba zata gane irin yadda take son mukhtar dinta ba,laifi ne dan baka haihu ba?,shine lawai dalilin da yasa suke ta rabata da farincikinta  a lokuta mabanbanta,ina ma ace ana siyar da haihuwa yau da ta sayeta koda zata rasa zanin daurawa,koda zata rasa lomar abincin da zata sanyawa bakinta,don dai kawai su barta da mukhtar suyi rayuwar farinciki.

          So take ta bude baki da gaya masa magana ko zata ji sauqin tuquqin da zuciyarta ke maga amma sai ta kasa,girman mukhtar cikin idonta yafi gaban haka,miqewa tayi gudu gudu sauri sauri idonta na saukar da qwalla kan kuncinta,miqewa yayi biyita da sauri cike da muradin cimmata,saidai tuni ta afka toilet dinta ta rufe qofa tare da sakin kuka.

         Bakin toilet din ya tsaya yana naci da magiyar ta fito,sai da suka kusa kwashe minti ashirin a haka,ba zata iya kallonsa ya tafi dakin wata ba hakan ya sanyata cikin muryar kuka tace
"Bana son ganinka yaya mukhtar ka tafi don Allah ka qyaleni"
"Yau nine sumayya baki son gani?.....yau......." Bai kamamala maganar ba wayarsa dake aljihun gaban rigarsa ya hau ruri,hannunshi ya zira,ganin mai kiran ya sanyashi dagawa
"Dear m,ina ka tsaya ne wai bayan na ji shigowarka",bazai iya tantance mai yaji ba,so yake ya rufeta da masifa amma sai ya kasa,maimakon haka sai ya bige da cewa
" ina gun yayarki zance ko qanwarki ina lallashi"gabanta ha fadi haushi ta turniqeta,kada fa ace duk abinda ake bata labari kan sumayyar gaskiya ne,amma babu komai saura qiris tayi maganin abun
"Lallashin me kuma dear bayan ba wannan ne karo na farko ba da aka fara mata kishiya,ka taho ko nazo da kaina na tafi da kai"
"Ok gani nan" ya fadi da sauri tare da katse kiran,maida idanunsa yayi ga qofar toilet din,ya tabbatar taji duk abinda suka ce,kamar sumayyan ce ke gabansa ya marairaice
"Shikenan sumayya zan tafi,ga ledarki can cikin daki Allah ya bamu alkhairi" ya fada yana juyawa.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now