Babi na dari da bakwai

22.2K 1.3K 376
                                    

*bamu kasance masu azaba ba har sai da muka aiko da dan aike(manzo)*

*haqiqa mun aiko ka manzo(annabi muhammad)kan al'ummah,Allah ya isa shaida*

*wanda ya yiwa manzan Allah biyayya haqiqa yabi Allah*

*haqiqa mun shiryar da shi hanyoyi biyu(dan adam)kodai ya zamanto  mai godiya ko ya zamto mai kafircewa*

*haqiqa mun halicci mutum  daga digon maniyyi dake cakude da ruwan mace da namiji muna jarrabashi da takhlifi(nauye nauye na shari'a Allah na nufin jarrabarsa a sanda ya dace)saboda haka muka sanyashi mai ji mai gani*

*haqiqa wannan gargadi ce ga talikai to wanda yaga dama sai ya riqi hanya izuwa ubangijinsa*

_____________________________________

         Sosai ta shiga gyara cikin satin bata zauna ba,ummu kam ta daure mata qarqashi ta kwashe mata su amatallah,duk wani abu daya kamata ta aiwatar da shi,har kwaskwarimar bangarenta sai data yi,kafin ranar dawowarshi komai ya zama neat.

     Ranar da zai dawo din mahmoud ne zaya je dauko shi,kafin isowarshi ta shirya tsaf cikin shigar cikakkiyar bahaushiya atamfa,ga mata cas a jiki dinkin ya zauna mata,yaran duka ta shiryasu cikin kaya iri daya komai da komai,sun fito sak a twince dinsu,sunyi wani kyau da girma,sanda taji isowar tasu sai ta kasa zaune ta kasa tsaye,kai tsaye wajen baba ya wuce,ya taddashi tare da matan nashi,ba wanda baiyi farinciki da ganinshi ba,sai a sannan ya yiwa baban bayanin me ya zaunar da shi,shiru baban yayi yana jinjinawa namijin qoqarin da yayi cikin qasar daba tashi ba,aqalla ya kusa mintuna talatin kafin ya wuce sashensu.

       Awa uku da shigowarshi amma ta kasa zama,sai qirqirarwa kanta aiki data yi,zirga zirga take tsakanin kitchen da falo,duk wani motsinta yana kan idanushi,ya ganeta sarai,tana nufin sai ya sake sabon yaqin neman soyayyarta?,kunyarta keson musu shamaki,yana zaune ne da boxer da singlet fara qal bayan yayi wanka,ba abinda ke fita jikinsa sai qamshi mai taushi na turaren safirul hubb da wasu nau'in turarukan,tuni amatallah da amatur rahman sukayi bacci kan qafarshi dake miqe,sai ya yunqura ya miqe da su saman kafadarsa sanda ta sake zuwa ta kwashe duk abinda yayi amfani da shi zuwa kitchenbda alama wanke wanke zata yi,sai da yaje ya kwantar da su din sannan ya nufi kitchen din.

        Tana tsaye gaban sink kuwa tana wanke wanken,taji shigowarshi amma sai ta kasa waiwayowa,a hankali ya qarasa bayanta,ya sanya hannayenshi ya kamo qugunta ya manna da nashi,sannan ya hade bayanta da qirjinsa ya dora habarshi saman kafadarta,nannauyar ajiyar zuciya ta saki saboda wani saqo na musamman da jikinsa ya aikata mata
"Wani abu kake so" ta furta qasa qasa
"Ke nake so maman 'yan biyu?,wai baki da labarin nayi kewarki ne?" Sai ta ajjye kwanukan alamar tabar wanke wanken,abinda ahi bai sani ba kunyar shi take ji sosai ta rasa dalili
"Um um ci gaba da wanke wankenki,zamuyi hirar a haka....bani labarin bayan rabuwa baby....nikam nayi rayuwa ne kawai,gani nan tamkar mutum mutumin,ina rayuwa ne tsahon wata biyar ba tare da nasan nau'in dandanonta ba,amma alhamdulillah,tunda alwashin da naci na cikashi" ajiyar zuciya ta saki tana dauraye wani kwano
"Bansan ya zan misalta maka ba noor,rayuwa babu kai ashe tamkar gangar jikin da babu ruhi ce,kullum sai nayi kukan rashinka,raba dare nake ina kokawa da tunaninka,sai inji kaman ka tafi kenan,kaman ba zaka dawo ba kaman yadda anty su'ad ta tafi...." Sai ta saki kwanukan ta juyo tana kallonshi,sannan ta lafe a qirjinsa kaman mai tsoron wani abu
"Don Allah noor.....kada ka sake tafiya ka barmu haka,ni da yara duka muna buqatarka" dagota yayi suna duban juna kafin ya sakar mata qayataccen murmushi mai kwantar da rai
"Ba zata sake faruwa ba my summyyy,ni dinma ina tsananin buqatarku cikin rayuwata....,bari in nuna miki kadan wani dan yanki daga cikin yadda nayi kewarku" bai saurari komai ba ha dagata baki daya tana dariya da roqon ya sauketa zata taka amma ya qiya,yace baiso tayi komai wannan karon shi zai sarrafata yadda yaga dama,zai kuma dauke duk wani aiki daya zama nata ya hada da nashi duka yayi.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now