Babi na hamsin da shida

9.6K 853 31
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

Wa wassainal insaana bi walidaini ihsaanaa*

*mun yiwa mutum dan adam wasiyya/umarni da kyautatawa iyaye(uwa/uba)kyautayawa(matuqar kyautatawa)*        
_________________________________

      Tana idar da sallar minal ta shigo dakin da gudu
"Anty kizo ana kiranki a waya"
"Waye yake kirana?" Bata amsa mata ba yarinyar sai jan hannunta da ta soma tana nuna qofa da yatsarta,murmushi tayi don tasan halin minal din,sai kawai ta miqe ta bita,tayi tsammanin wayarta dake gun anty dije ake kira,saidai bata tsaya ko ina ba sai kitchen,ta dangana da ita zuwa bakin wayar su ta landline
"A nan ake kiranki" cikin mamaki tace
"A nan kuma,ba wayarku bace ta gida,saidai ko anty ake kira ko?"
"A'ah sumayya suka ce" inji anty dije dake shigowa kitchen din,cikin shakka da ko kwanto ta daga bayan wayar ta sake sakin qararrawa.

      Neman wajen zama ta soma yi jin muryar namiji,gabanta ya yanke ya fadi tsoro ya kamata,ta tsani abinda zai hadata da namiji,ta amsa gaisuwar da ake mata sannan mamallakin muryar ya soma magana
"Nasan baki sanni ba duk da kin taba ganina sau daya,amma nasam zaki iya tunani,shekaran jiya na ganku a wani restaurant dake kaduna ke da qannenki da yayarki,so naso na tare ki na miki magana sai kuma kunyar idon mamanki ya hana,na lura akwai sanayya tsakaninku da masu wajen,gurinsu na amshi lambarku ta gida"
"To sai kuma akayi yaya?" Ta fada gabanta na faduwa tana neman wajen zama saboda sanyi da jikinta yayi,tana mai fatan alaqar ta yanke daga nan,murmushi yayi wanda har sai data jiyo
"Haba yi a hankali mana beauty,ni da nake so mai qulla dangantaka da alaqa mai kyau?"
"Me kake nufi?" Ta tambayeshi gabanta na faduwa
"Suna na alqasim,Kin gane,tun ranar da na dora idanuwana a kanki Allah ya dora min qaunarki,duk duniya naji babu wata diya mace da zuciyata ke so da qauna sai ke,hakan ya sanya na kasa haquri da ke,ina kuma fatan zaki karbi maganar da hannu bibbiyu"
"Hmmmm,Allah sarki" tayi qarfin halin fada tare da kife kan wayar ta miqe ta fice daga kitchen din,baki daya jin zuciyarta tayi ta quntata,itakam duk yadda take qoqarin killace kanta bata tsira ba?.

       Kusan ragowar ranar baki daya a daki tayi ta,dadin abun ma suna tare da su laila,kwanakin qarshen mako ce,sai jibi litin zasu koma.

  *******   *******   *******

      Washe gari tana zaune falo ita da hafiz da minal suna kallo,hafiz kuma na goge musu uniform dinsu,da yake da kansu suke wankinsu saboda suna da inji wanki(washing machine),sumayya ke girkin dare suna ta murna yau zasu ci tuwo saboda haka hankalinta ta rabashi gida biyu,anty dije ce ta sauko daga sama laila na binta a baya hannunta riqe da turamen atamfofi guda biyar,har suka qaraso falon laila na wa anty dujin rakin kayan sun mata nauyi
"To hafiz guga yake muku da ya rakaki,khalipha kuma nasan idan ya bikin ba dawowa zaiyi da wuri ba,kuma aiki ne da shi zaiyi gyaran jakankunan makaranta,idan kinje bakin get baba haruna ya karba miki ku qarasa ciki"
"To" lailan ta fada tana nishi ta fice,dariya sumayya ta dinga yi mata tana tsokanarta wai taji kunya.

      Minti kusan ashirin shiru laila bata dawo ba har sumayyan ta kammala abincin dare,anty dije dake shirin shiga wanka ta sauko qasa tana duban sumayya
"Kinji lailan itama shiru kamar an aiki bawa garinsu?"
"Ko a tura khalipha ya ganota tunda har yanzu hafiz bai gama gugar ba?"
"A'ah,ai duk kanwar ja ce,sanya mayafinki don Allah ya rakaki ki gano min ita" fuska ta yamutsa
"Banson fita anty wlh"hararata tayi
"ke kam ko gajiya da zama a gida bakiyi,tun jiya da kika shigo ko waje baki leqa ba,to ba wani gu bane gidan Baabaa prof ne,gashinan yana kallon gidan nan" dan jim ta sake yi,haka kawai bata son shiga gidan,don tun daga qofar get din zaka ga banbamci qarara da sauran gidajen da ke dukka layin da kewayen unguwan,ba yadda ta iya ta shiga daki ta fiddo dogon hijabinta ta dora saman riga da skert na atamfa dake jikinta ta zura silifa ta fito khalipha ya biyo bayanta.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now