Babi na tamanin da tara

16.9K 1.4K 353
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim

La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin

ADDU'A CE GA DUK WANDA YA SHIGE CIKIN QUNCI

_____________________________________



        Ci gaba tayi da tunkararsu ba tare data dauke idonta daga garesu ba,tamkar zuciyarta zata fito waje saboda tsananin kishi,kamar ta kurma ihu ko zata ji sauqin abinda ke sukar zuciyarta,bata taba jin bala'i irin wannan ba arayuwarta,ashe a baya duka qaryar kishi take kan almustapha?,almustaphan nata ne riqe da hannun wata haka?,sun kuma jero suna tafiya kan bigire guda?,ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,shi sam baiyi zaton ganinta ba ma a wannan lokaci,sai da suka qaraso dab da juna sannan ya zame hannunshi daga na sumayyan ya dubeta
"Idan kika shiga bana so ki fito,bana son yawo ki zauna waje guda,nasan duka nan za'a dawo akwai walima da zasuyi" sai ta samu kanta da narke masa cikin wani irin salo
"Ina so naje wajen umman khalipha fa,tunda nazo ban shiga ba" girarsa ya dage salon ya matuqar qayatar da shi
"Ko zakin ba yanzu ba,idan na dawo zan sanar miki" kai ta gyada tana jifanshi da wani irin qayataccen murmushi daya sake narkar da shi
"Ok,to a dawo lafiya,Allah ya tsare hanya" idanu ya lumshe addh'a ta masa dadi,qarakin murmushi ya subuce masa
"Amin,thanks" kai ta gyada tana juyawa cikin takunta na nutsuwa,baki daya idanuwa su'ad ta bita da shi,ji take kamar ta fincikota ta yarfa mata mari,ba'a tabacin fuskarta irin haka ba,a gabanta wata ke soyewa da mijinta?,ita dun da dukkan 'yammatan danginsa sunsan halinta sarai ko cikakken kallo bata so taga ka fiya masa yanzun zata ci miki mutunci?,saiga wata a gaban idanunta tana narkewa mijinta,ga sumayya kuwa sanda ta juya sai ta dinga jin wani abu na mintsininta cikin zuciya,sai taji kamar ta koma,me yasa ta barsu su biyun?,zuciyarta ta cunkushe,kallon data lura su'ad na mata bai dameta ba,qarfin gwiwar da bata taba jinsa kan kishiya ba wannan karon shi take ji,ba abinda zai sanyata taci gaba da barwa wasu matan mazanta,ta tabbata ko ba'a gaya mata ba babu zancan zaman arziqi tsakaninta da su'ad,ta santa tun ba yau ba,ta santa tun kafin miji ya hadasu,bata da kirki bata da mutunci,bata ganin girman kowa,a haka taci gaba da takawa zuciyarta dake cike da kishi na bata shawarar ta waiwaya amma ta daure zuciyarta ta hana kanta aiwatar da hakan.

      Yatsan tsakiyarsa da babban yatsanta ya hada ya murza a fuskar su'ad din wadda tabi sumayya da kallo,kishi ke sukarta,sam bata gane ma sumayyan ba,saboda ba duka wanda yayi mata qaramin sani irin wanda su'ad din tayi mata bane zai iya tantanceta ba tashi guda,idanunta da suka kada ta dauke ta maida kan almustapha,shigar jikinsa kadai ta bata mamaki,bata taba ganinsa da manyan kaya ba tunda suke sai yau din,wani qyama da takaici ya kamata,ya auri 'yar nijeria arewa ta fara zuba masa duhun kai kenan,to wallahi bazata lamunta ba,wata babbar riga harda hula sai kace wani limami,bakinta na rawa cike da tsantsar kishi tace
"Almustapha?,ashe da gaske baka sona?" Shanyayyun idanunshin nan kawai ya zuba mata yana dubanta
"Almustapha ka dubi yadda kake nuna qauna da kulawa ga wata bayan ni,dama zaka iya aikata hakan?" Ci gaba yayi kawai da dubanta,karon farko da ya soma ganin aibun irin shigar da takeyi,cikin qasarsa gidansu kuma gidan iyayensa surukai a garesu,ba shakka ta nan shine babban mai laifi,amma sam bai gane illar hakan bane sai yanzu,tunu hawaye ya soma wanke mata fuska,sai ya saki hannayenshi ya sake matsowa inda take ya kama hannayenta,ya sani qwarai kishi abu ne mai zafi cikin zuciya,abu daya ne wanda zai janyo mata ta rasa dukkan wata dama daga gareshi shine taci gaba da hauka da tashin hankali
"Enought.....daga gani na sai kuka,ya isa" wani ratsawa wadan nan taqaitattun kalaman sukayi har cikin zuciyarta,sai kawai ta fada jikinsa rungumeshi tana sake sakin kukan,hakan bai dace ba saboda suna tsakar filin gidan,kowa ma na iya ganinsu a haka,dagata yayi daga jikinsa yana fadin
"Zan wuce ne wajen daurin aure kada na makara,ki koma ciki,but ki sauya kayan jikinki kafin na dawo zuwa atamfa lace ko shadda,coz akwai maza da zasu shigo da yawa bayan dawowar tamu bana son kowa ya sake zuwa ya ganki da wannan shigar,ya kamata ta zama tsakamin ke da ni ne kawai cikin gida,understand?"mamaki ya kusa kasheta,bai taba furta mata makamanciyar wannan maganar ba sai yau,me yake son maida ta ne,irin kidahumar matarsa?,taga sarai shigar jikinta,ta nannade kanta da wani material kamar gawa ba wajen shan iska,itakam ba zata iya ba
"sai na dawo ko?" Bata saba yi masa a dawo lafiya ba ko wata addu'a tun da can ma da ake zaman dadi bare yanzu,saboda haka har ya juya ya koma wajen motarsa driver ya bude masa ya shiga suka fice tana tsaye wajen,ashariya ta lailayo ta qunduma cikin harshen nasara,tana jin nemawa kanta 'yanci ya zama dole,ba zata taba lamunta ta zauna cikin irin wannan rayuwar ba,da wannan tunanin ta tattaka cikin sassarfa ta wuce nasu bangaren.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now