Babi na sittin

11.8K 1K 101
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*SHIN KO KUNSAN DUK LOKACIN DA AZABA TA TSANANTA GA DAN WUTA,FATAR JIKINSA TA KWASHE TA QONE,ANA SAUYA MASA WATA FATAR NE SANNAN ACI GABA DA GANA MASA AZABA*

*Allahumma la tada a lana zanban illa gafartah*

____________________________________

        Dattijo ne mai kimanin shekaru sittin da biyar zaune kan daya daga cikin kujeru na alfarma dake zagaye da falon,haiba kwarjini da kamala sun bayyana qarara kan fuskarsa,Allah yayi masa baiwar furfura tun daga gemu zuwa kansa,farin gilashi ke saye a fuskarsa baya ga shaddar dake jikinsa fala sol,dogon wando da riga mai gajeran hannu iya gwiwa,da alamu akwai babbar rigarsu wadda bai sanya ta ba,gefensa daga hannun dama samari ne guda uku,wanda ke daura da shi yana fuskantarsa sosai,bisa alamu magana suke mai muhimmanci,kyakkyawan matashine mai cike da kyau kwarjini izza da haiba,sanye yake da irin kayan tsohon bisa dukkan alamu anko sukayi,shi dinma fuskarsa sanye take da gilashin,daya hannun nashi ma wasu matasanne su biyu sai mata guda biyu.

     Tunda suka shigo falon gabanta ke mugun faduwa,sosai ta dinga qoqarin baiwa kanta qwarin gwiwa saboda haka sai ta sadda kanta qasa har suka qaraso cikin falon suna sallama,dattijon ne ya amsa da wasu daga cikin mazauna falon,idonsa na kan antyn da sumayya har suka qaraso,gefe ta samu ta zauna daga qasan carfet din,da sauri baabaa yace
"A'ah,tashi ki koma saman kujera mana" murmushi tayi kanta na qasa,ta soma gaidashi tare da yi masa sannu da zuwa,fuska sake tamkar ya santa ya amsa mata,anty ta dubeshi
"Nasan baka santa ba" sake dubanta yayi yana gyada kai
"Gaskiya kam,koda na santa to ta kwanta min,kinsan shekarun sun fara turawa sai a hankali" sauran dake zaune sukayi danyi dariya banda mutum daya da tun shigowarsu ya dauke kansa ya maida hankalinsa kacokam kan wayarsa yana tura saqonni,hakanan ransa yake a bace.
"Itace wadda ka dinga bamu labari ka kwashi girki na kwana ashirin ka dinga zabga santi" baki daya dariya suka kuma saki wanda hakan ya dan ja hankalinsa,har ya sanyashi daga kai ya mata kallo daya tak ya sake maidawa kan wayarsa yaci gaba da abinda yake
"Masha Allah,Allah yayi albarka,naji dadin abinci kam qwarai da gaske,Allah yayi albarka"
"Amin baabaa,na gode" ta fada cikin jin dadi bisa dabi'arta ta son na gaba da ita wanda take saka ran addu'arsa zata iya binsa ya sa mata albarka,hannu ya miqawa husna wadda ke hannun sumayya,ta kuwa lafe a jikinta tamkar ta santa,qememe taqi zuwa,sai ya zura hannunshi cikin aljihun rigarsa ya zaro alewa,kasancewarsa mai yawan kyauta,musamman a irin wannan lokaci da jikokinsa ke kasancewa a gidan tare da shi,hakan ya sanya baya rabo da alewa da sabbin kudi,miqa mata yayi take kuwa ta tafi gurin nasa,hannu yasa ya dagata yana dariya jama'ar falon na tayashi,tsaki ya ja qasa qasa yana miqewa,shikam bai san me yasa abun dariya bai yiwa su mu'azzam wuya ba,shi baki daya ma baiga abun dariya ba,yarinyar ma tunda ta shigo baki daya ma yaji ransa ya baci,musamman katse musu hanzarin da tayi kan muhimmin batun da suke tattaunawa,tun dazun dama yake addu'ar kada wani ya shigo saboda baison abinda zai katse masa bayanin da ya daukowa baban,ya san mutum ne shi mai mutunta baqo,kome yakeyi yana iya katsewa ya saurari baqonsa,sarai baaban ya ganshi amma sai ya qyaleshi,yasan halin kayansa sarai,da idanu ya rakashi har ya fice,ganin ya fita ya sanya sauran miqewa
"Baabaa kada fa ya tafi ya barmu"
"Jeku,don tsaf zai iya aikatawa,musamman da kun zo da tsarin da baiyi masa ba"dariya suka yi sannan sukayi sallama da baban suka fice,tattambayarta baabaa yayi kan wasu abubuwan tana amsa masa,har alokacin kanta na duqe,ta miqe bayan wasu mintuna ta masa sallama,sai anty ta ajjiye masa kwanon tana masa bayani,qwarai da gaske yaji dadi,domin shi mutum ne da baya raina alkhairi komai qanqantarsa,koda yafi qarfin abu ka bashi shi yana ganin girmansa abun agunsa,dakatar da ita yayi yana fadin
"bari na baki zamzam da bagaruwa ko"
"To" ta fada tana murmushi,antyn yama kwatance cikin dakinsa,cikin sakanni ta shiga ta fito da wata jarka
"Ba ita ba,zamzam din da nayi dawafi da shi" mamaki antyn tayi,don irin wannan zam zam din ba kowa yake bawa shi ba,dashi yaje dawafi da addu'o'i,yakam zama magani cikin ikon Allah ga duk wanda ke jin lalura ya bashi yayi amfani da shi,duk da kasancewarsa tantagaryar dan boko amma akwai ilimin addini mai yawa tattare da shi,jarka ce guda tayi tsawon ta faro qarami ya zuba mata,sannan ya cika mata leda da bagaruwa da dabino,godiya tama baban sosai ta kuma ji dadin kyautar tasa,tare suka fito da antyn
"Anty zan koma"
"Haba daga shigowarki,kodai tsoron kike ji kamar yadda mahmoud ya fada,naga ko mutuniyar taki amira baki gani na,bayan ita tunda muka dawo take maganarki,na tabbata baqi ke suka hanata fitowa da tuni kin ganta,sannan baki shiga kin gaida ummee ba" sam bata so antyn ta debo mata wannan bayanin ba,amma sai ta sadda kai tace
"To,bari na shiga"
"Yauwa,ki gaida ummam khalipan don Allah idan kin koma,nasan itama baqi ke suka hanata leqowa,dukkanmu irin wannan lokacin sai haquri baqi muke ba dauke qafa"
"To zataji" ta furta sanda antyn ke yunqurin amsar husna,nan ma qi tayi,dariya antyn ta dinga
"Shikenan kuje da ita kin samu qanwa,idan tayi kuka ko laila kaya bada ta kawota"
"To anty" tafada tana dariya tare da yin gaba.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now