Babi na sittin da shida

11.3K 1K 127
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

Allah s w t yana cewa

HAQIQA SAI NA CIKA JAHANNAMA DA MUTANE DA ALJANU BAKI DAYA

Ya Allah ka yi mana tsari,ka suturta mu
__________________________________
__________________________________

     "Wannan shine cikakken tarihin familyn baabaa sumayya,na tabbata zuwa yanzu kin fahimci komai" murmushi sumayyan keyi tana gyada kai,sosai labarin asalin zuriyyar ya burgeta ya qayatar da ita,very interesting,ta tsinci darussan masu yawa a ciki,sunyi gadon karamci mutunci da halacci,qasan ranta take raya amma shi kam bata san inda ya tsinto nashi halayyar ba,tana masa duban mutumin da bai girmama mutuntaka ta dan adam,mutum mara saurin fahimta da dogon tsinkaye da bada hanzari
"Wa kenan"ta tsinci muryar anty dije na tambayarta
"Na'am"sumayya ta waiwayo da hanzari tana tambayarta,don bata tsammaci da ita take ba
"Idan na canka dai dai mustapha kike wa wannan yankan hanzarin ko?" Da sauri ta kada kai
"Ko kadan,me kika ji nace?" Murmushi antyn tayi ganin tana son musanta mata,cikin sigar tsokana tace
"Kiyi dai a hankali,kada kema ki fada tarkonshi,naga ba wuya 'yammata sun zurma cikin komarsa" wata matsananciyar faduwa gabanta yayi,kai ta soma kadawa
"Allah ya sawwaqe anty,ya rufamin asiri duniya da lahira,yanzu kyamin wannan fatan haba anty?,na kai su'adah ina,baya ga haka ma wallahi baiyimin ba ko kadan,banga abun burgewar ba anan wajen" dariya antyn tayi sosai har su laila dake sit din gaba suka waiwayo suna dubanta sai data ce su juya
"Dukka yadda akayi kallon tsoro kika yi masa,kece mutum ta farko da naji kin ambaci haka,ko minal dake da qarancin shekaru cemin take,mami uncle man yana da kyau kamar na 'yan india,ta yaya ma zaki gane shi bayan kallon mukhtar kika yi masa ba ainihin kamarsa kika gani ba,kuma ma meye na saurin rantsuwar baiyi miki ba?,kika san inda rana zata fadi?"
"A inda ta saba faduwa mana anty,komai kyansa bazan gane ba anty daga kan mukhtar an gama namiji" ta qarashe zancan fuskarta na nuna rauni da karaya da zuciyarta tayi,hakan ya sanya antyn yin shiru,yayin da itama tayi shirun tana maida numfashi tare da hadiye yawu da qyar.

        Kai ta girgiza bayan ta gama wassafa ta yaya zata zauna zaman aure da wani bayan mukhtar din,sam,ji take ba zata iya ba,babu wannan mafarkin cikin rayuwarta,kamar soyayyar da take nuna masa bata cika ba kenan.

        Cikin hukuncin Allah suka isa qasar lafiya,tun daga airphort sumayya ta soma gane banbanci baro baro da tata qasar,haka tayi ta kalle kalle sanda taxi ke dauke da su zuwa masaukinsu,sai ta samu kanta da yiwa qasarta addu'a tare da fatan samun ci gaba kamar wannan qasar.

         Da suka isa a gajiye suke,gida ne wanda ke dauke da falo guda daya,sai kitchen,bedroom uku,kowanne da manne da toilet,sallolinsu kawai suka rama kowa ya kama makwancinsa,kusan ita ce qarshen bacci a gidan,ta jima tana juyi kan gadon,hakanan take da tsananin baqunta,duk sanda ta sauya muhallin data saba da shi tana dadewa kafin bacci ya dauketa.

       Tunda suka je uncle farouq bai zauna ba,yana ta zirga zirga kan abinda ya kawoshi tare da yi musu siyayyar abubuwan da zasu buqata na gida,sai da suka ci sati guda cur kafin komai ya daidaita,ya miqa laila da khalipha wata makaranta wadda ke nan cikin unguwar,yayin da ya samawa sumayya wata center ta manya dake karantar da su dukkan wasu karatuttuka irin na 'yan secondry tun daga matakin farko cikin shekara guda su baka certificate dinka,itama babu nisa tsakaninsu,ko a qafa zaka iya zuwa,idan kana da buqata kuma kana fita bus zata zo ta daukeka ta qarasa da kai,da fari sumayyan ta tsure,tsoro take ji,tana tunanin ta yadda zata dinga zuwa wajen ita daya,ta zauna cikin baqin fuska,fararen fata,wadanda akwai banbancin addini harshe da al'ada tsakaninsu,kamar tayi qwalla saboda tsoro,anty dije ta dinga tuntsira mata dariya
"To ko ni zan dinga rakaki?" Ta zolayeta
"Dole fa ki saki jikinki sumayya,nan qasar babu ruwan wani da wani ce,kowa abinda ya kawoshi shi yakeyi,ki zama mai budadden kai,so nake a kasa ganeki duk sanda muka koma gida" da irin wadan nan kalaman ta qarfafi gwiwarta.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now