Babi na goma sha uku

9.4K 882 87
                                    

*wa iyyamsaskallahu bi durrin fala khashifa lahu illa huw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih*

           A qofar gidansu mai adidaita sahun ya ajjiyeta,ta biyashi sannan ta ja akwatinta zuwq ciki.

         Ta jima a soron tsaye gabanta na faduwa,tana mtuqar shakkar iyayenta,saidai hakanan taji ana ingizata zuwa barin gidan,wani irin qunci take ji idan tana cikin gidan,numfashi ta ja sannan tayi shahada ta shige.

           Qannanta na tsakar gida suna karyawa jikinsu sanye da unifoarm din islamiyya,innarta kuma na daga cikin rumfarsu,
"Lah sannu da zuwa yaya sumayya" suka fada halima na karbar mata akwatinta tare da shiga da shi cikin rumfar tasu ita kuma tabi bayanta.

           "Lafiya sumayya da safiyarnan?" Innar ta tambayeta cikin fuskar mamaki,gefan kujerar ta samu ta zauna sai kawai ta fashe da kuka ba tare da tace komai ba,baki innan ta sake tana kallonta kafin daga bisani ta yiwa halima nuni da hannu kan ta fita ta basu guri,daga qarshe itama da ta gaji da tambayarta sai ta miqe ta fito tsakar guda ta hau ayyukanta ta barta cikin dakin.

           Wuni guda innan na tambayarta amma ta gaza cewa komai,to me zata ce mata ya korota daga gidan,ba matsala bace tsakaninta da mijinta ba ballanta na tace,ba wani abu sukayi ba,to meye dalilinta,sosai hankalin innan ya tashi ganin taqiyin maganar,gashi kuma malam din baya gida sun tafi musabaqa ta jaha da ake gudanarwa daga shi har yayan ta abubakar,amsa daya ta iya bata data tambayeta ina mukhtar din ta sanar masa yayi tafiya,sai kan innar ya sake daurewa,har dare tana zuba ido ko zata ga wani kan sumayyar amma shiru haka suka wayi gari.

            Mamaki innar ta kuma tashi da shi na ganin washegari sumayyan ta sake sarai,walwalarta take kamar babu wani abu da ya shalleta,wannan damuwar da ta zo da ita jiya duka yau babu ita.

           Tunda suka dauko hanya daren jiya yake Allah Allah ya iso gidan nashi don yayi tozali da sumayyar tasa,qarfe uku da minti biyar dan adaidaita sahu ya ajjiyeshu qofar gidan nasa ya sallameshi ya shige gidan bakinsa dauke da sallama fuskarsa qunshe da murmushi don yana da yaqinin samun tarba mai kyau kasancewar ya tafka sa'a cikin ranar girkinta zai dawo din.

           Mamaki ne ya maye gurbin doki murmushi da fara'ar da yakeyi ganin yadda tsakar gidan yake a tarwatse babu cikakkiyar tsafta,sallama ya sakeyi karo na biyu saidai shiru babu amsa,a hankali idanunsa suka sauka kan dakin sumayya,take yaci karo da kwad'on da take kulle dakin duk sanda zata fita,mamakinsa ya sake ninkuwa,ko da can sumayya sanda take da qananun shekaru ainun bata taba fita ba tare da uzininsa ba koda kuwa maqota ne,ya maida kallonsa dakin fa'iza ana sakaye,ya qarasa ya tura ya leqa kansa ciki bata nan,ya tura bandakin ya leqa nan ma bata ciki,jikin bango ya koma ya jingina tare da ajjiye jakar bacco din hannunsa,ba fa'iza ce damuwarsa ba sumayya ce,lambarta ya lalubo ya kira saidai an sanar masa da cewa a kashe take,ya maida wayar cikin aljihunsa yana maida ajiyar zuciya tare da shiga tunani.

          Maganar fa'iza ta katseshi wanda da alama da wasu dake daga waje take maganar,ya zubawa qofar soron idon har ta qaraso,da fari tayi turus,sai kuma ta qaraso tana dubansa
"Au......ashe kai ne.......ashe yanzu zaka dawo.....na dauka sai anjima gashi ban tanada ma komai ba"
"Ina sumayya take?" Ya tambaya ba tare da ya kula da surutun da take zuba masa ba,wani abu ya takore wuyanta,wato ta sumayya ma yake ko,zai gane kuransa ne wlh,baki ta tabe sannan tace
"Ka bani ajiyarta ne?"idanunsa ya ware baki daya har sai da taji tsoro
" ke bana ciki da iskanci,ni kike gayawa haka,zan tattaki ne wallahi naga uban da ya tsaya miki,banza sha sha sha,ina sumayya take nace miki"cikin gunguni tace
"Oho,nidai da asussuba naga ta hada kayanta ta fice bansan inda taje ba".

        Bai qara bi ta kanta ba ya shige dakinsa ya ajjiye kayan hannunsa,da sauri ya sake zaro wayarsa saboda tunawa da yayi waccan satin sumayyan ta saka maaa lambar wayar innar tata ta gaya masa ya abubakar ne ya siya mata waya.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now