Babi na talatin da shida

9K 927 101
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa'iza sa'a laka ibady anny fa inni qarib,ujibu da'a watad da'i iza da'aan*

*_idan bayina suka tambayeka game da ni kace ni makusanci ne(ina kusa da bayi na),ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roqeni_*

_______________________________

      Har ta idar sallahr isha'i babu abdallah ba mukhtar,sai ta rushe sa kika ganin qarfe takwas na neman gotawa,komawa tayi ta jingina da jikin katifa tana maida numfashi tare da sakin ajiyar zuciya.

        Kamar daga sama taji muryar mukhtar din kamar daga can soro suna magana da yaya abubakar,sai ta miqe zumbur ta zauna tana saurare har zuwa sanda abubakar din ya daga labulen qofar dakinta ya leqo
"Kije ki karbi abdallah,wai yau ni zaiwa rashin m yaga babansa yaqi yarda na karboshi" ya qarashe zancan yana sakin labulen,tana ji yana ma mama qorafi tana musu dariya,zumbur ta miqe kamar mai jira,dama tun hijabin da tayi sallah shine a jikinta bata cireshi ba.

       A soron ta tadda su tsaye yana rungume da abdallan,tana zuwa ta miqa hannu alamar ya bata shi,banza yayi kamar bai gane me take nufi ba,ya dubeta fuskar nan a dinke tsaf
"Duk randa kika sake gigin fitowa gun bazawarinki da yaro na,idan har na tafi da shi ya tafi kenan har abada" ya qare maganan sannan ya miqa mata shi wanda tuni bacci ya fara dibansa,hannu tasa cikin azaba ta karbeshi,cikin hanzarin ta shige gida kamar wanda zaice mata dawo da shi,binsu yayi da kallo har suka shige,ya jima tsaye cikin soron ba tare da ya iya tafiya na a haka abubakar ya cimmasa sannan sukayi sallama ya tagi,har yanzu bai cimma burinsa na ganin wanda ke zuwa gun sumayyan ba,amma babu shakka ba zai guahe ba har sai ya gano waye.

        Dare ya fara miqawa amma tana kwance idanunta biyu,abdallah na jikinta yana ta barcinsa,a haka halima ta daga labulen dakin ta shigo
"Yaya sumayya wani ne keta kira tun dazu yana cewa sumayya yake nema,nace masa ba ita bace amma yace ita ta bashi number din "
"Wani?" Ta tambaya cikin mamaki,don har ga Allah ta mance shaf da luqman.
"Eh,yace dazu da yamma" sai a lakacin ta tuna da shi,don baki daya abdur rahman ya hargitsa tunaninta,maganar sa ta mata girma,ga mukhtar shima da yaso hautsina ta,kafin tace komai wayar ta sake ruri,haliman ta kalleta
"Yaya gashi,shi ya sake kira" tsaki ta dan ja tana ganin baiken kanta tun farko da bata bashi lambar bogi ba,kanta ta maida kan filo sannan tace
"Kice da shi nayi bacci"
"Amma yaya....." Haliman taso yin qorafi saboda ba sabonsu bane yin qarya
"Don Allah ki fita ki bani guri ki gaya masa yadda nace din ko kisan me zaki gaya masa" ganin sumayyan ta harzuqa har haka wanda basu saba ganin hakan tattare da ita ba ya sanya ta juya ya fice ba tare data amsa wayar dake ta faman kururuwa ba.

*****     ******    *******

       Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya haka take wuni sukuku,ga maganar abdur rahman dake mata amsa kuwwa a kai,gefe guda kuma ga luqman daya matsanta da kiran waya ba dare ba rana,duk da ko daya bata taba amsa wayarsa ba amma hakan bai sanya ta gajiya ba.

        Gani take baki daya abdur rahman ta shigo da maganar ne don ya dagula lissafinta,domin shi kansa yasan yana magana ne kan abinda bashi yiwuwa,ta yaya zata aure shi bayan ta auri dan uwansa?,ta yaya zata yadda ta sake maida kanta cikin ahalin da bata da farinjini ko sau daya a gunsu?,ahalin da tasha wahala tasha jinyar zuciyarta duk a kansu,ahalin da basu ganin alkhairi tattare da ita?,duk a ture ta wannan ma yaushe zata aure musu abdur rahman?,matashin saurayin da ko auren fari baiyi ba?,sam bata jin zata iya wannan abu koda a mafarki ne ballanta na kuma a gaske.

        Ranar da ta fara amsa wayarsa suna zaune ne baki dayasu a falon maman suna cin tuwon dare wayar haliman ta sake tsuwwa karo na wajen uku kenan,mama ce da ringing din wayar ya soma damu ta dubi halima
"Wai halima idan ba zaki daga wayar nan ba ki kashe ta mana haba"
"Mama bani ake kira ba yaya ake kira,yau kusan kwana hudu kenan wlh taqi ta daga ko sau daya" sai maman ta juya tana suban aumayya wadda ta cika tayi fam sabida halima ta gayawa maman
"Ke sumayya wake kiranki" cikin murya mai kama da shagwaba wanda sau tari idan ranta na bace bata aon magana haka yanayin muryarta ke komawa tace
"Wani ne nima mama ban sanshi ba"hade rai maman tayi sannan tace
"Ha'aa,baki sanshi ba kamar yaya?,ina cewa ke kika bashi lambar ko?" Dan jim tayi sannan ta gyada kai
"To maza bana son shashanci karbi ki amsa kirab,na gane take takenki sarai,kuma kinfi kowa sani malam ya fara maganar baiga kina magana da wani ba,kinsan halinshi sarai tun da can baya ma shi ba mai barin yara su girme a gabanshi bane,su kansu su halima rashin tsayayye ye ne ya sanya har suke gida iwar haka" gabanta ya fadi fargaba ta lullubeta,wani irin aure kuma?,duka duka mutuwar auren nata da bai wuce shekara biyu ba?,tilas ta karbi wayar ta miqe ta shige daki.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now