Babi na dari da biyar

21.8K 1.3K 266
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana bayyana kansa cikin qur'ani mai girma da*

*FA'AALIL LIMA YURID(mai aikata abinda yakeso*

*ya Allah muna gareka kayi mana jagoranci*
_____________________________________

*Wannan shafi sadaukarwa ne ga*

*HAUWA'U AG tare da diyanta AHMAD*

        Ba wanda ta amsa sallamarsa a cikinsu,hakan ya sanya sumayya tayi wucewarta ba tare data sake cewa komai ba.

        Satinsu biyu dai dai a kano suka koma dubai,bayan sun ziyarci gidan maimmartaba sarkin rano,mahaifin ummi,tsoho mai ran qarfe,karon farko kenan da sumayya ta kai ziyara,tsantsar soyayyar da tsohon kewa almustaphan ta shafi sumayya,kowa haba haba yake da su yana neman wajen ajjiuesu,taga kara taga karamci,ba qaramin dadi zuwan yayi mata ba,duk da bata samu zuwa gidajen sauran 'yan uwa ba,amma tayi alqawarin duk sanda tazo kano toba shakka zata sake zuwa musu,kyautar girma tsohon yayi musu shida matanshi,duk da mahaifiyar ummi ta rasu,amma matan baban nata sun daukeata tamkar diyarsu,suna farinciki da juna suka rabu,tun a sannan ummi taso riqe sumayya har sai ta haihu amma almustapha ya shafawa idonshi kwalli yace ba yanzu ba zai kawota idan lokacin yayi,yayin da cikin zuciyarshi ma sam ba haka bane,don baida niyyar kawota din,yana ganin meye amfaninsa a matsayinsa na likita kenan.

      A hankali kwanaki suka ci gaba da wucewa,ba abinda ta daga qafa ko ta sauya game da kyautatawar da takewa almustaphan,dukkan wani abu data sani cewa yana so takan sanyashi gaba da komai nata,lamarin su'ad kam sam baya damunta,duk wani iskancinta da tambotsanta basa gabanta,sai taga dama ma zata ganta bare wani sabga ya hadasu,abu daya take qoqari a kai shine tausar almustapha a duk sanda ta kunnoshi,sam bazata so ace su'ad din tabar gidan na,kullum fatanta shine Allah ya shiryata ta gane illar abinda take yi,ta tabbatar da cewa duk duniya bata da wata mafita matsawar almustapha ya sawwaqewa su'ad tofa za'a ce itace sila,bayan duk wanda zaiyi alqalancin baisan meke wakana game da zamantakewar auren su'ad din cikin gidan ba,saidai hasashe dai kawai.

       A haka cikinta ya shiga watanni tara har ya soma yunqirin shiga na goma,kallo daya zaka mata ba zaka so sake dubanta ba sabida tausayi,sosai cikin yayi wani girma har wani lokaci sai ta tallafeshi idan tana tafiya saboda girmansa da yadda ya sauko qasa,ta sauya kamanni sosai kamar ba sumayyan ba,munin da tayi a da nafila ne,har bata son kallon kanta a mudubi,sau tari idan taga almustapha na kallonta sai ta kau da kai tana tunanin munin da tayi yake kallp,saidai shi sam ba haka bane cikin zuciyarshi,tsananin tausayinta ke damunshi,ba don kada yayi riga malam masallaci ba da tuni ya yankata ya cire mata cikin ta huta,yakan tallafo fuskarta ya saki murmushi
"Ki daina boyen fuskarki,a hakan kinmin kyan da ban taba ganin kin yimin irinsa ba,kinsan me?" Sai ta kada kai cikin murmushi
"Da zaki sake zama haka nan da wata takwas ma bayan kin haife wannan cikin ina so,da nafi kowa murna"
"Kayimin addu'a Allah ya rabani da wannan ma lafiya"
"Yadda zuqar numfashina ya zamemin dole haka wannan addu'ar ta zamemin dole" ya fada yana karata da jikinsa tare da shafa bayanta a hankali yana ci gaba da yi mata addu'a cikin ranshi.

       Semina ce ta kamashi ta sati guda wadda za'a yi a china ta 'yan kasuwa,sam yace ba zashi ba,ita ta tausashi da qyar tace ba'a jiran haihuwa sai sanda Allah ya kawota,ko kadan baison tafiya don ko fita ya rage,tausayi take bashi matuqa,hatta tashi sai tayi da gaske take iya yinsa ko shi ya dagata,ita ta tayashi hada kayanshi tana yi tana tsokanarshi wai ya zama rago,jawota yayi jikinsa yana dan mintsinarta yadda ba zata ji zafi ba yana murmushi
"Laifin wa?uhmmm babe,bake kika maidani haka ba?" Dariya ta saki,ta jawo hannunsa ta dora saman cikinta
"Laifin wannan ne ba nawa ba"sake matseta yayi a jikinsa yana sakin murmushi,tasan duka hanyar da zata sashi nishadi.

       Sai da ya hadata da babban asibitin dake qasar wanda anan yake musu aiki lokaci lokaci,ya basu lambarta lambar gidan da adress,sannan itama ya bata number dinsu,sannan ya karba mata nurse guda daya wanda suka tanada saboda jinyar marasa lafiya wadda zata dinga zuwa tana kwana da ita,sam bai fadawa ummi ba don ya tabbatar cewa zatayi ya turota nigeria,shikuwa baison ko daya abinda zai rabashi da ita dai dai da minti daya

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now