Babi na casa'in da tara

18K 1.3K 276
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*duk wanda ya aikata daidai da qwayar zarra na alkhairi(komai qanqantarsa) zai gani(cikin littafin ayyukansa,zai ganshi a rubuce kuma za'a masa hisabi da hukunci a kansa),hakanan duk wanda ya aikata dai dai da qwayar zarra na sharri zai ganshi.
__________________________________________



          Tun daga lokacin sumayyan ta zubawa eesha ido cikin nutsuwa,tana kula da takatsantsan da duj wanu taku nata,a bangaren eesha kuwa ko daya bata sauya qudurinta ba,ko da yaushe tunaninta daya na yadda zata illatar da sumayyan ne.

   ******    ******    *******

      Qarfe goma da rabi ranan ta sauko bayan farkawarta daga bacci wanda kusan almustapha ne ya tasheta,sai data gama biye masa sannan ta shiga tayi wanka ta shirya ta sauko don ta karya,bata da damuwa tasan cewa komai na shirye,tun daga randa wancan abun ya faru bash sake barinta shiga kitchen ba.

        Tare suka sauko da sajida,ummi na sashen anty maamaa,sajida ta wuce dining don ta karya,ita kuma kiran halima da ya shigo wayarta ya sanya ta wuce saman kujerun falon ta zauna tana amsawa,qarar sajida data jiyo shi ya sanyata sakin wayar ta miqe,bata jin nauyin jikinta haka ta nufi sajida da tayi zaman 'yan bori saman step na dining area,wajen ta isa tana dagata gami da tambayarta
"Faduwa nayi anty" ta bata amsa tana shirin sakin kuka saboda qafarta ta bugu sosai,idanunta sumayya ta kai wajen sai taga ruwa ne ya zube wajen
"Ya akayi kika zubda ruwa haka sajida?"
"Bani bace nima haka naga wajen,kuma ban kula ba har sai da na fadi" wani tunani ne ya darsu ran sumayya,ta sanya hannun ta cikin ruwa sai taji yana santsi da qanshin klien,to waye ya zubda ruwa haka?,tasan cewa babu yadda za'ayi ma'aikatan su zubda ruwan su tafi ba tare da sun gyara ba,ummi bata nan sajida ba ita ta zubar ba
"Eesha" zuciyar sumayya ta raya mata,kai ta girgiza,batason ta zargeta bayan bata gani da idanunta ba,riqe sajidan tayi don dawo da ita saman kujera,tana juyowa suka hada idanu da eeeshan,sai ta juya ta shige dakinta,mamaki ya kama sumayyan,wai me eeshan ke nufi,take ranta ya baci,ta zaunar da sajida saman kujerar ta kama qafarta tana mammatsawa,gefe guda ke mata ciwo,sai ta isa bakin dispenser ta tari ruwan zafi ta dawo kusa da sajidan ta gasa mata qafar sosai,cikin ikon Allah wajen ya saki,ta shafa mata man zafi a wajen sannan taje da kanta ta goge wajen sannan ta hada mata abin break din taci ta kwanta.

       Tana saman kujera zaune kanta a qasa,ranta a tsananin bace yake,don me zata dinga neman cutar da ita?,tana tunanin dai dai gaggawar unguwar zoma ta bari a haihu ko?,ta bari su hada miji tukunna,meye na hanzarin son cutar da ita tun yanzun,saqar data dinga yi kenan cikin zuciyarta,qara qofar dakin eesha tayi,itace ta bude ta fito,tana tafe dai dai ta hura hanci,idanunta da suka kada saboda bacin rai ta zuba mata
"Aisha..." Ta kira sunanta cikin kakkausar murya wadda ta sanyawa eeshan tsayawa ta kuma juyo tana dubanta
"Jan kunne nakeso nayi miki na qarshe....duk abinda zakiyi kiyi qoqari ya tsaya iya ni,kada ki bari sarkarcinki da haukanki ya sake taba wani cikin gidan nan,yanzun da kin karya musu yarinya kuma kice me?,haka rannan kika watso ruwan zafi saura kadan a fuskar sajida,kina gidan kakanninta kina cin arziqinsu kina neman salwantar musu da jikoki?"maganar sumayyan ta qarshe ta sosa mata rai,ita zata yima gori bayan ita ya cancanci ta yiwa gori
"idan kuma banji jan kunnen naki ba me zaki iya diyar malamai masu ci da buzu da tawada?"murmushi ta sake mata sannan ta bata amsa cikin nutsuwa
"alhamdulillah da na kasance diyar malamai magada annabawa,zancan rashin jin gargadina kuwa....koni zan iya miki hukunci.....amma da yake ni din mai uwace a gindin murhu,kunnen mutum daya maganar zata je kiga yadda dunuyarki zata gigita" ta fahimci sarai tana son hadata da almustapha ne ko shi ko baba,to har gwara ma baban akan shi din,kuma ta sani sarai qarshen lamarin bazai mata da dadi ba
"Duk abinda zakiyi baki isa ki hanani shiga gidan almustapha ba wallahi,baare ma ya sameshi bare kuma na gida" murmushi ta kuma yi
"Kan me zan hanaki dama?,nima fa wata ta taras,sannan kuma ba kanku na soma zama da abokan zama ba,abu guda kawai nakeso daga gareki.....koda zaki auri almustapha to ki kiyayi taba lafiyar jama'ar da basu ji basu gani ba.....ki taqaita haukanki....ki adana shashashanki har zuwa sanda zaki shiga gidan nashi"tana yunqurin maidawa ummi tayi sallama,hakan ya sanyata dole yin shiru,bata ji ke suke fada ba taga dai sajida kwance
"a'ah lafiya kuwa?" Ta tambayi sajidan tana dubanta
"Ruwa ne ya zube sai na fadi" ta bata amsa,gefe ummin ta samu ta zawa
"garin yaya ruwa ya zube a wajen?" Ta tambaya cikin mamaki,wannan karon sumayya ce ta karbi zancan
"Wallahi ummi,sashen dai ba kowa,ni da ita kuma tare muka sauko sai ihunta kawai naji" waiwayawa ummin tayi tana duban eesha
"Aysha ya akayi ruwa ya zube wajen?"
"Nima ummi ban sani ba"
"Bake na bari wajen ba kina karyawa?" Sai ta langabar da kai
"Tea ne ummi,ina so ma goge kuma na mance naje na kwanta"
"Amma ya kamata ki dinga kulawa tunda kinsan yadda wajen nan ke da santsi,ko su lami kika saka zash goge,yanzu da amira ce ta taka wajen Allah ne kadai yasan me zai faru,ki kula sabida gaba"
"To" ta fada tana zumbura baki ta koma daki,ranta cike fal da baqincimi,ita wacce iriyar mara sa'a ce,kuma wai ummin har take goyon bayan wata bare a kanta,lallai kam ba zata qyake wannan abu ba zatayi mai gaba daya ne kawai komai ta fanjama fanjam,ruwa ummi ta buqata ta gasawa sajida wajen,sajidan tace ai anty ta gasa mata,hakan yayiwa ummin dadi,daya daga cikin abinda yasa har kullum take sumayyan ke sake shiga ranta kenan sanin ya kamata,ba qaramin jin dadin zama take da ita ba,ba shakka da zaiyiwu riqe sumayyan zatayi wajenta har ta haihu,amma tasan hakan ba maiyiwu wa bane,ita kanta tasan alkunya almustapha kawai yake mata,wanda dukkan alamu sun nuna ya fara gajiyawa,don ya soma yi mata qananun qorafi,ko haka kawai ba gaira ba dalili sai ya dinga tashinta cikin dare yana sata kaiwa sumayya waya.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now