Babi na hamsin da uku

7K 545 34
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

HAQIQA SHAIDAN ABOKIN GAABARKU NE,KU RIQE SHI ABOKIN GAABA

Afuwan nayi mistake na number,yau ne zamu tashi page na 53

___________________________________

        Yanayin sanyi ya fara ja baya,yayin da zafi ya fara sako kai,wannan shike nuna alamu na tahowar damuna,mafi yawanci lokutan zafi bata iya bacci mai yawa,hakan shi yake sanya ta tashin wuri,qarfe goma tuni ta kammala ayyukan gidab,bata ma jirayi tashin zainab ko halima ba,wanka tayi ta sanya kaya sa'annan ta debi kayan kari daga kitchen ta shiga falon mama,a zaune ta sameta itama tana gyara mafitai tunda lokacin amfaninda su ya zo,kasancewar ba ko da yaushe ake samun wuta ba,nan ta zauna tana karyawa suna hira da mama,bayan ta kammala ta dauko kayan hadin humrarta tana fadin
"Mama bari kiga na fara hadawa anty dije tata,saura kwana biyar tazo kada lokaci ya quren"
"Ai kam don idan tazo baki matan ba ke da ita,ya taku kada ku sakani ciki" dariya sumayyan ta danyi tana bude robar ruwan turare
"Ai ba'a shiga fadan uwa da d'a mama,Allah mama tun ina mamakin irin qaunar da anty dije kemin har naxo na daina" murmushi mama tayi
"Ko sanda muna gida tamu tafi zuwa daya ai,dana haifi abubakar lokacin bata yi aure ba cewa tayi da sai ta karbeshi,sanda na haifeki kuma basa garin nan ita da farouqu da tuni gunta zaki tashi,kinga kuma kina da shekara sha uku aka aurar da ke" kai take jinjinawa tana hadin humrar tare da jin dadin labarin da mama ke bata.

      Halima wadda bata jima da tashi a bacci ba ta shigo dauke da wayar dake burari sumayya wadda gunta wayar ta kwana tana miqa mata
"Yaya ana kiranki" kanta ta daga ta dubeta
"Waye?"
"Baquwar lambace" ta daga mata kiran sannan ta miqa mata,karawa tayi a kunnenta tana mai sallama daga daya bangaren aka amsa mata sannan ta buqaci sanin waye,ajiyar zuciya ya saki yana lumshe idanuwansa
"Amma kam banji dadi ba da har cikin sauri haka kika manta da ni sumayyah" gabanta ne ya fadi,idan ba gixo kunnenta ke mata ba muryar lukman ce,dakewa tayi cikin qarfin hali tace
"Ba abun mamaki bane don na mance muryar wanda ban sani ba" dariya ya dan saki sannan yace
"Lukman ne sumayya,lukman tsohon mijinki wanda kuma yake fatan sake zamantowa mijinki a karo na biyu" jikinta ne ya dauki bari,sai kawai ta katse wayar tana duban halima da ta zuba mata ido tana kallonta,mamanta shiga uwar daki maida mafitan
"Halima lukman ne wai" ta fadi muryarta na rawa
"Mene?,me ya gaya miki?"
"Ba komai"
"Shine kuma duk kika bi kika rude yaya,har yau kamar mune yayun kece qanwar wlh,kinga,ki tsaya kiji me zai fadi bawai ki katse waya ba"
"Cewa yayi tsohon mijina mai kuma fatan sake zama mijina"
"Dole aka ce haka ce zata tabbata?" Ta tambayeta tana kallonta,shiru tayi bata amsa mata ba,ganin bata da alamar ansawa ya sanyata juyawa zata fice,sai sumayyan ta niqa mata wayar tace ta tafi da ita.

       Gabanta ne ya dinga faduwa,sai aikin nata ya koma sukuku sabanin dazu da take yinsa cikin karsashi,har mama ta ankara saidai bata tambayeta ba,tana zaton ko mukhtar ta tuna,da yake yawancin lokuta haka na faruwa da ita idan ta tuna shi,tana shirin miqewa ta adana kayan haliman ta sake shigowa riqe da wayar,idanuwa ta tsareta da shi
"Ya aka yi?"
"Ba lukman bane wannan karon ya abdur rahman ne" tsaki ta ja tana ci gaba da ayyukanta,ta gama lura da take takensa
"Duk kanwar ja ce,dauki kice bana kusa"
"To" haliman ta fada tana daga wayar gami da ficewa daga dakin.

      Sai bayan kusa awa daya sannan ta dawo dakin tana dariya ta dubi sumayy
"Wlh yaya kin ban kunya,kinga ya abdur rahman ya gane fa,cewa yayi har da ni a yi masa qarya ko,yace zaya zo anjima zamu hadu" shiru tayi ba tare da ta ce komai ba,bata fata ko buri abdur rahman ya dora daga inda ya tsaya wajen yada manufarsa,domin a yanzu bama abdur rahman ba,bata buri kowanne namiji ya sota,don kwata kwata bata ji a rayuwarta zata iya sake yin aure,idan tayi tana jin kamar taci amanar mukhtar ne,gwara taci gaba da rayuwarta a haka har itama tata tazo ta tadda ita ta hadu da mukhtar dinta a jannatul firdausi.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now