Babi na saba'in da biyar

16.1K 1.2K 318
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ALLAH S W T YANA CEWA*

*ALLAH BAYA JINKIRTAWA WATA RAI IDAN AJALINTA YAZO*
______________________________________

        Wannan karo anty dije daga ita sai yaranta suka koma abuja cike da kewa,kowa cikinsu sai yaji babu dadi,kasancewar sumayyan ta riga ta shiga jikinsu.

         Sati guda malam ya yiwa baabaa maganar ya za'a yi da jeran sumayya,ce masa yayi babu ruwanshi wannan ba huruminsa bane,murmushi kawai malan din yayi
"Ku qarata kai da 'yar taka" ya fada yana dariyaanty dije ce ta matsa kan ko daki daya abasu su saka mata kaya,tilas baabaan ya sanya aka bude daki daya dake saman aka basu shi suka saka kayan gadon da malam ya siya mata,idan baku manta ba gidan baabaan na da sashe biyu ne,ko wanne sashi akwai sassa a ciki,sashin daya barwa yaran nashi daya na wansu ne adam da matan shi,daya nasu mahomud ne da mus'ab,daya na almustapha ne,kowanne sashi yana dauke da balcony sama da qasa,sannan babban falo da dakunanan bacci manya manya wanda zasu iya cinye kayan gado set biyu,bedrooma din cikin corridor suke wanda ke hagu da daman falon,sai ka fito daga ciki zaka samu falon,sai qofar kitchen daga can gefe wanda qofa daya ce amma idan ka shiga zata tadda qofofin kitchen biyu biyu,akwai wata qofar daban da zaka fita vantilation,kusa da kitchen dining area ne,saman babban falo ne shima da dakunan bacci guda uku,daya ne makeke wanda a ciki mustaphan yake,kowanne sashe nada girma da yalwa,duk yadda ka kai ga son jin dadinka.

        Dakunan baccin duka guda biyun again dake qasa baabaa yasa aka shirya mata su ba tare da sanin kowa ba,illa ya yiwa kamfani waya ya basu adress,royal beds ne set dinsu masu azabar kyau da tsada,hakanan kitchen din aka zuba qawata shi da dukkan wani kayan qawa da kayan amfanin buqata na kitchen,falon ma ba'a barshi haka ba,sai da ya sanya aka sauya duk wani abun amfani,a taqaice dai tashin farko sashen ya sake sauyawa sosai,duk da dama sashe ne wanda ya tsaru ya qawatu tun da can,yafi kowanne sashe kyau da qyale qyale,kasancewar mai sashin mai son tsafta da gyara,yayin da matar sashen ta zama mai dagawa da son nuna iyawa da kuma qaunat ganin tafi kowa.

       Ba wai don almustapha bai da wani gida ba,yana gidan daya kusa a qalla shekara hudu ana gininshi yana narka masa kudi,har rade radi aka dinga yi a rean cewa da qyar idan ba gidan wani shugaban wata qasar vane,babu abinda bai zuba ba a cikin gidan,dai dai da cokali gidan baya buqata,hatta da kayan sangawa baki daya cupboard din gidan a cike take,wani irin tsari aka yi masa mai bala'in kyau da daukar hankali,hatta da qasashen da suka ci gaba samun irin wannan gidan sai an tona,to saidai babu wanda yasan da gidan do ba wanda ya gayawa,shi wani irin mutum ne da bai fiya son fadin abubuwan da yake yi ba,da fari yaso maida su'ad ciki,saidai irin rayuwar da yake so ya shimfida cikin gidan ba ita ta shiryawa yi ba,rayuwar soyayya da kulawa zalla tsagwaronta yakeson shimfidawa cikin gidan wanda dama ya ginashi ne don ya morewa rayuwarshi da arziqin da Allah ya mallaka masa,duk sanda ya kalli gidan yana sanyashi nishadi da walwala,ya zuba ido yana jiran yaga ranar da su'ad zatayi daidai da tsari da ra'ayinsa,ta shiryar karbar irin rayuwar da yake so,to a lokacin yake saka ran maidata gidan wanda har yanzu hakan bata samu ba,a qalla kusan watanni shida kenan da kammala komai na gidan,saidai lokaci lokaci idan yana buqatar kebewa ko hutawa yaje ya wuni ko ya kwana daya ya dawo,cikin dribobinsa ma mutum daya kacal yasan da gudan kasancewar shi ke kaishi.

  *******  *******    *******

      Duk yadda taso kauda da damuwa cikin ruhinta ko don saboda malam abun yaci tura,a yadda take yaqe da qoqarin zama cikin mutane duk da gidan nasu yanzu sun sake raguwa,daga ita sai mama,abdallah ma yaqi zama kasancewar gidan yayi shiru da yawa,ya gudu wajen yaya yahanasu don acan yake baje kolin tabararsa yayaan da su jamila na biye masa,ga yara 'yan wasa kamarshi,kana duban sumayyan kasan akwai kwantacciyar damuwa a zuciyarta,a hankali ciwon marar ke sake matsanta mata wanda ta kai ga cewa har sai ta sha paracitamol wani lokaci yake barinta tayi bacci.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now