Babi na ashirin da biyu

9.1K 812 68
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ma yaftahillahu lin nasi min rahmatin fala mumsika laha,wama yumsik fala mursilalahu bin ba'a dihi*

_Allah ka sanya mu daga cikin wadanda zaka yita saukar da rahamarka garesu,alfarmar sayyadina rasulullahi S A W_
_______________________________

         Hannu ya sanya ya amsa,sai ya latse wayar ya kasheta baki daya ya ajjiyeta gefansa yaci gaba da aikinsa,wanda yana duba yanayin ginin gidansa wanda a yanzun ake daf da kammalashi
"Sai da na gaya miki kada ki daga" ya fadi idanunsa na kan computer din,cikin wata iriyar mutuwar jiki da kasala ta lallaba ta koma kan kujerar data tashi taci gaba da kallonta,saidai sam ta daina fuskantar komai,wani abu mai kama da zazzafan kishi ne ya shiga taso maga,ta dinga ambaton sunan Allah har zuwa sanda suka qare film din ta koma dakin gadonta.

           Sam bacci yaqi zuwa mata face nazari da take tayi ita kadai har mukhtar din ga gama abinda zaya yi ya cimmata akan gadon,jikinsa ya janyota sannan cikin taushin murya yace
"Meke faruwa ne sumy uhmmm?"
"Babu komai" ta furta can qasan maqoshinta
"Ban santa ba nina sumayya,abinda kawai na sani customer dina ce,tazo shago na siyayya ita da 'yan uwanta,ta buqaci number dita saboda koda zasu tashi zuwa wani lokaci,tun daga ranar take matsanta min da kira ba yau ta fara ba,na gargadeta na kuma ja mata kunne amma bata ji ba,wannan shine abinda na sani" shiru sumayyan tayi taba nazarin maganar,sosai wani kishinsa ke taso mata
"Allah ya kyauta" ta iya cewa kawai,sai ya juyo da ita ta fuskanceshi
"Haka ma kadai zaki fada ko?,wato ma baki kishi na kenan sumayya" ya fada yana matse mata yatsu har sai da taji zafi ta saki 'yar qaramar qaara,sai ya hade bakinsa da nata cikin wani irin salo da ya mantar da su komai

         ***     ***       ***

            Ta maida kiransa ya zame mata tamkar ibada,idan ma bai daga ba zata yita jelan tura masa saqonni iri iri wadanda dukkaninsu a akwatin share saqonni yake zuba su.

           Sau tari wani abun dariya yake bawa sumayya,tana mamakin yadda mata suka sauke farashinsu ya fadi qasa warwas,tana jin inda ita dince sam ba zata iya haka ba,ko babu komai akwai kunya irin ta diya mace,duk da ta sani cewa koda matar ma'aiki ta farko nana khadijatul kubra ta nemi ma'aiki da ya aureta,amma bata irin wannan sigar bace,ta siga ce mai tsafta,mai ban sha'awa mai cike da hankali nutsuwa da kuma KARAMCI,sa'an nan ta nemi a aureta a inda take da yaqinin samun qauna da kulawa,a 'inda ko babu qauna akwai tausayi girmamawa da kuma MUTUNCI.

            Sau da dama idan saqonni da kiran ZAINAB ya ishi mukhtar yakan zauna yayita sababi,sai ta sa baki da haqurqurtar da shi,wani lokaci kuma ta zolayeshi shi kuma ya bita da harara,ko ya ranqwashi kanta,a haka lamarin yaci gaba da wanzuwa har tsawon watanni uku cur babu sassauci haka na babu sauyi.

*Wace ce zainab?*

       Zainab haifaffiyar garin kano wadda ke zaune cikin unguwar sheshe,suna da rufin asiri dai dai gwargwado,gida ne wanda ya kasance ya samu rarrabuwar kai da sabanin mabanbantan ra'ayi ga jama'ar gidan,maman zainab itace amarya a cikin gidan yayin da zainab ta kasance 'yarta ta uku baya ga maza biyu da ta biyo,mama amarya mahaifiyar zainab ta zamewa mata biyu data tarar cikin gidan qarfen qafa,babu wanda ke da fada a ji cikin gidan sai ita,ita ke juya kowa ciki harda mai gidan,taci karenta babu babbaka har zuwa lokacin da Allah ya yiwa mai gidan rasuwa aka raba musu gado kowa ya kama gabanshi,koda zainab tayi auren fari mama amarya ba irin mijin da take so zainab din ta aura ba kenan,miji take so ta samu koda ba mai kudi ba amma yana da abun hannunsa,wanda zasu maqale suyita tatsarsa suna tara abun duniya,talaka ne bashir futuk,qarfin soyayyar da zainab din ke masa ya rufe mata idanu har ta aureshi,tayi aurenta ne bayan data kammala kataratun ta na NCE a federal college of education kano wato FCE,kusan zamu iya cewa bashir abokin karatunta ne tare suke daukan lactures course dinsu daya,bayan kammala karatu kuma aiki bai samu ba,sai shagon wani maqocinsu dake kasuwa yake zuwa yana masa jira ana biyansa.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now