Babi na arba'in

10.6K 925 111
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*innal laha la yugayyiru maa bi qaumin hatta yugayyiru ma bi'an fusihim*

_haqiqa Allah baya canzawa mutane(halin ko yanayin da suke ciki)har sai sun canza da kansu_

______________________________

        Ungawa ce mai matuqar kyau da tsari,akwai nauikan mutane daban daban cikinta,saidai akasarin mzauna cikinta din masu hannu da shuni ne da kuma masu rufin asiri ko wadanda suke ma'aikatan gwamnatin tarayya ta basu gida su zauna kamar su anty dije.

       Sai da mansur ya fidda kayanta baki daya ya shigar mata cikin gidan ta masa godiya sosai sannan ya ja motarsa ya shige wani katafare kuma hamshaqin gida dake kallon nasu.

         Dukka yaran gidan na nan kasancewar ranar qarshen mako ce,laila ita ce babba,sai hafiz mai bi mata,sannan khalifa sai nasir sai auta amina minal,a qalla laila zata yi shekaru goma sha hudu,ita ta fara ganin shigowar sumayya falon,ihu ta sanya wanda ya janyo hankalin 'yan uwanta ta nufi sumayya ta rungumeta,haka sauran suka baibayeta wanda ya janyo musu faduwa a qasa dukansu suna dariya,da qyar ta samu suka dagata suka koma saman kujera sannan ta soma tambayarsu anty dijen don bata ji motsinta ba,dining laila ta nuna wa sumayyan tana cewa
"Kinga yaya sumayya can duka abincinki ne,tun dazu mama ke jiranki baku iso ba har ta gaji ta shiga gidan daddy prof,amma bari naje na kirata" ta fada tana yafa dan yalolon mayafinta tayi waje da sauri,khalifa sumayya tasa ya fara nuna mata toilet ta shiga tayi alwala,tana kammala alwalar anty dije na shigowa
"Sai yanzu?,gaskiya kunyi nauyi a hanya kamar wadanda suka hau motar haya inji hajiya bilki" murmushi sumayya tayi tana duban anty dije wadda ta sake gogewa bisa dukkan alamu zaman garin ya karbeta matuqa,ta kuma zama 'yar gayu ita da yaranta baki daya
"Wallahi anty sai da muka biya kasuwa muka karbo wasu kaya sannan har mun dau hanya wani oga ko yallabai ya maida ku zoo road karbo dinki"
"Eh inaga man ne dinkunan su'ad ce,maza yi sallar kizo kici abinci kafin mu zauna hirar yashe gamo" ta fada tana sanya su laila dauke akwatunta zuwa wani daki da aka tanada saboda baqi irinta.

      Sai da taci ta qoshi sannan suka baje a falon ana hiran yaushe gamo,kusan haka suka qarar da wunin ranar,ko da malamar lesson din yaran ma tazo guduwa sukayi suka qi zuwa sai tafiya tayi,da dare ma yayi da qyar suka tafi dakinsu don cewa sukayi tare da sumayyan zasu kwana,saida anty dije ta korasu saboda tana son suyi zance,sosai suka sake kuwa don mai gidan ta baya nan sun tafi semina lagos,sosai anty dije ta sake kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari ta rufe da fadi cikin sigar tsokana
"Duk da nasan sumayyan tawa zuwa yanzu ta fara girma,hankali ya fara zuwa mata" itama dariya tayi,sai wajen sha daya da rabi sannan ta fita ta barta,to nan din ma lukman bai barta ba da hira sai data ce tana jin bacci sannan yace
"Ki kula min da kanki to na baki amanar kanki my dear kinji"ajiyar zuciya ta saki sannan ta amsa masa ta katse kiran,taso kiran halina taji ya abdallah yake,amma ganin dare yayi nisa ya sanyata ta haqura ta barwa gobe,duk sai taji tana kewar yaron nata.

   ******     ******     ******

      Kwanakin da tayi a garin kwanaki ke da suka yi mata dadi sosai,kullum yaran na nanuqe da ita suna hira,sauqin abun sun gama jarabawa hutu kawai suke jira,wani lokaci da yammaci anty dije kan debe su da motar mai gidan da ya barta a gida ta kaisu park su dan sha iska suyi ciye ciye su dawo,hakan na yiwa sumayya dadi,lallai ko yaya ka motsa daga wani gu zuwa wani gu zaka samu sauyi zuciyarka zata yi dadi.

        Duk wani abu da ya kamata a yiwa amarya anty dije da kanta ta yiwa sumayya,cikin kwana goma ta hadata tsaf.

       Ana ya gobe zasu koma kanon laila na kwance kan cinyar sumayya sumayyan na tsefe mata kitsonta zasu wankin gashi da yamma anty dije ta fito ta dubesu
"zan dan shiga gidan daddy prof zamuyi sallama da su,Allah baiyi da ni za'a yi sunan nan ba"sumayya ta daga kai ta dubi anty dije
" au haihuwa akayi halan?"
"Sai yau zaki tambaya kenan,kwana na nawa ina leqa su amma baki taba karar ki shiga ku gaisa da mutanen ba,direban gidan ya dauko ki daga kano fa,surukar gidan ce ta haihu" murmushi sumayya tayi
"To ai ban sansu bane anty"
"Ni ai na sansu kuma gashi na gaya miki,mutanen akwai tsabar mutunci da karrama mutum,duk yadda Allah ya musu tsabar arziqi amma basu raina na qasansu,mai gidan bakiga yadda ya dauki abban khalifa ba kamar dan cikinsa,su khalifa kuwa ya maidasu tamkar jikokinsa" jinjina kai sumayya keyi sannan tace
"Allah ya saka musu da alkhairi,kice ina musu barka"
"Zasuji tunda ba zaki din ba" inji anty dije ta fice tana mita sumayya ta bita da dariya.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now