Babi na ashirin da shida

8.2K 862 60
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim *

*wa may yattaqil laha yaj'al lahu min amrihi yusrah*

_duk wanda yaji tsoron Allah Allah zai sanya masa sauqi cikin lamuransa_

          Su biyun ne zaune cikin falon kowa na sabgar gabanta,sumayya na guga saboda socket dinta ya lalace ya tilasta mata fitowa falon don yin gugar,yayin da zainab ke zaune saman kujera qafa daya kan daya kamar yadda ta saba zama kenan cikin izza da nuna ita watace,gama share falon da mopping dinta kenan ga zauna don ta huta,duk wanda ke da girki shike wannan aikin,ba laifi zainab din nada tsafta dai dai gwargwado.

          Sallamar da ake zabgawa daga harabar gidan shi yaja hankalinsu,zainab ce ta miqe tare da ajjiye remote din hannunta ta bude qofar ta fita,fadima ce ita da jamila diyar yaya yahanasu,bakinsu a washe suka soma takowa zuwa inda take
"Ku tsaya daga nan da Allah ku cire takalmanku kada ku batawa mutane waje yanzu na gama mopping" da fari jamila tayi dum amma ganin fadima ta tsugunna ta cire nata ya sanya itama dole ta cire,juyawa tayi fuska a cusgune su kuma suka bi bayanta.

           Zama tayi kan kujerar ta maida qafarta yadda take,suna shirin zama saman kujerar da sauri tace
"A'ah,da Allah ku zauna a qasa,ai carfet ne,idan kuma baku iyawa ku tafi can ga nata kujerun can ku zauna a kai" tsabar qin da suka yiwa sumayyan suka gwammaci zama a qasa,suka gaidata ta amsa da qyar,ko kusa baau dubi sumayya dake guga ba,haka suma ko qurar data kwasosu bata kalla ba
"Dama yaayaa ce ta aiko mu gun yaya muntari" inji fadima,wani kallo ta watsa musu
"Bacci yake,ku fadi saqon sai na gaya masa idan ya tashi" shiru suka dan yi sannan suka dubi juna alamar basu son fada,hakan yasa ta dubesh kai tsaye
"Sai ku tashi ku koma da saqonku,ko kuma wadda ta aiko kun tazo da kanta"
"Yaaya yahanasun?" Suka fada tare cikin mamaki
"Eh,ita din mana,to meye?,kunga ku tashi ku bani guri da Allah,muta ne sai shegen binbinin tsiya haba" ta fada tana jan tsaki tare da mai da kanta gun t.v.

         Zuciya ce ta zowa jamila wuya,bayan sun miqe sai ta kasa shiru
"Kema halin fa'izan gareki?,lallai akwai butulu a duniya da yawa,to wlh bari kiji,baki isa ki shiga tsakaninmu da dan uwanmu ba wallahi"kallon banza ta yi mata sannan ta saki murmushi tana kada qafa
"A'a'ahhhhhh.....yaro man kaza,quruci dangin hauka"
"Ke za'a gayawa wannan ai mahauk......."
"Idan kika sake bakinki ya qarasa wallahi sai na tashi na tsitstsinka maki mari,na kuma tattaka ki naga wanda ya tsaya miki...." Ganin yadda ta yunquro kamar zata sanya musu dukan ya sanya fadima ta janyeta suka fice jamilan na ciccika baki tana cewa "ai umman zata zo naga uban da ya isa ya hanata ganin dan uwanta,mata duka sai shegeb butulci duk wadda ka yiwa rana sai ta yi maka dare" itakam sumayya na gefe,ci kanku bata ce ba balle ta dago ta dubi abinda ke faruwa,tana jin zainab din na ci gaba da banbaminta mai kama da jirwaye da kamar wanka
"Ni wallahi babu wata yar miji da zata shiga rayuwata tunda ba ita ke aurena ba,idan da can an saba muku toni wallahi bazan lamunci a dinga tatsemin miji ba" ita dai ko kallo bata isheta ba,cikin hakan mukhtar ya fito sanye da doguwar riga jallabiya
"Ke dawa haka ina daki ina jiyoki?"
"Ni da danginka mana,haka akeyi basu da aiki sai zuwa roqo tsakani da Allah?" Zancan sai ya baiwa sumayya mamaki,iko sai Allah,ke kudin nan ba naki bane,kuma wanda suka roqa din ai dan uwansu ne ko?.
Tsaki yaja yana zama kan daya daga cikin kujerun
"Kudi take so zata biya kudin makarantar yara,na kuma gaya mata tayi haquri ribar hannuna na baki zaki fara saida mayafai,kasuwa kuma yanzun sai a hankali ba kamar da ba amma ta qi yarda,gwara da suka tafi din don ko sun sameni ba ni babu abinda zan iya bayarwa"
"Ato nidai na kora musu jawabi" ta fada tana tafa hannuwa
"Samamin ruwan zafi du Allah" ya fada yana kashingida.
"Gaskiya muntari na fara gajiya,aikin gidan nan fa akwai wuya kawai ka sama min mai aiki" ta fada a shagwabe,murmushi ya danyi sannan yace
"Kada ki damu,kafin a kama azumi za'a samar mikin ki bada cigiya"fari tayi da ido cikin salo" kai dear na ko gode....bari na kawo maka"miqewa tayi tana wani rangwada tare da sakin wani dan qaramin fito na jin dadi,a duniya bata da burin wulaqanta sumayya,tunda ita taqi samuwa to ko ta hanyar mukhtar din kawai ya isheta tunda tana cimma burin cusguna mata.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now