Babi na goma

10.1K 869 95
                                    


*wa ufawwidu amri ilallah,innal laha basirun bil'ibaad*

Yau kam da ta dora girkinta zama tayi cikin kitchen din tana kallo cikin wayarta har takammala girkinta,duk da cewa yau din akwai sauqim zirga zirgar fa'izar tana daka tana jinya,yau daga ita har yaranta sun wataya abunsu.

Yau ma tare sukaci abincin dare,saidai babu fa'izan,don tun sumayyan bata jima da kammalawa ba ta fito ta kamfata ta fice,ita kam sumayyan mamakin shege cin abinci irin na fa'izan take.

Abin jiya akaso a maimaita ko kuma nace har ma ya wuce na jiyan,don kusan har da dambe ne yaso kaurewa tsakanin fa'izan da mukhtar din,ba wai don tana burgeshi ko abinta ya dada shi da qasa bane ya sanya shi dagewa kan sai yayi,ko kadan,yana so ne ta bambance tsakanin aya da tsakuwa,yana so ne ya dasa mata qin abun ta yadda ba zata sake marmari ko gigin nemansa ba.

Iya wuya kam ta shata don har taso ta zarta ta jiya,don yau har mikin jiya sai da ya dawo sabo fil baya ga sabon da ta yo guzirinsa,kamar jiya haka yayi fitarsa da asuba,saidai wannan karon a masallaci yayi zamansa har gari ya ida wayewa,shi kadai ya dinga murmushi saboda yasan ya gama koya mata lesson.

Tun daga ranar ta shiga kulle qofarta,dariya ya dinga yi cikin zuciyarsa yana fadin
"Ta dauka wani damuwa akayi da abinta,bata san ko giyar wake na sha bazan sake rabarta ba" kewar sumayyansa ce kawai take damunsa sam fa'izan bata a cikin lissafinsa.

Har ta qarasa cinye kwanakinta bata sake yarda ya kwana dakinta ba,haka nan sumayya ma qin yarda take ganin cewa ba kwanakinta bane,bugu da qari kuma maman naana na tsumata,so take ta d'ai d'aita tunanin mukhtar din a duk lokacin da ya dawo hannunta.

Randa zai dawo dakinta tun safe take jin nishadi,ta shiga dakinsa ta masa gyaran tsaf lungu da sak'o ta k'alk'ale ko ina,sai data kammala duk wani abu da ya dace sannan ta zauna tana jiran zuwan yammaci.

Tana kan kujerar falon ta kwance bayan sallar azahar tana hutawa taji sallama qofar gida,saukowa tayi ta sanya hijabinta don ganin waye,don ta sani cewa ko digewa mai yin sallamar zaiyi ba amsawa ko saurarensa fa'iza zata yi ba.

Abdur rahman ne d'a ga qanin mahaifin mukhtar,gefansa qanwarsa ce bahijja wadda zatayi shekaru sha biyar,fuskarta qunshe da fara'a tayi masa iso kan ya shigo ta juya yabi bayanta,dai dai lokacin da fa'iza ke shimfida tabarmarta a tsakar gida da alamu zama zata yi,abinda bata taba ganin fa'izar tayi ba tsawon kwanaki takwas da zuwanta gidan,da kallo ta bisu suna gab da shigewa dakin sumayyan ta rabka salati
"Meye haka zaki kama ki shigo mana da gardi cikin gida?" Waiwayowa sukayi dukkaninsu suna dubanta
"Gyara maganarki qani yake ga mukhtar,muje bahijja" ta fada tana dage musu labulen suka shige.

Ruwa ta gabatar musu da lemo wanda ta tanada cikin cooler dinta saboda mukhtar,kasancewar ya musu yawa yasa suma suka samu rabonsu
"Mutanen misra,kaga ko yadda ka koma abdur rahman,yaushe ka dawo ne?" Sumayya ta tambaya tana murmushi,karatu ya tafiyi qasar misra saboda schoolership da ya samu daga gwamnatin tarayya,kasancewarsa haziqin dalibi cikin daliban dake jahar wanda ke karantar fannin da ya shafi addinin musulunci,shekararsa biyar da tafiya sai yau ya dawo,a lokacin da ya tafi din shekararta daya da aure da mukhtar,da gidansu jikin gidan mukhtar din yake kafin su tashi,wani lokaci idan mukhtar din nason fita kuma baiso ta fita abdur rahman din yake kira ya tayata zama,hakanne yasa suka saba har ya zama kamar wani abokin wasanta,a lokacin duka duka shekararsa sha bakwai shima.

Ruwan da yake sha ya ajjiye yana fadin
"Kwana na uku kenan,ashe yaya mukhtar bai gaya miki ba kenan?"kai take girgizawa
" bai gayamin ba kam ina ga ya sha'afa"
"Ya manta kam,irin wannan mace da ya ajjiye haka a gidansa babu kan gado" cewar bahijja don ita ta qulu da abinda ta musun,murmushi sumayyan kawai tayi,abdur rahman yace
"Itace matar da aka ce ya kuma aure?" Kai sumayya ta gyada masa sai yace
"Masha Allah,Allah to ya baku zaman lafiya,lokacin ina misra ai munyi waya da alhaji yake gayamin don alokacin anata rikici ya mukhtar ya kai qarar umma yahanasun" kai kawai ta kuma jinjinawa cikin mamaki din ita bata ma san ya kai qarar ba,hira suka sha sosai,suka tuttuna baya sai wajen qarfe uku suka yi mata sallama suka tafi bayan abdur rahman ya bata kyautar abaya har guda biyu masu kyau ta rakosu har soro tana musu godiya tare da bawa bahijja dari biyar tace ta hau mota.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now