Babi na saba'in

12.9K 1.2K 253
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL*
___________________________________

         Mamaki ya kama anty dije ganin sumayya,dariya ta dinga yi tana cewa
"Maganinki,da kika qi dawowa ga mai gaba daya nan taje ta taho mana da ke ai" itama sumayya dariya take
"Hmmm,amira,amira rigima amira tabara,sai ganinta kawai nayi wallahi"
"Ina sane ban gaya miki ba ai" guri sumayyan ta samu ta zauna tana ci gaba da dariya.

        Nan ta shantake suna ta hira da anty dijen,bata tashi farga ba sai taga har sha daya tayi,hakan ya sanya ta bude dakinta tayi kwanciyarta,anty dije je cewa
"Abdallah fa?"
"Barshi anty,babu lallai yayi rigima"

   ******     ******    *******

        Qarfe goma na safe tayi wanka bayan ta gama hada breakfast ta barwa anty dije sauran aikin gidan,doguwar riga ta saka ta wani irin yadi mai talewa,hijabi ta zura wanda ya saukar mata har saman tafin qafarta,niqabinta ta daura sannan ta fita ta tadda anty dije na goge kayan kallo a falo
"Anty zan wuce,nasan amira tana can ta cika fam,fashewa kawai take jira tayi" ta fada tana qyalqyalewa da dariya,dariyar itama tayi
"Ato,yau mai rabaku sai Allah" tana dariya ta saki niqab din nata ta fice a gidan.

       Ya kusan a qalla mintuna talatin zaune cikin corridor din dake saman benanshi,bata san sanda ya shigo ba,tun daren jiyan taje zaman jiran shigowarshi taji shiru,ta kira wayar babu adadi saidai duka amsa daya ce wayar a akashe take,tun tana kumbura har zuciyarta ta fara saukowa,ta sani cewa fushinsa bashi da dadi,tana shan wuya a duk lokacin da yayi fushi,hakan ya soma daga hankalinta,kusan ranar bata yi cikakken bacci ba,saidai duk da haka bata san shigowarshi cikin gidan ba.

        Cikin qanqanin lokaci zuciyarsa tayi fes,fuskarsa ta soma washewa,yaran dake shawagi kan idanunshi a harabar gidan,yaro daya tak yake hangowa cikinsu wanda bai sanshi ba baquwar fuska ne,saidai a yadda wasan da yaran ke gudana duka ya fisu kuzari da wayo,motsin yaron ya dinga bi da kallo yana sakin murmushin gefan baki.

          Sai data tsaya suka gaisa da baaba mai gadi kamar yadda suka saba sannan ta sanya kanta cikin gidan,tunda ta shiga gabanta ke wani irin faduwa,kusan yara sunfi yawa a harabar gidan suna wasanninsu,jifa jifa mutane na kai kawo,juyiwar da abdallah zaiyi ya hangota,duk da niqabin dake fuskarta da hijabinta hakan bai sanya ya kasa ganeta ba,da gudu ya tafi yana kiran
"Ammiiiii....amminaaaa" cak yaran suka tsaya suna kallonshi ganin suna tsaka da wasa ya bar gun.

       Da idanuwa yabi yaron ganin yayi wani guri da gudu,hannayenta ta bude baki daya duk da har yanzu niqabin na kan fuskarta amma murmushi ne kan fuskarta,durqusawa tayi ta daga shi tana nishi saboda nauyin da abdallahn ya dan yi mata sannan ta dage niqaf din,fararen jerarrun haqoranta a waje
"Wai abdallah,na kusa fara kasa dagaka,me kaci yau ka qara nauyi?" Dariya ya saki irin ta quruciya sannan yace
"Ammi,wata ummi ce,na kwana a dakinta,ta yimin wanka ta bani chips da qwai ni kadai na cinye,harda tea da suger sosai" dariya ta kamata,har sai data dora tafin hannunta kan bakinta,kafin tace wani abu hibba tayo gaba da gudu itama sauran yaran suka biyota,bata ankara ba taji an ruqunqumeta ana fadin
"Anty,kin dawo zaki mana labarin?" Waiwayowa tayi tana dariya,ta sauke abdallah tana fadin
"Kin manta yau ana bikin anty ameeraa?,sai idan an gama zan muku,muje ku rakani inda anty amiran take" gaba tayi yaran na binta a baya wannan ya riqe hannunta wannan ya riqe hijabinta a haka suka tafi.

        Baisan yana binsu da kallo ba sai da suka bacewa ganinsa,ya lumshe idanunsa sannan ya bude a hankali,abun ya burgeshi ya bashi sha'awa,yana son yara har cikin zuciyarsa,bayansa ya jinginar jikin kujerar yana fidda zazzafan huci daga bakinsa
"My man" yaji an ambata a tausashe,yasan ko wace hakan ya sanya yaqi waiwayawa,sannu a hankali ta tako gabanshi,sanye take cikin riga da wando,ire iren shigar da tasan yana muradi suna burgeshi qwarai idan tayi,jikinta na fidda wani irin qamshi mai dadi,duka hannayenta ta zuba a kafadarsa,cikin shagwaba salon da tasan yafiso tace
"My man,ka sanyani a damuwa jiya,kasan cewa ina buqatar ka,baki daya kwanakin da zamu kasance tare ba masu yawa bane,amma man ka qauracemin" ko kadan bai da buqatar maganarta,hakan ya sanya ya saka hannunshi ya sauke hannayenta dake kafadarsa sannan ya ture kujerar ya miqe tsaye ta juya yana shirin barin gun,ranta ne ya baci,hankalinta ya tashi,ta tabbatar cewa ya hau bigerin da shawo kansa zaiyi wuya,bata kuma isa ta sha gabanshi don hakan zai iya jawo mata wata matsalar,tilas ta janye jiki tana kallonshi ya wuceta,hannayenta ta saki zuciyarta na zafi,idanuwanta na neman tara qwalla,babu shakka idan banda mustapha mustapha ne da babu namijin da zata zauna a duniya yayi mata haka,saidai mustaphan na dabanne kamar yadda yake daban a zuciyarta,mafita daya gareta ta kaishu gaba inda za'a sashi tilas yayi mata abinda take so din,bama inda ta saba kaishi ba wannan karon na can zata kaishi ba,sai ta juya da dan sassarfa ta ratsa ta dakinsa zuwa falonsa ta sauko qasa ta nemi hanyar ficewa ba tare data damu da sauya kaya ko daukar babban mayani ta suturta jikinta ba ko don girman wanda zata gurinsa.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now