Babi na arba'in da biyu

8.1K 905 107
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wala tahsabannal lazina qutilu fi sabilillahi amwaataa,bal ahya'u inda rabbihim yurzaqun*

*_kada ku zaci wadanda aka kashe ta hanyar Allah(shahidai)matattu ne,rayayyu ne a gun ubangijinsu ana azurtasu_*
_______________________________

       Mukhtar dake falo zaune saman abun sallah yayi saurin sallame raka'arsa ta qarshe wadda dama zaman tahiya yake,qarasowa abdallah yayi yana kebe baki ya fada jikin mukhtar,tambayarsa yake menene kamar wani babba,babu baki sai gwalanto da yake masa wanda bai gane mai yake cewa,miqewa yayi da sauri sabe da shi a kafadarsa sabida tunawar da yayi dazu da ya fita siyo ma abdallan alawa ya manta ya bar qofar gidan a bude.

        Tana zaune qafa daya kan daya tana kadasu hankalinta kwance,tana jin ba ma sai taje nemansa ba da kanshi zai fito,qamshin turarensa da ta ji shi ya maida hankalinta zuwa qofarsa,shi dinne dauke da abdallah sanye da jallabiya sak irin ta abdallan,har ga Allah bai lura da ita ba sai da yaji an ambaci
"Ranka ya dade" cak ya tsaya sannan ya waiwayo ya dubeta,idanunta ya dan juya don tabbatar da cewar ita din ce?,ita ce don kuwa zuwa yanzu gabansa take takowa,dab da shi ta qaraso tamkar zata shige jikinsa,cikin narke murya ta soma magana
"Haba my mukhtar,ka riga da kasan irin kamun da soyayyarka tawa zuciyata,ta yaya kake tunanin nisanta kanka da ni bayan kasan cewa ina mutuwar sonka,a yau ina so ka maidani dakina ba sai gobe ba domin shine burina kaji" ta qarashe maganar ta sigar bada umarni.

       Wani bala'i ke cinsa,ya tabbata cewa idan har baiwa zainab akuyanci ba ba zata taba barin rayuwarsa ba,yarinyar da kullum kwanan duniya ya zauna tunani yake tare da tambayar yaya akayi ya aureta ma wai?,mene ya ja hankalinsa,ko da yaushe yakan godewa Allah da bai QADDARA rabon zuria a tsakaninsu ba.

        Cikin tsantsar bacin rai ya soma nuna ta da yatsa kamar zai tsone mata idanuwa
"Cikin halittun dabbobi ke wacce iriya ce a cikinsu?,bakiji gargadin da na miki ba kenan?,tunda nake ban taba ganin ballagazar mace irinki ba,sha sha sha kawai wawiya,to wallahi zan miki gargadi na qarshe,duk sanda kika sake shiga rayuwata sai na miki abinda ko hanyar da nake bi aka ce kibi ba zaki biba,bace min da gani banza qazama kawai" ya fada kamar zai hankadata.

       Tsantsar tashin hankali da baqinciki suka taso suka tokareta,amma data tuna yadda bokanta ya jaddada mata kyawun aikin da yayi mata sai taga bari ta sake gwada sa'arta
"Wai mukhtar me na maka da zafi haka,nina shiryawa sumayya dukkan wata gadar zare kuma a idanunka sumayya ce ta aikata laifin,to amma na lura tsanar da ka yimin baka yi mata koda rabinta ba" sosai maganar ta daki kunnensa gangar jiki da zuciyarsa duka lokaci daya,wani abu yaji yana zagaya kansa,wani irin sanyi jikinsa yayi ya zubawa zainab ido har baisan sanda yace
"Kika shirya mata gadar zare kamar yaya?" Wani fari tayi da idanuwa tana ci gaba da kallonsa,a tunaninta sanyin da jikinsa yayi aikinsu ya fara shiga jikinsa ne,sai ta kama hannunsa babu musu ya bita zungui zungui,don baya gane komai a yanzu,abinda ke yawo kansa kawai shine irin abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninsa da sumayya a lokacin,sai da ta kaishi gefan kujera ta zaunar sannan ta zauna gefansa.

       A hankali ta dinga warware masa zare da abawa tamkar wadda ake umarta,ko da yake umarni ne na rabbil izzati da yaso ya fidda bayinsa daga wani mummunan sharri,ta qare da cewa
"Dukkan wannan saboda tsananin qaunarka da kishinka da nakeyi ne ya janyo na aikata hakan,kuma babu abinda bazan iya aikatawa duk don saboda kai saboda na mallakeka ni kadai,a shirye nake na sadaukar da dukkan abinda na mallaka" ta fadi tana karya wuya tare da sakin murmushin alamun samun nasara a tunaninta.

      Gaba daya daina zagayawa jini yayi a jikinsa,kansa ya masa nauyi,cak qwaqwalwarsa ta tsaya da aiki,wani duba yakewa zainab din mai cike da tsantsar tsana,daki daki musgunawa da zargi da kallon tsana da ya dinga yiwa sumayya ya dinga dawo masa kamar bitar karatu,yanzu duk baki daya ba bisa laifinta bane ashe?,ashe ita din bata aikata komai ba kamar yadda tasha sanar masa?,bai taba jin ya tsani wata halitta a duniya ba kamar yadda yake jin tsanar zainab na yawo cikin jininsa da ruhinsa ba,sai da wuta ta dauke masa na wasu mintuna kafin ya fara tunaninsa ya fara dawowa kan hanya.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now