Babi na shida

11K 782 34
                                    

*rabbana afrig alaina sabran watawaffana muslimin*

       Idonta ta runtse tana jin qarar rufe maga qofar da yayi,ta gefe daya ta kwanta ta sake mirginawa daya gefan,gaba daya take jin gadon yayi mata fadi.

        Ganin tana neman cinhe daren idanu biyu ya sanyata runtse idonta,ta damqe filon da take kai tana fadin
"Ya rabb,afrig li sabra" tayi ta maimaitawa babu qaqqautawa,Allah maji roqon bawansa,bata san lokacin da wani bacci ya sadado ya sace ta ba.

        Qarfe shida ta farka firgigit tana ambaton sunan Allah,tayi mamakin yadda tayi bacci mai nauyi irin haka,cikin mutuwar jiki ta sauko daga kan gadon ta fito.

         A hankali ta murda qofar dakin nata kana ta tura ta ta bude,tashin farko idanunta suka sauka kan qofar dakin fa'iza amarya,qofar dakin na kulle gam da alamu ba'a bude ta ba tunda aka rufe,sai taji wani qunci na ziyartar zuciyarta,ta kau da kai tana jan tsaki kana ta wuce bakin fanfo,ta taro ruwa ta shige bandaki ta kama ruwa sannan ta fito ta daura alwala.

      Har qarfe takwas na safiya tana saman abun sallar,ta kalli agogo sannan ta janyo rediyonta data kunna wadda ita ta tayata zama ta kashe,ta miqe ta zare hijabin jikinta ta ajjiye ta fito zuwa tsakar gidan,ta saba tun tuni da kammala ayyukanta da wuri saboda ya mukhtar bai wuce goma a gida.

         Idanunta suka sake sauka kan qofar dakin karo na biyu,sabanin dazu yanzu an sassauta rufin qofar da alama an budeta ne,sake dauke kanta tayi sannan ta shiga ayyukanta kamar yadda ta saba.

          Sai da ta tsabtace ko ina har zuwa dakinta sannan ta shiga tayi wanka,tsab ta shirya cikim daya daga cikin ragowar sabbin dinkunanta,atamfa ce dinkin riga da skert da ta fidda shape din qugunta yayi das,bata sake yarda da kyawun dinkin ba sai da taga yadda yayi mata a jikinta,maman nana ce ta zabar mata shi.

          Tsakar gidan ta dawo,kitchen ta shiga,sai yanzu taga jeran da aka ma fa'iza,za'a iya cewa ta fita duk wani kayan aiki na kitchen nesa ba kusa ba,bangaren ta ta nufa ta wanke tukunya ta tara ruwa ta dora ruwan tea wanda ya sha hadin kayan qamshi sannan ta koma gefe ta fara fere dankalin turawa,babu abinda mukhtar din bai siya ba na kayan abinci tun shekaran jiya.

       Aikin take amma zuciyarta a cunkushe take,fuskarta kawau zaka kalla ta gaya maka hakan koda bata bude baki ta fada ba,ta gama firar ta wanke sannan ta juye shayin cikin wani sabon tea flask wanda yake seat ne da farantansa da kofuna.

         Tana cikin suyar dankalin ta dinga juyo motsi a tsakar gidan,bata fasa abinda take ba kamar yadda bata damu tasan waye cikin su biyun ba,aikinta taci gaba da yi har lokacin da taji hancinta ya cika da qamshin turaren mukhtar,kamar ta waiwaya sai ta fasa,wani haushinsa ta dinga ji tana ji hakanan.

     "Sannu da aiki uwar gida na" taji ya ambata yana takowa zuwa cikin kitchen din,ta dan waiwayo hannunta riqe da abun tsame dankalin yana tsaye a bayanta gab da ita,maimakon ta tarad da annuri da qyalli irin na ango sai ta tarad da sabanin hakan,fuskarsa tana nan kamar kullum
"Ina kwana" ta fada a taqaice fuskarta a daure ba tare da ta damu da yanayin fuskarsa ba,maimakon ya amsa sai taji ya sanya hannu ya karbe abun tsamewar ya matsa gefanta ya shiga kwashe dankalin wanda shi yayi saura cikin man
"Sumy,me yake faruwa?" Ya tambayeta yayin da take jingine da kantocin fa'iza hannunta harde a qirjinta
"Kamar me?" Ta tambayeshi tana debo qwan da zata soya tana zubawa cikin kwano,ya bata amsa sanda yake qwace bowl din ya fara fasa qwayayen
"Babu fara'ar nan a fuskarki yau ko kadan" shiru tayi masa bata da niyyar fankawa,ganin haka yasa shima ya ja bakinsa ya tsuke har ya kammala suyar.

       Nata kayan karin ta diba ta kammale musu nasu a kitchen ta wuce dakinta,tana zaune kan kujera tana kallon mbc yayin da take zarar dankalin da dai dai da dai dai tana ci tamkar bata so mukhtar ya shigo dakin,yayi kyau cikin dinkin shadda ruwan qasa mai turuwa sai qamshi ke tashi
"A'aha,ya kike karyawa ke kadai ina namu break din"
"Yana kitchen" ta fadi tana ajjiye plate din hannunta,kai ya girgiza yana zama gefanta
"Ba haka na tsara ba,ki shirya mana a nan falon naki,gaba daya zamu karya,daga nan ki shiga ki kira fa'izan" bata ce komai ba ta miqe ta fita din ta dinga kwaso kayan tana jerawa har ta kammala.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now