Babi na tamanin da daya

17K 1.4K 501
                                    

  *Bismillahir rahmanir rahim*

*ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis,aslih li sha'any kullahu,wala takilni ila nafsy darfata aynin*
___________________________________

       Qarfe takwas na safe ta farka bayan baccin data koma bayan ta kammala sallar asuba,babu kowa a dakin sai ita daya,alamu sun nuna ma ya fita,gefe daya ta tarar da kayan break fast,komai da komai irin wanda zata iya ci,toilet ta shiga tayi wanka ta dawo ta gyara dakin sannan ta sanya kayan taja kayan ta karya,kwanciya ta sake yi bayan ta gama,ba dadewa wani baccin yayi awon gaba da ita,bata farka ba sai data ji ana knocking qofar,ta miqe ta isa ga qofar,ga mamakinta a bude take muqullin ma na jiki yau bai rufe ba kenan.

       Matashiya ce sanye da kayan ma'aikatan hotel din,cikin murmushi ta dubi sumayya ta gaidata da harshen larabci cikin kokwanto,don bata da tabbacin zata ji,murmushi ta saki tana mamakin jin larabci mai kyau a bakin matar,tasan yawanci larabcinsu ba irin wanda ake mana amakarantu bane ta maida mata,sai ta sake fadada murmushinta ganin cewa tana jin yaren,ta miqa mata wani abu a nade da wata leda mai qyalli tana shaida mata abincin ranarta ne,sannan ta nuna mata tarin lemuka da ruwa tace idan ba damuwa zata sanya mata a fridge,matsa mata tayi tana fadin
"La ba'as,tafaddal" ta koma ciki ta biyota,tana tsaye ta gama shirya komai sannan ta maida qofar ta rufe bayan tayi mata godiya,sai data fara sallar azahar sannan ta bude,gasashshiyar kaza ce da soyayyar taliya sai hadin coleslow,ba wani da gawa taci ba ta rufe kasancewar bata jin yunwa.

        Kusan haka ta wuni ba cas ba as,har kwanciyar ma ta isheta,ita ba sanin kan hotel din tayi ba ballantana ta fita,sai daga bisani ne ma ta koma bakin window din dakin tayi zamanta kasancewar tana ganin mutanen dake kai komo ta nan.

         Kusan haka zaman nasu ya kasance har kusan kwanaki goma,da safe zata tadda ya fita amma ga breakfast dinta,da rana wannan matar zata kawo mata lunch,da yammaci ta dawo ta tambayeta koda wani abun,sai kuma na dare zata sake kawo mata shima,sau tari kafin ya dawi tayi bacci,sai haduwa tayi wuya a tsakaninsu idan ba da asubahi ba,sai data ta farka taga an fidda abincin da bata cinye ba a ajjiye mata wani,abinda ta fuskanta shine shi din mutum ne wanda bai san dadin jikinsa ba,mutum ne da ya baiwa sana'a da business muhimmanci mai tsoka cikin rayuwarsa,bashi da wani lokaci sai na kasuwancinsa,bugu da qari kuma ta lura da yadda matsalan kamfanin ta sanyashi a gaba,sam ba haka rayuwarsa ya kamata ta kasance ba,ya qare qarfinsa wajen kasuwanci ba kawai,tana ganin hakan bai dace ba,ita kanta ta soma qosawa da zaman garin,don baki daya bata ga wani amfani da zamanta ke da shi ba,tunda bata ganin wanda take zaunen saboda shi,saidai kullum taci ta sha ta kwanta,hakanne ya sanya yau ta qudurce ba zata yi bacci ba har sai ya dawo,tanas son tayi waya da 'yan gida,mama,malam abdallanta,zainab da halima baki daya,ga anty dije,layinta tunda suka shigo qasar ya daina amfani,kuma batasan inda zata samu wani layin ba bare fa nemesu.

     Tana idar da sallar magariba ta shiga tayi wanka,zama tayi bakin mudubi bayan ta fito ta mutstsike jikinta da turaren humra bayan ta shafa mai,ta goge fuskarta da powder sannan ta wadata lebbanta da man lebe mai taushi da qyalli,kwalli ta zizarawa fararen idanuwanta wanda hakan ya sake fito da kyawunsu sannan ta gyara jagirarta,kai tsaye ta wuce gun kayanta ta fito da atamfarta,holland ce dark brown ne jikinta,yayin da aka yi maya ado na mint green da yarfi yarfin fari,riga ce da zani simple,saidai rigar tayi maya cas a jikinta,daurin ture kaga tsiya tayi saidai baiyo gaba sosai ba,wanda yake fitar da kyan fuskarta da tulin gashinta dake daure,takalmi ta sanya plate fari qal,sabone shima kamar yadda kayan jikinta suke sabbi,wani masifar kyau tayi,kallo daya zaka yi mata ya tabbatar maka cikakkiyar BAHAUSHIYA CE,a qalla tasan zata iya kashe awa biyu kafin ya shigo,hakan ya sanya ta yanke shawarar fita waje ko hakan zai ribaci idanunta har ya dawo.

       Karo na farko data fara fitowa tunda suka shiga dakin,doguwar corridor ce a qawatacciya mai kama da falo wadda ke dauke da dakuna ajere reras cikin tsafta qamshi da tsari,kamar zaka zuba abinci a qasa kaci,a hankali ta dinga takawa,har ta fice daga corridor din bata ga kowa ba,ta karya kwana ta fita wata varender wadda aka tanadeta saboda hutawa,an tsarata da kujeru da 'yan shukoki cikin qananun tukwane masu kyau,daga nan kaya iya ganin harabar hotel din sarai da dukkan abinda ke kai da kawowa,ta nan zaka iya sauka zuwa qasa ko kuma kaa wuce zuwa ciki,hakan yayi maga,sai ta jita sakayau,ta tsaye dafe da makarin varender wanda yake na silver ne tana kallon komai daidai fuskarta a washe tana more iskar gun da kalle kallen da takeyi.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now