Babi na hamsin da hudu

9.7K 880 60
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Rabbukum a'alamu bima fi nufusikum*

*(haqiqa)ubangijinku shine mafi sani ga abinda yake cikin zukutanku*
_________________________________

       A rude anty dije ta soma tambayarta
"Lafiya sumayya?,me yake faruwa?,ko wani ne ya mutu?" Ta jero mata tambayoyin baki daya,jin tayi shiru bata tanka ba ya sanyata itama shirun tana sauraren kukanta,ta tabbatar wata matsalarce ta taso mata haka jikinta ya bata,tausayin yarinyar take ji,sai yaushe ne zata fita daga matsala,sai data dauki a qalla minti goma sannan ta soma magana cikin karayar zuciya
"Anty,lukman da abdur rahman"
"Me ya samesu?"
"Anty......dukkaninsu sun dawo,kowanne so yake na aureshi,fisabilillahi anty ni bazan huta ba?,duka duka yaushe na soma samun nutsuwa?,anty bana buqatar sake wani auren yanzu,tsoro nake ji kada su nufi malam da maganar,idan malam ya umarceni anty bazan iya bijire masa ba" sai ta fashe da kuka,tsaki anty dijen tayi sannan tace
"Zancan banza,kema kin riga da kinsan cewa malam yasan haqqinki na hannunki yanzu,ke zaki zabawa kanki miji ko?,sannan tsakanin lukman da abdur rahman akwai wanda ya isa ya aureki ne bada amincewarki ba da zaki tadawa kanki hankali ki dinga zubda hawayenki?,duk wanda kika zubar a baya bai isheki bane sumayya?,ko so kike wani ciwon ya sokeki?,to nikam na gaji da ji da gani,kishirya da gaske idan nazi tare zamu koma,idan yaso naga wanda zai qara bata ranki" ta fada tana katse wayar.

       Shiru tayi tana juya wayar a hannunta,ba haka taso anty dije tace ba shawarar yadda zata kubuce daga tsakanin da lukman da abdurrahman suka sanyata take so ta bata,amma da tayi tsai sai ta lura lallai babu hanyar da zata zille musun idan ba barin garin kanon zata yi ba kamar yadda anty dije tace,sai ta sauke ajiyat zuciya tana goge hawayenta,tana qiyasta idan ta bar kano koda na tsawon wata daya ne itama ta samu hutu,ta samu ta manta da wasu lamuran ta manta da damuwoyinta.

  *******  *******   *******

  Washegari ta shirya don zuwa gidan yaya yahanasu ta dauko abdallah tunda duka duka saura kwana biyu anty dije tazo,tana tsaye a falon mama tana sanya hijabinta tare da yiwa mama sallama suka ji sallamar abdur rahman,kamar ta juya ta shige daki amma tasan idan tayi hakan kamar ta nunawa mama akwai wani lamari tsakaninsu irin wanda ya faru a baya,abinda bata da buri ko fatan kowa ya fahimta kenan
"Ina yini" sumayyan ta gaisheshi tana shirin ficewa bayan sun gaisa da mama
"Lafiya......ina zuwa haka?" Ya tambayeta yana dan dubanta,cikin hanzari ta soma sanya takalmanta tana bashi amsa
"Zan dauko abdallah he gidan ya yahanasu"
"Yauwa,nafi jin dadin tafiya,dama jiya da naje na yiwa abdallah alqawarin yoghourt" ya fada yana miqewa tsaye,kamar ta zura da gudu haka taji,take yanayin fuskarta ya sauya wanda tashin farko ya fahimci bata ji dadin shishshigin da ya mata ba,saidai sam bashi da damuwa matuqar zai kasance da ita,inda zata iya zata ce masa bata so amma idanuwan mama ya sanya ta kasa cewa komai
"Sai mun dawo mama"
"Allah ya kiyaye hanya ku gaida min yahanasun"maman ta fada ba don son ranta ba,don ba kasafai take barinsu suna shiga motocin gida ba koda na 'yan uwa ne,tafi ganewa su hau ta haya
"Zataji" inji zainab wadda ita ce 'yar rakiyar.

      Gaban motar ya bude mata da kansa,sai da yaga ta shiga ta zauna sannan ya zagaya nashi mazaunin ya tashi motar suka tafu,shiru ya ratsa motar,babu mai magana tsakaninsu,sai ya sanya hannunshi ya dannan plate jikin redion motar,cikin sakanni lacture malamin dake cikin fefan ta fara tashi,ya daj qaro volume din sannan ya dauke hannayensa ya maida kan sitiyarin motar
"Nikam bansan wanne irin baqin jini ne da ni ba" ya fada qasa qasa yadda ita da shi ne kawai zasu iya jin me yake fadi,ta gefen ido ta kalleshi don ta tabbatar da ita yake ko kuwa,sai ta gane da ita din yake saboda yadda yake kallonta kadan kadan,shiru tayi bata da niyyar tankawa saboda bata fuskanci ma inda zaurancen nasa ya sa gaba ba
"Sumayya me nayi da jiya baki sona,yau ma kinqi karbata,ko na aikata miki wani laifi ne?,ko ina da wani aibu da ban cancanci a soni ba?" Ya tambayeta yana mai muradin jin amsarta
"Baka aikata komai ba,amma don son annabi mubar maganar nan,kada ka manta har yau jinyar zuciyata nake bata warke ba,ban kuma san ranar warkewarta ba" ta fadi tana duban gabanta ba tare da ta dubeshi ba.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now