Babi na hamsin da bakwai

10K 865 72
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wallahi tallahi billahil azim duk wanda baibi Allah ba ya shiga uku,duk wanda baiji tsoron Allah ba ya kade,duk wanda tsoron Allah bai hanashi bin son zuciyarsa ba yana cikin babbar musiba,dan adam ba kowa bane hakanan ba komai bane shi,kaji tsoron ubangijinka kayi biyayya a gareshi KAJI TSORON AZABARSA KAYI KWADAYIN RAHAMARSA sai ka samu rabauta,ka guji duk wani abu mara kyau,kayi riqo da kyawawan ayyuka, 'YAR UWA,KI KARANTA YADDA UBANGIJI DA MA'AIKI SUKA WASSAFA MANA JAHANNAMA,ALLAH KAYI MANA TSARI DA ITA BADON HALAYENMU BA,KADA KA NUNA MANA ITA KO NA QIFTAWAR IDO NE,KA BAMU IKON YIN BIYAYYA A GAREKA,KA KADE MANA ZUKATANMU DAGA TUNANI KO AIKATA DUK WANI SABO KO ZALUNCI*

______________________________________

       Kwanaki nata tafiya,tun tana a takure da zaman garin har tazo ta fara sakin jiki,abu daya ke damunta kewar abdallah,tausayinsa take hakanam tausayinsa ya ninku a zuciyarta tun daga randa ya rasa mahaifinsa,kullum takan kira a bata shi su gaisa susha hirarsu,abinda ya sake kwantar mata da hankali a nan ba inda take zuwa bare ta gamu da wani yace mata yana sonta,hakanan kiran waya ma da ake ana nemanta tun ranar da anty dije tayi magana aka samu sauqim kiran,sai jifa jifa shi din ma ba dagawa take ba,abdur rahman ne kadai ke kiranta su sha hirarsu har ta riga da ta saba,babu wata rana da zata fito ta fadi bai kirata ba,ta sake sosai don bai qara yi mata wata magana daban ba banda ta zumunci,anty dije tayi ta mata tsiyar batasan muguwar kifin rijiya bace ita sai yanzu,bata son zuwa ko ina,ko gidan baabaa prof shigarta biyu kwata kwata shima da dalili na farkon kiran laila da taje,na biyu kuma da sumayyan tayi dambu gidan ba yara ta sata ta kaiwa anty maamaa da yake ita mai son dambu ce,kota shiga din ma bata wuce minti biyar ko goma ta fito,hakan ya sanya anty dije ta bada sautun kayan turare da humra aka kawowa sumayyan ta soma yi a nan,cikin designers kwalabe take zubawa,nan take kuwa ta soma ciniki,duk da wani gu ake kaiwa,'yan unguwar ne kawai ki zuwa siya cikin gida.

      Yau ma kamar kullum babu yara a gidan suna makaranta,gab suke da fara jarabawa ayi musu hutu saboda gabatowar wata mai alfarma na azumin watan ramadan,suna zaune da anty dije a kitchen tana anty dijen ke girki yau sumayya na ganin yadda take yi din don bata iya irinsa ba,iya zamanta da anty dijen ta qaru da abubuwa da dama ta fannin zamantakewar gida,girki iri iri,gyaran jiki da kuma uwa uba iya gayu,wayarta anty dijen ta daga wadda ta fara ruri ta kara a kunne,ganin haka sumayya ta karbi yankan cabbage din da takeyi taci gaba,sai data gama sannan ta dubi sumayyan
"Sumayya,inaga fa ke zaki miqawa anty maamaa humrar nan,kaya take hadawa kuma kinga yaran basu dawo ba" kasaqe tayi,sarai anty dijen ta gane bata son zuwa ne,bata san me yasa bata qaunar shiga gidan ba amma sai ta shareta,ta gane mai anty dijen ke nufi tilas ta miqe tace to,dakinta ta shiga ta sanya dogon hijabinta har qasa sannan ta jawo ledar data jera humrorin wadda anty maamaa ta bata tayi mata,saboda umrar azumi da zasu tafi ita da maigidan da kuma ummee,sai babban yaron gidan shi da matansa biyu sai qaninsa da tashi matar,sai manyan jikokin gidan su biyar duk da basu wuce shekara sha hudu zuwa qasa ba,duk laila aku(sunan da idan taso take kiranta da shi kenan kusamman idan tayi hali ) ke bata wannan labarin tunda ita ba shiga take ba ballantana ta sani.

       Kamar kullum a hankali ta dinga ratsa gidan bayan sun gaisa da mai gadin dake gadin wannan qofar sa suke shigowa da yake akwai wata qofar ta baya,mutumin ya haifeta shi yasa take ganin girmansa,mutum me mai faran faran da son jama'a,duk da ganinsa da sumayyan baifi uku ba amma yana yabawa hankalinta yadda take rusunawa ta gaidashi,duk da yasan iyalan gidan alhj umar farouq ba baya bane wajen tarbiyya.

      Kanta a qasa qirjinta na bugawa ta dinga kutsawa cikin gidan,batasan me yasa take yawan faduwar gaba ba idan ta shigo gidan,ko don tana ganin kamar akwai banbancin matsayi tsakaninsu bai kamaci ta dinga shiga musu gida ba.

     Tazo mararrabar sashin anty maamaa data ummee sai taso ta manta wane waje ne na anty maaman don bata rarrabewa da sunayensu,a hankali ta juya idanuwanta tana canki canki,karaf idanuwanta suka sauka a kansu,zaratan samari ne ke tsaye su biyu suna magana da junansu,dukkaninsu dogaye ne saidai daya yafi daya masu matsakaicin jiki,kowannensu na sanye da t.shirt da trouser masu mabanbantan kaloli kowa da kalar nasa,farare tas da su kamar yadda ta dan fahimci haka kalar fatar masu gidan take,fuskar daya kawai taje gani bata ganin ta dayan kasancewar ya juya baya ne yana magana da dayan,da alamu kuma duk hankalinsa na kanshi,shima ya ganta,idanu ya sanya yana kallonta har waccan ya kammala fadin abinda zaice yayi gaba ya shige daya sashen.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now