Babi na dari da hudu

16.3K 1.2K 134
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin*
_____________________________________


       Har ta qarasa wajen basu lura ba,sai data tsaya dab da su sannan hankalinsu gaba daya ya dawo kanta,idanu kowa ya zuba mata yana mata kallon qurilla
"Fa'iza?" Sumayyan ta fadi tana dubanta,jin tayi shiru bata amsa ba ya sanyata sake cewa
"Ko ba fa'iza bace?"
"Nice,nice mana" ta fada tana yanqare haqora tare da cire yaronta daga bakin nonon,farinciki fal ranta yau cikinsu su wajen goma 'yar gayu ta mata magana ita kadai har tana nuna ta santa,har ga Allah sam bata gane sumayya ba
"Fa'iza kece haka?" Sumayya ta fada cikin mamaki da al'ajabi
"Eh wallahi...amma na kasa heda fuskar taki"
"Sumayya ce fa....sumayya kishiyarki wadda kuka taba auren mukhtar tare" miqewa fa'izan tayi dafe da qirji tana cewa
"Keeee.....sumayya?,da gaske?" Ta fada tana matsowa kusa da ita ta soma shafa kayan jikinta tana qare mata kallo,sai kuma ta fashe da kuka tana cewa
"Kina nan dama sumayya?,naji labari ashe mukhtar ya rasu?" Cikin raunin zuciya ta gyada
"Mukhtar ya rasu fa'izw,shekara kusan shida kenan"
"Wayyo Allah,dama mukhtar na raye na roqeshi gafarar cusguna muku da nayi" gefe fa'izan ta janye sumayya,kan wasu duwatsu guda biyu dake wajen suka zauna,nan take sanar mata labarinta,bayan fitowarta gidan mukhtar kamar wadda aka yiwa baki ba wanda ya taba zuwa taya aurenta,ko dama can bata da farinjinin samari ko kadan,hakanne ma ya sanya aka hada ta da mukhtar din,sai daga bisani baban yaron dake cinyarta ya fito neman aurenta,wanda yanzu yaransu uku,wannan ne qarami,bayan auren ba komai ta tsinta ciki ba sai wahala,matanshi hudu kowacce ita ke dauke da dawainiyar kanta data yaranta,zai zube musu hatsi ne kawai a rumbu saura kuma ya rage nasu,sosai taji ta tausayawa fa'izan,wato rayuwa kowa da irin jarrabarsa,hakan duk abinda ka shuka dole wataran saika girba,ko ka jawa yaranka gadon wahala su su girbe abinda kaine ka shuka shi,gashi dai taqi uarda ta zauna gidan mukhtar dake cikin birni,yana da matarshi daya da rufin asirinsa qwarai,babu abinda bai dauke musu ba na dawainiyar gida,sai gashi ta fada gidan mai mata uku,banda hatsi bai kula da komai naku ba,ga haihuwa tanayi
"Ya taki rayuwar sumayya?,da alama komai ya miki kyau" ta fada tana qare mata kallp,tun daga takalmin qafarta zuwa lafiyayyen material dake jikinta,dankunne agogo sarqa da jaka,murmushi kawai ta saki sannan tace
"Kowanne bawa da kalar tashi qaddarar,kuma ba shakka duk inda kayi sai ta bika,saidai Allah yakan yiwa bawa sakayya gwargwadon abinda ya shuka,idan alkhairi ne bayan Allah ya gama jarrabaka sai ya maka sakamako mai kyau,haka idan sharri ne ma" a taqaice ta bata labarin komai,ta dinga jinjina kai tana sake nutsuwa tare da dana sani kan abinda ta aikata a baya,nan ta nemi gafarar sumayya,bata da riqo sam ballantana ma ita bata ga abin da za'a riqe fa'iza da shi ba,don baki dayarta abar tausayi ce,yafe mata tai sannan ta bita da alkhairi,ta tambayeta nawa take buqata na jari,wanda zata bar wannan aikin taje ta riqe iyalanta
"Dubu uku ma ni ta isarmin" ta fafa cikin zumudi,baki dayanta kalar tausayi ce,jakarta ta bude,ta zaro dubu goma 'yan dari biyar biyar sababbi ta miqawa fa'izan,ai batasan sadda ta dire danta dake kan cinya ba hannu na rawa
"Don Allah kada kice min da wasa kike" ta fada bayan ta gama qirga kudin,murmushi sumayya tayi tausayinta na kamata
"Ba wasa nake miki ba fa'iza,ki riqe kija jari,don Allah ki baiwa yaranki tarbiyya da kuma ilimi,shine kadai gatan da zaki musu"
"Da izinin Allah sumayya na gode na gode na gode" sai ta fashe da kuka tana sake jaddada godiyarta.

       Daya daga cikin matan ne ta iso wajen tana sanar da fa'iza ta taso za'a biya su kudin aikinsu na yau,sannan mai gonar zai basu wani abu,daa tace ba sai taje ba,sumayya tace haqqinta ne taje ta karba ta hada,baki dayansu suna tattare waje daya,tare suka isa wajen,almustapha na tsaye jikin motarshi,tun dazu yake raba ido yaga ta ina zata bullo,gefan matan itama ta tsaya cikin tausayi take dubansu,tana godeww Allah matuqa kan ni'imar da yayi mata,ba tare da wayo ko qarfinta ba,da idanu ya dinga binta,tausayin da ya gani zallah cikin idanunta ya sake burgeshi,ko da yaushe dabi'arta tasha banban data saura daya saba gani masu shekaru irin nata,take yayi wani quduri cikin ranshi,ba shakka zata dace da a bude mata wata qungiya ta tallafawa mata marasa galihu da koyon sana'o'i,da alheri almustaphan yabi kowaccensu,dukkansu ko sai da suka dara saboda kudin da ya basu,shi kanshi tausayi suke bashi,ina mazansu da haqqin ciyarwa da shayarwa ke kansu suka barsu suna wahala da fadin tashin ci da kansu,sai da suka gama kaf sannan sukayi sallama fa'iza na sake jadda da mata godiya,ta karbi lambar sumayyan tace ko cikin gari zata dinga shiga tana kiranta suna gaisawa lokaci zuwa lokaci.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now