Babi na saba'in da bakwai

14.6K 1.3K 187
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

___________________________________

      Bayan sun shiga cikin jirgi bata sake ganinshi ba,batasan inda ya zauna ba sai da suka sauka,cikin motocin gidan aka zo daukarsu,tana tsaye har ya shiga sannan itama ta bude ta shiga,yana zaune daga daya bangaren itama haka,motar tsit,shi yana danne dannen wayarshi yayin da ita kuma ta bige da kallon titi tamkar yau ta soma ganin garin a haka har suka qarasa.

       A hankali motar ke kutsawa cikin unguwar tasu,tana kallo suka wuce qofar gidan anty dije,kamar tayi tsalle ta fita haka take ji,saidai ba yadda zata yi,yanzun a qarqashin wani take dole,ajiyar zuciya ta saki tana sauke jumfashi,a yau a kuma wannan lokacin gata ta sake dawowa cikin gafin,saidai cikin wanu matsayi na daban,ta dawo cikin garin a matsayin matar wani kuma surukar gidan baabaa professor,ma'ajiyar motoci motar ta tsaya bayan mai gadin ya bude masu wakekiyar qofar gidan,a hankali ta sanya hannunta ta bude murfin motar bayan tsayawar motar,qafarta ta zura guda daya waje ihun amira ya karade kunnuwanta,kafin tace wanu abu tuni ta ruqunqumeta
"Wayyo amaryarmu oyoyo oyoyo" murmushi ya subucewa sumayya,da ido takewa amiran nuni da bayanta,sam bata ankara ba karadinta kawai take
"Ke matar nan kiji tsoron Allah,har an fara sanin dadin miji ko?,anty ta bani labari daga zuwa ganin doctor sai kawai ayi mai gaba daya,kodai......" Bata kai ga qarasawa ba ya fito daga cikin motar,wanda hakan ya tilasta mata sanyawa bakinta fulasta sabida kallon da ya jefeta da shi,magana ce fal cikinta amma tilas ta saita kanta,a ladabce tace
"Barka da isowa yaya"
"Sake mata hannu ko?" Ya fadi ba tare da ya damu da amsa gaisuwar tata ba,hannun ta saki tana baata fuska ta janye gefe,kafeta yayi da idanu yana mata alama data wuce yana yin gaba,binsa tayi a baya amira ta rufa musu baya,duk da haka bata haqura ba sai data tsaya saitin sumayyan murya qasa qasa
"Wannan hadi yayi kyau,Allah ka nunamin idanuwan su'ad naga ya zata yi" ta gefan idanu ta jefa mata harara amma hakan bai sanya ta fasa ba,waiwayowar musty din ne ya sanyata ja da baya tana raba idanu.

      Kai tsaye bangaren ummee suka soma shiga,a hankali suke takawa jere da junansu tamkar wasu shaqiqan masoya,su biyun ke zaune a falon ummee da maamaa,da alama suna tattauna wani abu ne,amsa sallamar sukayi kowacce fuskarta a sake,idanun umme bisa fuskarshi,shi ya soma yiwa kansa matsuguni kan daya daga cikin kujerun falon kafin ta qarasa takowa a ladabce zuwa cikin falon,kanta a qasa a kunyace ta qarasa amira na gefanta,wata kunya da nauyinsu take ji a yanzu wadda ta ninka ta da,musamman ummee wadda dama can ba wani sakewa ko sabo sosai tsakaninsu,gefe ta zauna qasan carfet kan ta a qasa
"Tashi ki koma saman kujera mana,wacce irin tafiya ce haka almustapha?" Ta tambayeshi tana dubansa,kanshi ya shafa yana yana yiwa ummeen magana da idanu zuwa sashen da su sumayya suke,ta fuskanci mai yake son fadi amma duk da haka bata fasa sake magana ba
"Babu sanarwa ba komai,halan ma baka barta ta kintsa ba ka tattago ta ko?" Inji ummeen tana bata rai,don tuni amira ta fesa mata yadda ya dauko sumayyan,cikim salon bada uziri yace
"Ummee,umarnin baba ne"dauke idanunta tayi ta maida kan sumayyan wadda suke gaisawa da anty maamaa,cikin murmushi ta soma gaidata
"Ummee ina yini"
"Lafiya qalau ya gajiyan hanya"
"Alhmdlh" ta fadi cikin ranta tana fadim wacce gajiya gurin mutumin da yayi tafiya a jirgi
"Anty kun yini lpy?" Cewar almustapha yana miqewa tsaye
"Lafiya qalau almustapha,ashe kuna hanya babu sanarwa bare ayi abun tarbar baqi" qaramin murmushi kawai ya saki na gefan baki,bai amsa ba sai ya jefo tambaya
"Baabaa fa?"
"Ya fita,yana can suna lissafin gidajen gonar nan"
"Ok" ya fada a taqaice yana takawa zuwa hanyar barin falon,ko motsawa sumayyan batayi ba,wanda hakan ya burge ummee da anty maamaan baki daya,ta tabbatar da cewa da su'ad ce da tuni miqe ta rufa mishi baya
"Kada ka rufe sashen idan ka shiga,anjima zamu kawo amarya" inji anty mama
"Ok" kawai yace yana ficewa a sashen,kamar jira amira takeyi ta buga tsalle ta iso gaban sumayyan
"Tashi muje namecy" harara ummee ta buga mata
"Saura ki hanata sakewa kuma bare ta huta gajiyan data kwaso ko?" Dariya amira tayi yayin da sumayya ta miqe ta bita tana murmushi kanta a qasa.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now