Babi na goma sha takwas

10.9K 1.3K 108
                                    

*Bismillahir rahmamir rahim*

*ala bi zikrillahi tad'ma innul quluub*

          Mamaki fal zuciyar sumayya,kanta ya daure tamau,ta kasa furta ma komai sai kallon mukhtar da takeyi,ta tabbata ba qarya ya yiwa fa'iza ba domin ba halinsa bane,amma halayyar fa'iza har ta kai haka?.

           "Ina naki abincin?" Mukhtar ya tambayeta,ta katse tunaninta ta dago ta dubeshi
"Ya d'aki"
"Ki dauko,ban amince kema. a yau kici ba,ki zuba a leda ki saka a shara a zubar,shiga kitchen ki samar mana abinda zamu ci koda indomie ce sai ki hada mana da qwai" ya fada yana kashingida gami da lumshe idanunsa,tsam ta miqe ta fice don aiwatar da abinda ya umarceta.

************************

           Cikin kwanakin ta dage sosai da addu'ar neman tsari,ta san tabbas shartin mutum girma gareshi,zuwa yanzu ta kuma sallama kaidin fa'iza,ta fahimci irinsu matan da suka dauki kishi ko a mutu ko ayi rai,irinsu wadanda zash iya aikata komai saboda kishi,sosai take takatsantsan kan duk wani motsi da kai kawo nata a gidan,ba ruwanta da sabgar fa'izan bare wani abu ya shiga tsakaninsu,koda fa'izan zata shekara tana takalar tashin hankali bata bi ta kanta,don ta riga ta tabbatar cewa akwai banbancin gida da kowaccensu ta fito,bai kyautu ta biye mata su zamana kamar wadanda suka fito daga gurbi guda ba.

********************

           Tun da asubahin ranar suka dinga jiyo kakarin amai a tsakar gidan nasu,sumayya ta dubi mukhtar dake gefanta wanda basu jima da kammala sallar asubahin ba kasancewar sun makara basu tashi da wuri ba
"Ya mukhtar,kamar kakarin amai nake ji fa a tsakar gida" shi din ma taji amma sam bai da muradin fita,tamkar bazai tanka ba sai ya daure yace
"Eh nima naji" yaci gaba da jan carbinsa,ganin yayi shiru ya sanya ta sake cewa
"Ya mukhtar ka duba mana,inajin kamar fa'iza ce fa" shiru ya sake mata ganin hakan ya sanya itama ta tsuke bakinta tayi shiru tana ci gaba da sauraran kakarin wanda yake fita tamkar da kayan cikinta,ya kammala azkar dinsa ya haye gado abinsa ya kashingida.

             Zuciyar musulunci ya sanyata ta kasa daurewa,sai ta miqe ta fidda hijabin jikinga ta nufi qofa,sanya baki yayi ya kirata tare da tambayarta ina zata
"Zanje na duba ne,bai kyautu da mutane cikin gidan ba kuma aqi fita a dubata ba,bamu san meke damunta ba" kai ya girgiza
"Dawo tausa nake so kimin"
"Kayi haquri naje na dubata din minti biyu kawai zan dawo sai na maka tausar"
"Idan ban isa da ke ba shikenan kina iya hakan" ya fada yana maida kansa ya kwantar kan pillow,sai jikinta yayi sanyi bata son saba masa ko kadan,saboda haka ta juyo a sanyaye tahaye gadon.

            A tausashe take masa tausar tana leqen fuskarsa ganin yaqi kulata,har ta soma tara qwalla bata iya jure fushinsa,sai taji kawai ya birkitota ya danneta da rabin jikinsa yana dariya qasa qasa
"Raguwa kawai sarkin kuka" ya fada yana lakuce mata hanci,dariya ta saki ya shiga mata cakulkuli daga haka suja shige duniyar ma'aurata wanda hakan shi ya hanasu fitowa da wuri.

             Qarfe goma ya gama shirinsa zaya fita,a tsakar gida daga can bakin qofar dakin fa'izan suka ganta zaune dirshan a qasa,ta wani wargaje can qafa can qafa tana numfashi da qyar,da sauri sumayya ta qarasa inda take tana fadin
"Hasbunallahu lafiya fa'iza?"
"Bani da lafiya" ta fada qasa qasa da qyar,ta daga kai ta kalli mukhtar da bai qaraso gun ba,yana tsaye abunsa bakin qofar dakin sumayyan yana daura agogo
"Yaya mukhtar,ko asibiti zamu?" Baice komai ba sai hannunsa da ya sanya cikin aljihun wandonsa ya zaro naira dubu biyu ya miqa mata
"Gashi sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya" ya sanya kansa soro ya tada machine dinsa ya fice.

            Tana jin rufe qofar gidan nashi ta miqe tamkar ba itace hajaran majaran ba,duk da yanayin jikinta ya nuna bata da qwari sosai,ta sakarwa sumayya harara sannan ta wafce kudin dake hannunta
"Babu inda zaki rakani munafuka" ta fada tana shigewa dakinta,kada kai sumayya tayi cikin zuciyarta tana fadin
"Allah ka shirya,wato hali zanan dutse".

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now