Babi na sittin da biyu

10.9K 936 73
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*KO KUNSAN SABODA BALA'I DA JAHANNAMA KE DA SHI HAR WANI SASHE NATA YANA NEMAN TSARI DA WANI SASHEN?*

*Allahumma ajirna minan nar*

_________________________________

        Luf tayi cikin motar idanuwanta a lumshe,duk da hayaniya da karadin da suke tayi cikin motar amma babu ita,bata san me ya haddasa mata mutuwar jiki ba,batasan me take tsoro ba,abu daya ta sani muryar na daga mata hankali,muryar na sanyata ta tuna da mukhtarinta,anty dije ma tayi tsammani bacci take saboda ta san jiya batayi wani isashshen bacci ba,yau kuma ta riga kowa sammakon tashi,tun tana jin hayaniyarsu sama sama har bacci barawo yayi awon gaba da ita.

      Kamar kullum yau ma sun tsayawa wannan restaurant din don cin abinci saidai banda ita,zaman ta tayi cikin mota sai takeaway sukayi mata sannan suka wuce.

      Yamma lis suka isa kano ta dabo tumbin giwa,ko da me kazo an fika,gari ba kani ba dajin Allah,wani farinciki ya dinga shigarta tun kafin su qarasa gida,iskar garin na kano take shaqa sosai,taje farinciki ya lullube zuciyarta,doki ya mamaye zuciyarta,kewar mama malam abdallah dama su zainab suka dawo mata sabuwa fil,kamar kuwa uncle farouq ya sani yace a fara biyawa gida a sauke sumayyan,anty dije zatayi qorafi kan ba haka ba su wuce gida idan sun huta baki daya sazo gobe yace a'a sam tana son taga mamanta,hakan ya mata dadi matuqa duk da ta boye dokinta,suna sauketa kuwa suka wuce kan sai gobe zasu shigo,tana fara'a ta daga musu hannu sannan ta sanya kanta cikin gidan yaran maqota na shiga mata da jakarta.

      A tsakar gidan ta ware muryarta tana kwada sallama,abdallah ne ya soma fitowa da gudu halima na biye da shi,da gudu ya qarasa wajenta yana kiran
"Mami na"
"Abdallah na" itama ta fada cike da kewa ta durqusa tare da ware hannayenta ya fada ciki ta miqe rungume da shi tana dubansa fuskarta fal murmushi,ya qara kyau wayo da girma kamar ba abdallahnta ba,kallo daya zakayi masa ka tabbatarwa kanka yana cikin kwanciyar hankali tare da samun cikakkiyar kulawa,yayi bul bul da shi,fes kamanninsa da babanshi kan fuskarsa.

       Dakin mama ta shige tare da su halima da maman,tana sanya kanta falon taga amina zaune matar abubakar ciki a gaba,baki sumayyan ta bude tana kallonta
"Antynmu kice kema kina gidan namu yau?"
"Gidanku ko gidanmu,aike kam yanzu baquwarmu ce" dariya sumayya tayi
"Allah sarki anty amina,kice kinyi nauyi shi yasa kika kasa tasowa ki tarbeni" dariya aminan tayi a dan kunyace saboda mama na gurin,gaban maman sumayya ta qarasa idonta a kanta tana jin wani dadi na gajin mahaifiyar tata,itama maman kallonta take,a gabanta ta durqusa ta gaidata,cikin farinciki maman ta amsa tana tambayarta ina dijen kuma,nan ta sanar mata sai gobe zasu shigo,hira ce ta barke babu qaqautawa tsakaninsu abdallah na kan cinyarta,yaqi yarda ko nan da can yaje,halima ke dungureshi tana cewa
"Zata tafi ta barmu da kai ne mai qaton kai da kaqi zuwa wajen kowa" amina ke kareshi
"Barshi malama,yaro da uwarsa,ai yayi qoqari ma,yaushe rabon da ya ganta?" Har magariba suna hira,sai da aka gama sallah magariba sannan sumayya ta cewa zainab ta hada mata ruwa zata yi wanka,dariya zainab tayi
"Wankan lafiya da daren nan?"
"Bazan iya bacci ba sai nayi wallahi" dariya ta kuma yi
"Kice ba banza ba yaya sumayya kika dad wannan dan banzan kyan,wallahi abuja ta karbeki,baki ga yadda kika koma 'yar gayu ba"
"Hada min ruwan sai kizo kici gaba da sharhin naki" sumayya ta fadi tana dariya,anty amina ce ta karbe
"Gaskiya ai ta fadi,wallahi garin ya amsheki sosai"
"Kin biye mata kenan antynmu" ta fada tana dariya anty aminan na tayata.

       Bayan tayi wanka ta sake shiryawa cikin doguwar riga ta wani cotting din yadi mau gajeran hannu,ta yane kanta da dan qaramin mayafi ta dawo falon mama,a nan suja zuba tuwon dare baki daya idan ka dauke maman,suna ci suna ci gaba da hira,har yanzun idanuwan maman ma kanta,ita kanta tasan diyar tata ta soma sauyawa kamar ba ita ba,ta tabbatar sauyin rayuwa ya fara samuwa a gareta,cikin zuciyarta ta dinga mata addu'ar Allah ya azurta ta da miji na gari,wanda zaici gaba da dawainiya da ita cikin ingantacciyar rayuwa.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now