Babi na talatin da biyu

14.9K 1.2K 367
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa iyyamsaskallu bi durrin fala khashifa lahu illa huw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih,yusibu bihi man yasha'u min ibadihi wa hul azizul gafur*

_"idan Allah yaso ka da cuta(lalura,abubuwa marasa dadi)babu wanda zai yaye maka face shi,idan kuma ya soka da alkhairi babu wanda ya isa ya maida falalarsa,yana sowa ga wanda yaga dama cikin bayinsa,haqiqa shi madaukaki ne mai gafara"_

       Cikin abinda duka bai wuce awanni biyu ba isar su asibitin da shiga dakin ganin likitan,umartar ta yayi da tahau wani dan gado wanda kusa da shi na'urar daukar hoton ciki ne.

       "Allahu akhbar" shine abinda likitan ke fadi yana jinjina kai tare da girmama iko na ubangiji,yaro ne kwance cikin mahaifarta ga motsi nan yana yi ga bugun zuciyarsa da komai,dukkansu ba wanda idonsa bai gani ba daga sumayya har mama,mamaki fal zukatansu tare da girmama lamarin buwayi gagara misali,sai da ya kammala komai har EDD sai da ya duba mata sannan yace ta sauko ya koma kan tebur dinsa ya soma rubuce rubuce.

       Magunguna ya rubuta mata wadanda zasu qara mata lafiya sannan ya bata wasu gwaje gwaje da ya kamata ace a wannam stage din da cikin ke da watanni hudu da sati uku tayi su
"Likita lafiyarsa qalau"furucin ya subuce ya fita daga bakinta jikinta a sanyaye,murmushi yayi yana dubanta
" lafiya qalau komai yake,babu wata damuwa tattare da shi"sai da ya bata amsar sannan kunya ta kamata ta sadda kai qasa,batasan cewa tana bala'in qaunar abinda ke cikin nata ba sai yanzu,wani qwarin gwiwa karsashi da soyayya take ji cikin ruhinta,banu shakka wannan karon tanajin zata iya yaqi kan cikinta a shirye take.

       Basu bar asibitin ba sai da suka kammala duk wani gwaji suka siyi magungunan suka nufi gida.

        Har yanzun maman ta kasa cewa komai kamar yada sumayya ta kasa magana,sam basuyi zato ba,basu tsammaci akwai sauran ciki jikin sumayyan ba,ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA ko ana muzuru ana shaho sai yayi kenan. Hakanan sumayyan ke jin zuciyarta fes da ita,bini bini ta saki murmushi tare da shafa cikin nata,maman na ankare da ita,tausayinta ya dinga ratsata,haqiqa babu dan halak din da zai guji haihuwa,babu wata halitta da bazato ganin jininta ba,dole dan adam ya koka idan ya rasa baya wato 'ya'ya,abu ne mai ciwo da cin zukata,Allah kuma maji roqo da addu'ar bayinsa ne,a yau gashi duk yadda akaso rabata da rabon da Allah ta bata amma hakan bai yiwu ba,ya riga ya QADDARA yana cikin QADDARARTA haihuwarsa da dadi ba dadi,saboda hikimarsa sai ya bawa yaron kulawa ta musamman,ya boyeshi daga kallon idanuwa,ta yadda ko mahaifiyarsa bata san da zamansa ba sai yanzu da buwayin sarki yaso ta sanin.

       Tun daga sanda suka koma gida daga asibitin maman ta fara bata kulawa ta musamman,ta hanata yin komai komai qanqantaraa,duk da babu wani ciwo ko laulayi da sumayyan keji,lafiya qalau take jin jikinta. Malam na dawowa maman ta sanar masa,sosai shima ya jinjina lamarin yana qara girmama isa da buwaya ta ubangiji,to ita kanta sumayyan ma alokacin ba'a zaci zata kai ba bare d'an dake cikinta
"Yanzu ya zama dole a sanarwa uban yaron saboda yasan da zaman cikin" inji mama.
"Wannan ya zama dole ai,zan sanya abubakar yayimin kiransa ko zuwa gobe ne" cewar malam.

       ****      ****    ****

      Kansa na duqe amma gumi tsatstsafo masa yake har ta kafar farcensa,babu shakka baya ga girman tsohon da yake gani da kuma farin sani da yayi masa kan wane shi da tashin farko zai qaryata batun da a yanzun yake gaya masa.
"Amma ga wadan nan ka duba hoton cikin ne da aka yi mata a jiya,idan ma duka basu gamsar ba kana iya zuwa gobe sai kuje da ita da su halima wani asibitin a sake gwada maka har da watannin cikin" malam ya fadi yana zube takaddun scanning da komai da komai a gabansa,jikinsa na rawa ya dauka ya soma dubawa,tsaf daya lissafa watannin cikin zuwa yanzu dai dai suke,sau taji wani abu na zaga shi,madaukakin farinciki ya wadatu a zuciyarsa
"Na gode maka ya Allah da baka bata damar salwantar min da ciki ba" ya fada cikin zuciyarsa idanunsa a lumshe,duk da zuwa yanzu yana mamakin me yasa ta aikata masa haka?,zuciyarsa kuma na kokwanton ita din ce da kanta?,wani sashi na zuciyarsa kan gaya masa ita dince mana,tunda kaga shaidu na magungunan cikin dakinta,kuma a baya likita ya tabbatar da ta sha din.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now