Babi na tamanin da bakwai

21.4K 1.5K 619
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*SANARWA DA BABBAR MURYA*

*BA NUFIN MU CIN ZARAFIN WANI KO BATAWA WANI BA,SABODA GUDUN RUBUTA MUNANAN AYYUKA CIKIN LITTAFIN AYYUKANMU,WANDA SAI MUN TSAYA GABAN UBANGIJI MUNYI BAYANI RANAR GOBE QIYAMA,AMMA TURA TA KAI BANGO,AN FARA SHIGA SHINGENMU ANA MANA BARNA,BAYAN MUN KAME KANMU DAGA DUKKAN WANI ABU DA ZAI ZAMA SHIGA HURUMIN WANI BATANCI KO CIN ZARAFI A GAREMU*

*GAREKU MASU SATAR FASAHA ZANCE KO BARAYIN ZAUNE*

*Ina mai shaidawa duk wani mahaluki da yasan cewa yaci da gumi na,ya dauki wani littafi nawa da na zauna na bata lokacina na rubutashi da hannu na don al'ummar ma'aiki su amfana,MALLAKINA ya kaishi wane waje ya saida yana zuba kudin a aljihunsa cewa NI SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA BAN YAFE BA,BAN YAFE BA,BAN YAFE BA,KUMA INA ROQON ALLAH YAYI MIN SAKAYYA KAYANA DA AKA DAUKA ANA SAIDAWA*

*GAREKA KO GAREKI BARAUNIYA A OKADA,DUK WANDA YA SANSHI KO YA SANTA YA ISAR MASA/TA*

*ABADAN DAYA SATA KOTA SATA,AKA KAISHI OKADA ANA SAIDAWA AKAN KUDI NAIRA DARI BIYU,NACE ALLAH YA ISA BAN YAFE BA,INA ROQON ALLAH KUMA YA FITAR MIN HAQQI NA MATUQAR BANI NA ZALUNCESU BA SU SUKA ZALUNCENI,TUNDA BAN TABA DAUKAR HAQQIN WANI MALLAKIN WANI NA MAIDA SHI MALLAKINA BA,ALLAH YA BIMIN HAQQINA,INA FATAR ZAKU SADAR DA WANNAN SAQO ZUWA GARESU*

*SANNAN WANNAN LITTAFI DA NAKE RUBUTAWA DAMA SAURAN LITTATTAFAINA,MALLAKINA NE,NA YISHI NE KYAUTA BA NA SAIDAWA BA,A DUK SANDA NAKE DA BUQATAR SAIDAWA ZAN SIYAR DIN,AMMA BAN BAIWA KOWA IZINI YA SIYAR MIN BA,WANDA KUMA YAYI HAKAN NA BARSHI DA FITOWAR RANA DA FADUWARTA,NA BARSHI DA MAI SAMA,MUGA ALFANUN DA ZAI SAMU CIKIN KUDIN DA KA SAMU TA HANYAR SAIDA ABUN SATA*

*WALLAHI WALLAHI ALLAH MU GUJI CIN HAQQIN WANI,BILLAHILLAZAI LA ILAHA ILLA HUWA DUK WANDA KA GANSHI RAN QIYAMA YA QETARE TO BABU HAQQIN WANI A KANSHI,WANNAN ALQAWARI NE NA UBANGIJI,SAI YA FITARWA DA DUK WANI BAWA HAQQINSA KAN DAN UWANSA,KODA DABBA CE TA ZALUNCI 'YAR UWARTA DABBA*

*ALLAH KASA MU DACE*
_____________________________________

ta fahimci salon magana ce kawai ta qwatar kai,tunda da aiki ne da tuni ya shaidawa baba,amma ko baban baisan da zuwanshi ba,koma meye tana maraba kuma tana fatan alkhairi da samun wannan kyakkyawan canjin,sai ta saki murmushi
"Masha Allah" ta fada tana maida dubanta ga sumayya
"Me zaku ci,ko zaki shiga kitchen ki sama muku ko snacks ne,yau duka ma'aikatan na can baya suna aikace aikace suma"
"Am ok ummee" almustapha ya fadi,farinciki ya mamayetq,ta tabbata tunda ya fadi hakan hakanne,sai ta waiwaya ta dubi sumayya
"To kefa amira?"
"Nima ummee na......"
"Qarya take,ba abinda naga taci tunda muka taho" almustapha ya katseta yana tsareta da ido,murmushi ya subucewa ummee,salon da bata taba gani wajen almustaphan ba yau sai gashi da shi
"Maza shiga ki samu wani abu kici,halan shi kin sama masa wani abun yaci ke baki ci komai ha ko?" Cikin kunya tana murmushi ta miqe kanta a qasa tayi kitchen din,yayin da ya bita da kallo yana yabawa salon kunyarta,yanayin yadda take ganin girma da darajar mahaifansa,tunanin yadda cikin qan qanin lokaci kan ya gama shiryawa ta hada misi wani hadadden patatoe salad ya fado masa,ya jima baici hadin salad da ya masa dadi irin wannan na,murmushi ua dan qwace masa,yanayim takun ta na burgeshi,ya dauke kai sanda ta kai ga shigewa kitchen din,sai suka hada ido da ummee,shi yai qasa da kai kunya na lullubeshi,ita kuma ta dauke kai tana sakin murmushin tsantsar farinciki,waskewa yayi da cewa
"Ummee ya adam bai qaraso bane?"
"Ka fadi haka mana tunda wannan karon ka rigashi zuwa,ina zaton sai wajen laraba zai qaraso,amma dai ni'ima ya hadato da yaran sunyo gaba,dazun da safe suka sauka,shi da fahariyya sai ran laraban"kai ya gyada cikin gamsuwa
"Kunje kun gaida maamaan ne?"
"A'ah"
"To bari ta fito sai kuje ku gaisa,da alama itama batasan da zuwan naka ba,babanku kam baya gari,ya tafi jigawa ta'aziyyar wani abokinsu da ya rasu,amma gobe ma zaya dawo" ta fadi tana daga wayarta dake ringing wanda amira ce ke kiranta,bayan sun gaisa take shaida mata zuwansu sumayyan,ihu ta saki har almustapha dake zaune yana jiyota,hararar wayar yake kaman amiran ma wajen,magiya ta dinga kan ummee ta bata sumayyan ta kira wayanta a kashe,dai dai sanda sumayyan ke fitowa daga kitchen din,ummi ta miqa mata wayar,a ladabce ta amsa ta koma gefe tana fidda murmushi,addu'a kawai take kada amiran ta baro zance ta bata kunya,ai kuwa zuba ta hau yi
"Amma namecy kinci amanar qauna da baki gayan har kin iso abuja ba,halan soyayya ta fara zaqi har kin soma mancewa da kowa sai wannan miskilin mijin naki,ina fatan kina bada wuta wajen sukurkuta masa shi muga ta tsiya,tab ai wallahi jibi nima zan taho Allah,ina fata kin samo mana tsaraban baby,wallahi har so nake naga babynku,kyau tako ina,wazai dauko uwa ko uba?,wa yaga ya man ya baby" gaba daya kunya ta cika sumayyan,yadda almustapha kadai ya kafeta da ido tasan yanajin komai amiran ke fada,ta sanshi sarai da kaifin ji,yunqurin datse kiran take sai ya miqa mata hannu,a hankali ta tako ta miqa masa wayar,ya kara akunnensa sanda amiran ke cewa
"Wayyo soyayyya zamu sha kallo......"
"Gidanku mara kunya fitsararra,idan naga qafarki gidan nan jibi sai na karyata na zubar,idan kin musa kuma bismillah" ya datse kiran,daga bangaren amira sai ta kwabe fuska zata sanya kuka,saifullah dake zqune gefanta ya dunga tiqa dariya har da qwarewa da lemon da yake sh,haushi ya sanyata daukan filo ta dinga maka mishi shi kuwa yana fadin
"Maganin aku kuturu mai shegen zance kenan,tun dazun nake kwabarki kiyi a hankali may be suna tare amma kika qi ji,tunda kuwa ya man ya fadi haka ke da zuwa gida sai ana gobe daurin aure"kuka kuwa ta sanya taba buga qafa
"wallahi wallahi ban yarda ba,don kawai kaji ya almustapha ya fada ko?"sai ta saki filon ta wuce bedroom alamaun taji haushi ya miqe da sauri ya bita domin yayi lallashi.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now