_Bismillahir rahmanir rahim_
_iza qada amran fa innama yaqulu lahu kun fa yakun_
Sati guda da kammala gyara gidan ranar wata litinin mukhtar ke gaya mata ran laraba masu kafin amarya zasu zo,sai da taji wata faduwar gaba da bata san ta mece ba
"Allah ya kawo su" ta fada kawai kana tayi shiru tana dubansa yana rubuta lissafin kasuwa cikin wani qaramin excercise book.Jin shirun yayi yawa ya sanyashi dago kansa ya dubeta,sai yaga littafin take kallo,ya sanya tsinin biron ya dan mintsini cinyarta,sai ga dago tana dubansa fuskarta dauke da murmushi tana sosa gurin
"Yadai 'yammata?" Kai ta girgiza tana murmushi
"Babu komai.....cewa nayi ai za'a yi musu girki ko,tunda naga ana yi",rai ya bata,don yasan yanzu zata fara soko masa zantukan da baiso,ya tabbatar sumayya danya ce shakaf,domin da wata macen ce aka yi mata zancan kishiya da tuni yanzu gidan ya dade da zama dan qaramin sansanin yaqi,ya tabbatar ba qaramin dauki ba dadi za'a yi ba,duk da quruciyarta ma ya tabbatar da gudun mawar qarin tarbiyya da ta samo daga gida,tunda ko a gidansu bata taso taga mamanta da kishiya ba,da wata ce wannan kadai ya isheta mafaka." ba da kayan abinci na ba,kuma kema ban lamunce kiyi ba,idan kunne yaji....."sai ta ja bakinta ta tsuke,don bata son yayi fushi da ita irin na baya kan zancan fenti da lefe.
Washe gari ranar talata gefin magariba lokacin dawowarsa,ta gama komai kamar yadda yake al'adarta,gidan nata qamshin turaren tsinke,tana tsakiyar yaranta ta siyo madarar ruwa ta musu iloka ta rarraba musu suna sha,wani yaro dake bayan gidansu yayi sallama dauke da akwati wasu yaran na bayansa.
"Wai gashi inji yaya mukhtar" ya fada kamar yadda yaji matar gidan na gaya masa,sai mamaki ya kamata don bata ji alamar shigowarsa ko qarar babur dinsa ba,tashi tayi ta bude masa labulen falonta suka shiga da su,akwatunane guda shida masu kyau duka iri daya uku set daya uku set daya.
Suna fita ya shigo yana dauke da baqar leda,duka yaran suka masa sannu da zuwa suna qoqarin tafiya gida,ya bibbisu da alawa kamar yadda al'adaraa take sannan suka bi sumayya da
"Anty sai da safe.....anty sai gobe"
"To Allah ya bamu alheri" ta amsa musu suka fice ta rufe gidan sannan tabi bayan mukhtar da tuni ya shige falon.Murmushi ta sakar masa kamar yadda ya sakar mata
"Kinyi kyau sumayya ta" kanta ta sunkuyar cikin kunya tana murmushi
"Na gode yaya na,sannu da zuwa" ta fada tana cire masa hular kansa da bai samu cirewa ba
"Ya kasuwar" ta sake fadi tana qoqarin ajjiye masa ruwa mai sanyi
"Kasuwa alhamdulillah......kinga ai my sumy abinci zaki kawomin don yunwa nake ji",ta dan zaro ido tana dubansa
" da wuri haka yau?,na zaci sai ka dawo daga sallar magariba",shafa cikinsa yayi yana murmushi
"Salla bazata yiwu cikin nutsuwa ba ina fama da yunwa,taimakeni ki bani sumayya magaribar da sauran lokaci,idan na kammala ko masallacin sun idar mayi jam'in da ke"
"To" ta fada tana miqewa zuwa kitchen.Bayan ta gabatar masa da komai tuwon semo ne miyar kuka sai qamshin daddawa take duk da babu nama amma tayi dadi qwarai,taasa bismillah sannan ta koma gefansa ta zauna.
Sai da ya kai loma biyu sannan yace
"Ga kayanku nan ki duba kiga" ya fada yana mata nuni da akwatunan dake jere gefe,da to ta amsa masa sannan sannan ta sauka qasa ta janyo akwatunan ta soma dubawa.Tana dubawa yana zuba mata santin tuwo,yayin da itama ke santin kayan,komai yayi kyau,sai data kammala tas,lokacin har ya gama cin twon ya jngina da kujera yana kallonta tana ta daga kayan tana yabawa,ta rurrufesu yadda ta gansu sannan ta dubeshi.
"Nayi zaton ma har an kai kayan ne naga lokaci ya qurato""Um um" ya fada a taqaice
"Sunyi kyau sosai ya mukhtar,Allah ya qara budi,saidai komai naga bibbiyu ka saka kala daya,nufina kayan dake cikin akwatin kayan sawa sune a daya akwatin,under wears da mayafai ma"
YOU ARE READING
KUNDIN QADDARATA
Mystery / ThrillerKalmar QADDARA kalma ce dake rataye bisa wuyan kowanne bawa,haka rayuwa ta gada,tafe take da QADDARORI kala kala,masu zaqi da akasin haka............. SUMAYYA na kallon yadda KUNDIN QADDARARTA ke ta bude mata shafi bayan shafi na TATA QADDARAR kowan...