Babi na goma sha hudu

9.9K 1.1K 87
                                    

*A hasiban nasi ay yaquluu amanna wa hum la yuftanun?*



Qarfe goma na dare tana saman gadon innar tata,juyi kawai takeyi tare da tuhuma da kuma bincikar kanta kan abinda ta aikata,batasan dalili ba batasan me yasa ba amma ji ta dinga yi kamar ana ingizata barin gidan,wata qauna da kewar mukhtar din suka kamata,halima ce ta shigo dauke da wayar innarsu
"Yaya sumayya,yaya mukhtar ne" ta fada tana miqa mata wayar,da sauri ta miqe ta amsa wayar sannan ta kara a kunnenta halima ta juya ta fita,kasa cewa komai tayi har sai da yace
"Sumayyah!" Muryarsa a tausashe
"Na'am" ta amsa muryarta na rawa
"Sumayya......me yasa kike son ki gujemin bayan kinsan zuciyata ba zata juri haka ba?,sumayya ko cikin mafarki banson mu rabu bare a gaske,a zahiri kuma idanu biyu" tuni ta fara tara qwalla a idanunta,zuciyarta na sake karyewa
"Ya mukhtar ban sani ba,nima bansan dalili ba da ya sanya na tsani dakina ba,bansan dalili ba na tsani dakina ma baki daya ba,kayi haquri ya mukhtar........kaji?" Shiru yayi yana mamako,babu shakka gaskiya take gaya masa har cikin zuciyarta,ya riga da yasan sumayyan sosai,koma mene yana jin ya haqura ya bada kwana ukun kamar yadda malam yace yaci gaba da addu'a kamin zuwan kwanakin,ajiyar zuciya ya sauke sannan yace
"Shikenan....babu komai kada ki damu kinji,muyi addu'a mu jira kwanakin ukun kamar yadda malam yace"
"To" ta fada,sai ya kawar da zancan ya soko wani don son faranta mata rai da kawar da zancan
"Yanzu me zan samu my sumy,nayi kewarki sosai,na dawo da kewar taki kuma tarar kin min yaji" ya qarashe cikin sigar shagwaba,dariya sosai ya bata har ta dinga jiyo sautinta ta cikin wayar wanda hakan ya masa dadi sosai,kewarsa taji ya kamata kamar ta bude idanu ta ganta gabanshi,nan ya janyeta da hira har sai da ya qarar da dukka kudin dake cikin wayarsa sannan ya haqura.

Cikin kwanakin duk wani hadi da malam din ya sani na kariya daga shaidanu ya hada ma sumayyan,suratul baqara itace ruwan shanta,ayatush shifa,da ayoyin karya sihiri,hadin ganyan magarya,man habbatus sauda shi take shafawa saboda yana kore duk wani shaidani da zai iya kusantarka,sai turaruka daban daban,azkar na safiya da maraice da wasu qarin addu'o'in kan wanda takeyi

Ita kanta cikin jiki da zuciyarta take jin salama da farinciki,dokin ganin mukhtar da son komawarta dakinta take.

Ranar kwana na biyun da maraice sai ga abdur rahman,sosai tayi mamakin ganinsa yace mata yaje gidan bai tadda ta ba,wannan sabuwar abokiyar zaman nata ta gaya masa bata nan,ta tafi kuma ba zata dawo ba,bata boyewa abdur rahman din komai ba ta gaya mishi.

Ya jima yana jinjina kansa sannan yace
"Idan zaki amince ina da buqatar muqullin dakin naki zan duba shi ko da taimakon da zan iya miki,kinsan fannin magungunan musulunci na karanta,yanzun haka ma yaya mukhtar din nazo kawowa katin gayyata zuwa bude asibiti da zamu dinga treating cututtuka da magungunan musulunci" cike da gamsuwa ba tare da haufi ba ta shiga daki ta miqa masa muqullin ya amsa ya mata sallama ya fice,a qofar gidan ha tsaya ya fidda wayarsa ya kira mukhtar ya shaida masa,take ya bashi izinin shiga,sai da yayi sallama sau biyar duka aka masa tare da dora
"Dalla a shigo an cikawa mutane kunne da wata sallama" a tunaninta yaya yahanasu ce ta mata aike,kai tsaye ya doshi dakin sumayyan ya bude ya shiga.

Cikin nutsuwa ya dinga nazarin dakin bayan wasu addu'o'i da ya dinga karantawa a bayyane,fa'iza na tsakar gida kame da qugu tana leqen dakin gabanta na faduwa,addu'arta daya kada ya zamto ya karya duk wani kafi da shiri da tasa aka yiwa dakin.

Tsawon mintina talatin ya kwashe cikin dakin yana karanta wasu ayoyi sannan ya kulle dakin ya fice,da kallo ta bishi fa'izar kamar idanunta kamar zai fado,sai da taga fitarsa sannan ta saki ajiyar zuciya tare da zama gefan rijiya.

Saidai bai wuce wasu mintina talatin din ba sai gashi ya dawo,hannunsa dauke da kaskon wuta mai garwashi sai qwarya,dakin ya sake budewa ya shiga bayan ya tari ruwa cikin qwaryan,zama yayi sosai kan daya daga cikin kujerun yayi bismillah ya fara karanta ayatur ruqya gabaki dayanta,sannan yabi kowanne lungu da saqo na dakin ya yayyafeshi tas da ruwan,komawa yayi falon ya ajjiye qwaryar ya bude wata farar leda mai dauke da 'ya'yan habbatus sauda ya watsa cikin dakin ya shiga turare dakin ciki da falo.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now