Babi na tamanin da biyar

19.3K 1.3K 308
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wannan page din kuma naku ne*

*sparkling son sorians by batool mamman*

*Allah ya bar zumunci*

_____________________________________

A qalla ya kusa minti talatin zaune cikin motar a qofar gidansu,ya dubi agogo karo na kusan biyar yaja dan qaramin tsaki,baisan me ya jawoshi qofar gidan ba,to idan ya shiga yace me?,me ya kawoshi?,la'asar ne bare yace malam yazo gani,bai da tabbacin yana cikin gida a wannan lokacin,tun suna hanya ya dinga kai kawo cikin wayarsa bangaren adana lambobi baiga komai ba da zai iya amfani da shi,ya motsa labbansa da niyyar bawa drivan umarnin yaja motar su wuce sai yaga fitowar malam din,sanye da shadda milk babbar riga,fuska akwai ruwa da alama alwala ya kammala masallaci ya nufa zaiyi sallar la'asar,cikin hanzari ya balle murfin motar ya fito,dakatawa malam yayi ya zubawa wajen ido sanda yake qarasowa
"A'ah,mustapha ne?,saukar yaushe?yanzu dama tasan da zuwanka amma ta fita unguwa?" A ladabce ya fara shirin rusunawa malam ya dakatar da shi da hanzari
"A'ah,miqe kada ka bata jikinka" duk da haka sai da ya dan rage tsawonshi suka gaisa
"Bari na baka ruwa ka daura alwala idan mun dawo sai mu shiga ciki ko?" Malam ya fada yana niyyar juyawa ciki,jin haka ya sanya drivansa saurin komawa mota don dauko masa ruwan riba,da hannu ya dakatar da shi,suna tsaye malam ya iso da butar ya miqa masa,ya koma saman dandamalin qofar gidan ya fara daura alwalar,a hankali yara suna fara giftawa suna kallonshi,kafin ya kammala sai ga yara sun soma taruwa suna kallonshi,a tsakaninsu suke qus qus din balarabe ne wlh,murmushi malam ya saki don ya jisu,karbar butar malam yayi ya aiki daya daga cikin yaran ya maida gida sannan suka wuce masallacin tare.

Tare suka jero da malam din suna hira jefi jefi har suka qaraso gidan,da kansa malam din ya bude masa sitting room yace ya shiga ya zauna,bai musa ba ya shiga ya zauna din yana qarewa falon kallo,ciki malam ya koma ya sake kiran sumayya ya shaida mata duk abinda take ta baro ta taho tayi baqi,cikin mamakin wanne irin baqi tayi haka tace masa tana dab da shigowa unguwar ta iso tuntuni.

Cikin sanda ta shigi soron,idanuwanta kan takalmin sau ciki dake qofar sitting room din,cikin gidan ta wuce kai tsaye,mama ta taras a falo tana wanke wani rubutu,tun da tazo taga tana yinsa kullum da yamma batasan dai ko na meye ba,baki sake maman ta kalleta
"Me kika shigo kuma yi?,baqon ai yana sitting room"gabanta ke faduwa hakanan da wani irin tsoro
" waye mama?"
"Idan kin shuga kya gani,tsaya ki karbi wannan ki shanye tunda kin riga da kin shigo" inji maman tana juye wani rubutun daga wata jarka wanda ke gauraye da zuma ta miqa mata,bata musa ba ta karba ra kwankwade,sannan ya zare niqab dinta daga saman zabgegen hijabin dake jikinta,don tunda tazo ta koma wannan shigar,sakamakon yadda aketa tanka canzawar da tayi,bugu da qari da yawan kallon da take fuskanta wajen maza idan ta fita,jakarta ta sabule ta ajjiye saman kujera ta dubi mama
"Kayana an kawo gugar?"
"Akwatin ma a hade yake,ba jibi ko gata zaki wuce ba?"
"Eh amma mama nikam banson tafiya wlh,da sai ranar daurin aure kawai" harararta maman tayi
"Ban koya miki sabawa umarnin miji ba,randa yace ki tafi koda yau ne tafiya zakiyi" murmushi ta saki kawai ta juya ta fice,tunda tazo maman bata da aiki sai ja mata kunnen tabi miji.

Tun kafin ta kai ga shiga dakin take ji qamshin wani turare kamar ta sanshi,hannu ta sanya ta yaye labulen bakinta dauke da sallama,idanu ya zuba mata yana dubanta,baki daya ko ina na jikinta a lullube yake tun daga saman qafarta har zuwa kanta da hijabi,wani sanyi yaji ya ratsashi,karon farko yaji shigar tayi masa,ba abinda ke nunawa a jikinta,idanu suka hada ta saki labulen tana takawa a hanakali kamar mai taka qaya,wani shegen kwarjini yayi mata,ya cika mata idanu baki daya,bai fasa kallonta ba har ta qaraso kan daya daga cikin kujerun dake zagaye da falon ta yiwa kanta matsugunni,gababshi kewaye da ruwa da lemuka saidai babu wanda ya taba
"Sannu da zuwa" ta fada tana dubanshi qasa qasa
"Ina kika je?" Ya tambayeta maimakon amsa
"Gidan aunty na,aunty salma"
"Wa kika tambaya?" Wannan karon dagowa tayi ta zuba masa idanu cikin mamaki,taga dai dole idan tazo ya sani zata gidan 'yan uwa dai,janye nashibidanun yayi wannan karon,kallon da take masa yana sake kasheshi da narkar da duk wani sashe mai muhimmanci dake jikinsa
"Tashi ki dauko kayanki mu wuce?" Ranta ya baci,take idanunta suka hada qwalla
"Amma sai jibi ai zan wuce abujan ko?,yau fa kwana na shida fa anan din?"
"Haka nake da buqata idan kuma ban isa ba to" idanunta ta kawar qwallar na zirarowa a idanunta,ta miqe tamkar zata rushe da kuka ta fice.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now