Babi na saba'in da uku

13.7K 1.2K 247
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL*

__________________________________

       Baabaa prof ji yake kamar isha'in ba zata yi ba,fata yake cikin ransa Allah ubangiji ya sanya sulensa ne,Allah ya qaddara saduwarsu,haka kawai yake jin zumudin zuwan sallar isha'in yayi yaje yayi tozali da mai wannan suna.

       Kai tsaye gidansa daya fara zama cikin garin kano tun zamanin quruciya can aka wuce da shi,gidan har yanzu yana nan da kyansa da daukar hankali,kasancewar bai bar gidan ya lalace ba,ko yaushe sake sabunta shi ake saboda ba'a rasa cikin iyalansa mash zuwa kanon,gida take kano a gun kowa,ko baka shigo ka zauna cikinta ba baqunta ko kasuwanci ya kawoka,ko ba haka ba ma hanya ta wuce da kai ta cikinta,wanka yayi ya sauya shiga sannan suka wuce masallaci shi da mus'ab da mahmoud baki daya kasancewar dab ake sa fara sallar magariba.

       Basu suka baro masallacin ba sai da akayi sallar isha'i,kai tsaye hassan driver ya koma gida ya fiddo motar ya kawota bakin masallaci suka shiga,tafiya ce da bata wuce minti talatin ba ta maidasu unguwar,guri suka samu sukayi parking sannan suka aika yaro yaje ya sanar da malam ana sallama,cikin sakanni ya dawo ya gaya masa yana fitowa.

      Tsaiwar mintuna biyar kacal ya hangoshi,idanuwa ya zuba masa baki daya ko qwaqwaqwaran motsi baya yi,tun kafin ya kai ga qarasowa inda suke ya shaidashi,girma ko tsufa baiyi isar da zaya sanya ya kasa gane sulenshi ba,dadi ko wuya babu abinda zai mantar da shi sule,shima takowa yake saidai sam bai kula da wanda ke gabansa,kasancewar yafi ganin mahmoud da musa'ab dake tsaye gaban baabaa prof din,a hankali ya qaraso ya dubi su mahmoud a nutse
"Yan samari kuke sallama da ni?"
"Basu bane,muntarinka ne,muntarinka ne sule,suken mai gado" da hanzari ya daga kai shima din gani waye?waye wannan dake ambatarsa da sunan nan qwaya daya jal da yasan duk gadin karkararsu shi kadai ke kiransa da shi,ya sanya masa sunan me tun daga lokacin da malam muhammadu(mahaifin baabaa prof) ya basu tarihin annabi sulaimanu da nana bilkisu,kutsawa yayi tsakiyar su mahmoud yana fatan kayalinsa ya zama gaskiya,ya tabbata kuwa,muntarinsa ne,muntarin da kullum matuqar rana zata fito ta fadi walau yana da cikakkiyar lafiya koko babu ita sai ya tunashi,sai yayi begen ganinsa,da sauri suka qarasa zuwa ga juna suka rungume juna kowa na ambatar sunan dan uwanshi,kowannansu jikinshi na rawa,lamarin ya yiwa su mahmoud nauyi ganin yadda dattawa ke fidda ruwan hawaye,yara masu wucewa suka soma tsayawa suna tunanin wani abu ne ya faru ga malam din,mus'ab ne yayi qarfin halin cewa
"Amm,baabaa yara fa sun fara tsayawa" abinda ya fargar da malam kenan ya saki muntari yana kallonshi,ji yake kamar zai sake bace masa bazai kuma ganinsa ba,ko kuma mafarkin da ya saba ne yake yi
"Ina zuwa" malam ya fada cikin sauri har yaja tuntube ya shiga gida a gaggauce ya karbi muqullin sitting room wajen mama yana shaida masa yau ga muntarinsa a gidansa,muqullin kawai ta bashi tana tantama,muntarin da tunda suka hadu take jin sunanshi daga bakinsa amma bata taba ji sun hadu ba shine tau aka ganshi?.

       Jikinsa har rawa yakeyi ya bude sitting room din suka shiga,har yanzu kowannansu gani yake kamar almara
"Sule kaine?,ko almara ce?"
"Nima haka nake ji muntari,saidai lamarin ubangiji yafi gaban haka,shi sami'ud du'a ne"
"Qwarai kuwa ba shakka"doguwar gaisuwa sukayi bayan sun gama sumbatun ganin juna,sam sun mance ma da wani mus'ab da mahmoud a wajen,har sai da mahomud da mus'ab din suka matso suna gaida malam ya amsa fuskarshi na fitar da annuri,dukkan wani nauyi dake cikin zuciyarsa ya yaye,a yau ya tabbata farinciki bazai barshi yayi bacci ba
" wadan nan 'ya'ya na ne sule,gasunan,akwai biyar a gida,baya ga jikoki da suka kusan tasamma guda goma matan aure biyu,kaifa sule?,ya rayuwa ta kasance?"ya fada yana dubansa,wani sashi na zuciyarsa na masa susa ganin alamun sulen bai kama koda kaso daya cikin goma na arziqin da shi yake da shi ba,bayan kusan tare suka sha wuyar tattala da tara dukiyar,saidai alhamdulillahi kana ganinsa kasan baya cikin wahala,yana cikin matuqar rufin asiri,miqewa mahmoud sukayi shida mus'ab suka koma qofar gida don bash waje suji dadin ganawa sosai,gyaran murya malam yayi sannan yace
"Bayan barina garinmu muntari na jima bansan inda hankalina yake ba,da na tashi kawai na tsinci kaina cikin makarantar allo ta almajirai,wani malami dake yawon rarraba almajirai ya tsintoni ya hada da yaran da zai kawo kano,sai na karbi rayuwar a yadda na ganni,na riqe karatuna da hannu bibbiyu,na zama daya daga cikin hamshaqan dalibai haziqai da malam ke ji da su,gefe daya kuma kasan tun asali bani da matacciyar zuciya,a duk lokutan da ba na karatu bane nakan fita neman na kaina,duk aikin da na samu zanyi kowanne iri indai na halal ne,batun gida kam baki daya na manta ma ni din dan wanne gari ne,tun malam na damuwa yana qoqarin tambayata har ya haqura ya watsar a haka rayuwa taci gaba da turawa,na samu cikakkiyar haddar alqur'ani mai girma,na zama daya daga cikin amintattun malam,'yan gaban goshinsa,muntari ban tashi tunawa da garinmu ba sai sanda Allah ya yiwa mahaifina rasuwa,naje na tadda rasuwarshi,na kuma samu labarin dukan abun arziqin da kake yi,na tambaya saidai kash ko daya ba wanda yasan inda kuka koma acikin gari,suce zuwa musu kake ka koma,da haka na isa ga dangin mahaifiyata wadamda suma mutuwa ta daddaukesu sai 'yan ragiwa,muka gaisa na dawo cikin gari na hau cigiyarka,wasu suce min sun sanka amma basu san matsugunninku ba,wasu suce ma basu sanka ba,da haka na haqura da dawo kano bani qwarin gwiwa,bayan wasu shekaru ban haqura ba na sake komawa,sai naje na tadda ma baki daya kunyi qaura daga gombe kun dawo kano,naji dadin hakan saboda ina zaton zan sameka ta sauqi tunda muna gari daya,saidai na manta cewa kano nada girma da fadi yawan al'umma da yawan qabilu,akwai tarin qananan hukumomi qarqashinta,haka na qaraci nemana tsawon shekaru,tun inayi tuquru da qarfina har na haqura.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now