01

8.3K 351 17
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳

Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*😘

In dedicated 2 nafsee

*0⃣1⃣*

*BISIMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*

Kwanche take akan gadon asibiti , kana ganinta kasan tana chikin tashin hankali mara misaltuwa , duk da rashin lafiyar da take chiki hakan bai sa nakasa gane kyan halittar yarinyar ba , yarinyache karama wadda shekarun na haihuwa baza suwuche shashida bah fatarta tanada haske amma ba fara bacheba , tanada matsakaichin tsayi , fuskarta Yar doguwache , tanada dara-daran idanu wadanda suke dauke da lashes zara-zara , ga hanchinta dogo ne madaidaichi , girarta siririyache amma kuma bakache sosai , saidan lip dinta wanda yake pink ne amma kadan ba sosaiba , sai gashin fuskarta wanda yakwanta sosai afuskarta har yafutar mata da wani siririn saje wanda ya kara qawata kyan fuskar tata . Ahankali naga yarinyar tafara motsi , idanunta ne suka fara budewa ahankali, dafarko hazo-hazo tafara gani, lokachin da tagama bude idanun ta lokachin ganinta yafara dawo wa daidai, ganinta tayi ah chikin asibiti, kuma akan gadon asibiti, ahankali ta fara tuna abubuwan da suka faru awannin baya da suka wuche, hawayene yake zirarowa daga idanunta zuwa kunnenta kasanchewar akwanche take , yayinda take furta
" innalillahi wa inna'ilaihir raji'un" ahankali chikin yanayi na mara lafiya , batasan tachigaba da tunawa da abunda yafaru, da ache akwai yanda zatayi tayi formating dinshi daga kwakwalwarta da tayi, kuka takeyi sosai amma bame sauti bah, turo kofar dakin akayi, yayinda naga wani mutumi sanyeda lab coat yashigo dakin, koba'a fada bah nasan likitane , wani mutumine ke binsa abaya saikuma wata mata, matar da tashigo akarshe che ta tura kofar dakin , ina kyautata zaton sune iyayen wadda ke kwanche kan gadon asibitin, dan naga alamar kama ataredasu, mutumin ne yafara karasowa dasauri yayinda matar tabiyoshi abaya itama chikin sassarfa, dasauri takama hannun yarinyar ta rige gagam kamar wani zai kwache mata ita, yayinda itama hawayen yake zuba ah idanunta, kowa achikinsu yakasa magana, mutumin ne yayi karfin halin chewa
" ya jikin naki shukuriyya ? Akwai inda yake miki zafi ? Yakike jin jikinnaki ?"
Duk ah lokachi daya ya zubo mata wadannan tambayoyin wadanda yayi karfin halin yinsu, dazarar ka kalleshi kasan yana chikin tashin hankali, kallanshi tayi Chike da karfin hali, bazata iya magana bah saboda yanda takejin zuchiyarta, saidai bazata iya share mahaifinta bah, murmushi tayi masa yayinda tayi kokarin tsayar da zubar hawayen da idonta yakeyi , domin batasan ganin tashin hankalin iyayennata, tanajin tausayinsu ah ranta dukda tasan chewar itache abar tausayi .
"Alhaji inaso ku kwantar da hankalinku, tana qara jin sauki kuma idan Allah ya yarda nan bada dadewa bah xata warware gaba daya, abun bukatar shine kwanchiyar hankalinku, ynxu inaso kuyi hakuri kubata wuri ta huta dan tana bukatar hakan"
likita ne yake wannan maganar chikin lumana da tausasar zuchiya fuskarsa dauke da alamun tausayi, matar che ta saki hannun yarinyar suka fiche daga dakin batareda sun Kara chewa komai bah, Umma kuwa ah zuchiyarta chewa takeyi tayaya zamu kwantar da hankalinmu alhalin y'armu tana chikin wannan tashin hankalin , bayan fichewarsu likita yayi yan dubedubensa kana yache
"yakike jin jikin naki shukuriyya ?" Rintse idanunta tayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, tache
" banajin komai likita saidai xafin danakejin jikina yanamun, musamman kirjina inajin wani abu ah tokare ah gurin"
likita yache
"indai wannan ne karki damu namiki allura da zarar kin samu kinyi bacchi kin farka zai sauka da yardar Allah"
daga mai kai kawai tayi alamar ta fahimchi abunda yake nufi sannan yafiche daga dakin, kamar jira take yafita, aikuwa yana fita tafara kuka mai tsuma zuchiyar mai sauraro, mutuqar ba kukan tayibah baxata ji sanyi ah ranta bah
"Allah ka sakamun!!! Allah ka sakamun!!"
Shine kawai abunda take iya furtawa, ta takure kanta guri daya dukda zafin da jikinta yake mata, daga karshe ma hannu ta daura akanta tana kuka sosai
" wannan wache iriyar *QADDARAR RAYUWA* che? nashiga uku, astagafirullah, Allah ka sakamun, Allah na tuba, wayyo Allah"
wadannan sune kalaman da shukuriyya kawai take iya furtawa , magana takeyi kamar wadda ta zauche, kana ganinta kasan tashin hankalin da take chiki ba karami bane, kuka takeyi sosai har tana shidewa , tun kana jin abunda take fada harka daina ji , daga bisani barchi yakwasheta akan gadon asibitin.

Meerah

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now