🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳
Written by CUTTIEEMEERAH
Assalamu'alaikum how you doing all? I apologize about the delay, but work, house stuffs is pretty busy!
If i could get any opportunity to write it should be QR, just know that ure in my mind......
Thank you all for your patience and support!!!!
1⃣0⃣0⃣
Taran suna akayi na gani na fad'a, wanda ya bar tarihi me dunbun yawa, akan taran sunan suka fanshe duk wani taro da basuyi ah baya ba, kana kallan yanda yanayi bikin yake tafiya zaka fahimchi chewar taro nerh na keche raini akayishi, twins sunchi sunayen parents din Nene, tajuddeen da hauwa-kulu, wanda hakan seda yasa Nene zubar hawaye dan bata tab'a tsammanin hakan ba, Allah yasan ko saka rai batayi ba, aranta saida taji dana sanin abubuwa dayawa dasuka faru abaya, she regret all that she have done, zuchiyanta be ta6a saqa mata hakan bah, she did more than enough to haiydar amma gashi yau!!!
Haka taran sunan ya watse lafiya lau, anraba kitchen utensils kala kala, atamfofi, calenders, memo, bags ko wanne dauke da hotunan twins d'in ajiki, sosai akayi 6arnar dukiya kowa yatafi yana sambarka.....
Chikin dare kowa ya gaji, more especially shukuriyya da twins, harga Allah saida ta gaji da snapping pictures, tun tana iya murmushin dole harsaida ta kasa, she can't wait to see the pictures dan tasan dayawa batayi kyau ba, it's not really easy, haka ta sake wanka tayi addu'ah sannan ta kwanta......
The next day da yamma su umma suka koma KD itada su kaka da inna, harda su haniff aka tafi dukda chewan sunso abarsu amma school baze bari bah......
Bangaren maganar auren mashkur kuwa wata d'aya aka qara, da sukayi magana da Sophie ma chewa tayi aqara 3month, dan har chikin zuchiyarta taji haushin chewa aqara din dayayi, anata nazarin wannan sam ba dalili bane ba, domin duk sun shirya wa bikin, both familyn ta da frnds dinta,harta gyaran jiki ta fara zuwa sannan yazo mata da maganar, shiko beyi tunanin gatse ta mishi ba, haka yaje ya sanar da su umma, sune ma suka che tayi yawa, abar wata dayan kawai, kafin nan yara sunyi kwari, anashi fad'in ma zuwa lokachin shikanshi yaqara samun yarda yakeso........
One week kenan da rad'in suna, yara har sunyi 6ul6ul dasu dasu kamar kwanakinshi yafi 14, ah hakan ma basa samun wadatcchen ruwan nono daga wurin mahaifiyarsu, mafi yawan abinchin su madara nerh ake basu, amma idan kaga yanda sukayi qwari abun ze baka mamaki, kamar wasu yaran turawa, shar-shar dasu gwanin ban sha'awa, farare tas kyawawa, haqiqa Allah yayi halitta awurin...
Dayawan lokachi idan goggo ta d'aukesu tana musu wasa takan che duk sun zuqe mahaifiyarsu ita daman ba jikin arziqi ba, saidai shukuriyya tayi dariya kawai,,,,,
dan gaskiyar goggo nerh duk kwanan duniya raguwa takeyi, amma hakan be ta6a damunta ba, dan tasan chewar shayarwa ba abu bane me sauqi bare shayarda yan biyu, musamman ma yanda kulu (sunan da suke kiran hauwa dashi kenan) takeda kukan tsiya, dan tsaf saita kwana tana kuka, bata ta6a barinta tayi bacchi, tasan ko hakan baxe barta tayi qiba ba......
Arziqinta d'aya yanda yan gidan suke tattalata, dan dazarar sunji ta fara kuka zasuzo su d'auketa, to kwana biyun nan nerh se ahankali saboda yaran gidan sunje Abuja, amma yaune daman zasu dawo, harta matsu su dawo dan ba qaramun takura tashiga ba rashinsu, gashi haiydar sam baya ganin kukan yarinyar, ita shukuriyya har so takeyi yagwada tafiya da yarinyar ya kwana, dan tanan nerh ze fahimchi abunda take fad'a, dazarar ta fara complain se yache ta chika zuzuta abune, hakanan dai zata gyaleshi ta bar mishi musun.....
Ranar bayan sun gama chin dinner abiii yache su shirya ranar Monday zasu wuche Egypt gaba d'ayansu, suje suyi hutu kowa yayi freshing mind d'inshi saisu dawo, sannan yanaso dakanan shukuriyya taqara ganin doctor d'inta, everyone was happy especially su usiii, they have never been their before not even once, godiya sukayita ma abiii for the visa, he always suprise them and it's always amazing, and this time trip din will be like never before, godiya sukayita mishi kafin kowa yanufi wurinshi.....
Tun ranar masu zumud'in chikinsu suka fara had'a kaya, usiii, biily nd co, basu ta6a having general family trip ba, saidai suyi da ummi kawai, but these one include the whole family, ga haiydar ga shukuriyya wanda basu ta6a having trip dasu ba, ga kuma new alert dinsu wato twins, this is so real......
Saturday morning abiii yakira mashkur yasanar dashi gameda trip din nasu, mashkur ba qaramun farinchiki yayi ba, he wish he could join them, be gama fad'a ah zuchiyanshi bah abiii yache
"I'll like you to join us if you're less busy"
Aiko kamar mashkur yayi tsalle dan murna"Abiii am not busy anymore I'll come with you, zanzo ranar lahadi da yamma inshaAllah"
Chikeda murnar amsa tayinsa abiii yache
"Nagode mashkur! We will be expecting you"Da haka sukayi sallama, mashkur was so excited which makes him not to calm down...
Umma da Abba mashkur yaje ya sanar wada tafiyan, fatan alkairi suka musu tareda addu'ar Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya, ranar lahadi tun safe mashkur ya had'a trolley d'inshi da yamma ya wuche Kano.....
Isarshi Kano sai ya tarar duk sunfishi zaquwa da murna, it seems like everyone is excited, haka suka mishi sannu da zuwa, usiii yakai mishi kayanshi sannan suka wuche masallachi dan anfara kiran maghriba, sai bayan sun dawo sannan yaje yachi abinchi awurin ummi, zuwa yayi ya gaisheda goggo sukasha hira kafin ya wuche wurin shukuriyya dake parlourn Nene azaune.....
Sun d'an dad'e suna hira awurin dukda chewar rabin hirar rarrashin kulu nerh, yarinyar tachika hayaniya da yawa, idan tana wuri bata barin kowa yaji gari, tunda mashkur yazo yazauna ya ansheta amma haryanxu batayi Shiru ba, hakan yana matuqar qona ran shukuriyya sosai, ga yayanta nan ah kwanche yana wasansa and that is something she will never do, tayi narana tayi na dare ko gajiya batayi, idan har tanasan yin bacchi saidai takaita wurin Nene ta kwana, she wish she should stop this, dan ko yarinyar bata kuka haka zataji kukan yarinyar yana mata gizo, idan kuwa tayi bacchi har mafarkin kukan yarinyar takeyi, this is too much for her......"Kulu tafiya kuka ya mashkur"
Ta fad'a tana yatsina fuska"Lafiya che ai"
Yafad'a yanawa kulu wasa, shi har yanzu kukan yarinyar be damunshi kamar yanda shukuriyya take zuzutawa, Itakuwa shukuriyya jin ya fad'i haka yasa tayi ajiyar zuchiya takoma ta jingina da kukera, dakashi se haiydar nerh kad'ai mazan data sani ah rayuwarta wad'anda kukan yara baya damunsu..."So how's your health?"
Mashkur ya tambaya"Feeling better Alhamdulillah"
"Bakya jin wani chiwo?"
"No! Not at all, ko ina bemun chiwo, amma naji abiii yache kafin mu dawo zanga doctor achan".....
" but just for check up"
Tayi saurin fad'a dan yanda taga mashkur ya d'ago alaman zeyi magana....Dariya sukayi dukansu, usiii da mienal nerh suka shigo suka samesu, nan suka zauna aka bud'e wani sabon shafin hiran, suna zaune ma haiydar yazo yayi joining dinsu, sun dad'e suna hira saida sukaga dare yayi sosai sannan suka nufi makwanchin su.......
Keep voting and commenting
MEERAH
