51

968 68 4
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳




Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘






5⃣1⃣



                
                    
          Wuraren 8 na safe na hango shukuriyya ta kintsa chikin doguwar raigan less, tasha d'aurinta me kyau, ga kwalliyan datayi ya ansa skin d'inta, although it was light as usual, amma still yayi fitting nata kamar kullum, tana gama gyara kanta ta feshe ko ina ah jikinta da turare sannan tafito parlour, tana fitowa taje tanemi wuri ta zauna ah d'aya daga chikin kujerun dasuke parlourn, she was thinking of had'a musu breakfast amma sam yanda takejin jikinta baxata iyabah, shex totally exhausted, sai kawai tayi zamanta awurin tana tunanin abubuwa chikin ranta......

     Bata dad'e wurinba saiga haiydar yafito daga d'ayan dakin dake parlourn, wanda yaxama na haiydar nerh, bcoux anan aka ajje mishi komi nashi, yana sanyeda shadda me kyau ruwan madara, he luks so cute.......

  Kallo d'aya tayi mishi ta sunkuyarda kanta saboda yanda takejin wata kunyarshi achikin zuchiyarta, shikuwa haiydar d'an dariya yayi ganin reaction d'in nata sannan yaqarasa kujerar datake kai ya zauna

     "Ina kwana amarya"
Haiydar yafurta yana riqo hannayenta, Shiru tayi takasa ansawa yayinda shikuma yafara wasa da hannayen nata, saboda yanda sukasha lalle sai hannun yaxama wani daban abun sha'awa....

   "Ina kwana"
Tafurta ahankali, dariya yanda tayi d'in yabashi amma saiya fuske kawai ya ansa,,,,

     "Kinyi kyau sosai"
Yafad'a yana d'ago ha6anta, meaning that yanason ganin face d'in nata sosai

   "Nagode"
Tafad'a tana murmushi still bata bari sun had'a idon bah

"Shukuriyya ki kalla idona mana,, ummnn,,"

Shiru tamishi bata d'ago d'in bah yayinda yachigaba da wasa da fingers d'in nata, hira ya farayi mata me dadi yana qara nuna godiyarshi agareta, chikin hikima da dabara yaketa gode mata yayinda idanunshi suke kallan fingers d'insu dasuke sarqe wuri d'aya, jikinshi har yafara sanyi saboda abunda ya tuna, hakan yasa yanayinshi yafara chanjawa,,,,

    Itakuwa shukuriyya tunda yafara magana ta qura mishi ido tana kallanshi, ba komai take fahimta ba ma gameda abunda yake fad'a, kawai kallnshi takeyi kaman yau tafara ganinshi, sai yauma take qara ganin kyawun haiydar afili, qurawa tawadar Allah d'inshi ido tayi, gatanan guda uku ajere ah right side d'inshi, baqaramun kyau take qarawa fuskanshi bah,,, ta shagala da kallanshi bata sani bah ma, sai gani kawai tayi yana waving nata, ad'an tsorache taja baya, saikuma tarufe fuskarta tana dariya, knowing that yariga ya kamata tana kallanshi, dariyar yayi shima sannan yache

"Na kamaki ae"

Qin bud'e fuskan tayi saima d'aura fuskan datayi akan kujerar datake kai,,, dariya yayi kafin ya miqe yache bari yaje ya nema musu abunda zasuyi karin kumallo dashi.

Yana tashi sukaji ana knocking gate ta waje, so sai yayi saurin futa dan ganin ko waye, yana bud'ewa yaga haniff nerh da kwandon abinchi ahannunshi, gaisheshi yayi ya ansa yana mishi dariya sannan suka shigo, dafarko ma qin shigowa yayi yache anche karya dad'e, saida haiydar yad'anyi insisting sannan ya shigo....

     Shukuriyya na zaune ah parlour taga haniff yashigo, ahankali tad'an miqe shikuma yaqaraso wurinta da sauri sukayi hugging d'in juna, sakinta yayi sannan ya ajjemusu breakfast d'in yache aiken umma nerh, sannan yafad'a mata chewan mutanen KT xasuxo anjima, umma tache karta dafa komai xa'a kawo musu abinchi, toh kawai tache mishi sannan yache xe tafi, haka suka rakashi har gate sannan suka dawo tana me kewar 'yan'uwanta,,,,

   Suna shigowa taje tayi serving nasu abinchin sukachi sannan ta kwashe komai takai kitchen, tsaftachesu tayi tas yayinda haiydar yake gefenta yake tayata, sai wani tattalinta yakeyi kamar kwai, yama kasa bata space kona seconds nerh tad'an huta....

Suna gamawa suka fito parlour suka zauna suna hutawa, ga TV sun kunna dukda daman bawani kalln sukeyi bah, hira kawai haiydar ke mata yana d'ebe mata kewa, anjima kad'an suka fara baqi, y'an uwa da abokan ariziqi aka fara zuwa ganin gidan amarya, daman already ankwota da garar ta, so saitayita d'ebo musu kayan zaqin tana had'awa da lemo da ruwa,,,

Wasu na fita wasu na shigowa, haka baqi sukayita musu chinchirindo achikin gidan, danma umma ta aiko musu da abinchi dayawa, amma zirga-zirga daga parlour zuwa kitchen baqaramun gajiya tayi bah,,,,

   Gashi haiydar baya barinta tayi minti goma da baqi saiya fara kiranta a wayarta, yana d'aki abunshi yaqi fita, kuma idan taje ba wani abu me mahimmanchi bane, saidai yafad'i shirmenshi kawai yache taje shikenan, its just that yanata missing nata nerh akusa da shi ah iya minutes d'in,,, shi ya matsu ma baqin suyi su koma inda suka fito dan ya gaji da jin hayaniyarsu,,,

  Haka akayita baqi harzuwa dare kafin suka samu kansu agidan, haiydar nafita sallar maghriba ta tsaftache ko ina da yara sukad'an 6ata sannan taje wanka itama, bayan tagama tayi sallah ta qara zuba kwalliyarta sannan haiydar yashigo gidan,,,
Haka ya zauna yaita zuba mata soyayyarshi,,, yanata zuba mata promises iri-iri, na qarya Dana gaskiya, dan surely wasu alqawarin dakaji kasan na zumud'in amarya nerh kawai, itakuwa sai jin dad'in kalaman nasa take, ahaka har suka nufi makwanchinsu.

                       🌳🌺😘








*MEERAH*

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now