64

950 68 4
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*

6⃣4⃣

               

          Isarsu Abuja suka nufi masaukinsu wato gidan da hamza yake chiki kenan, bayan sun huta hamza yafita yamusu order sannan yadawo da kaya niqi-niqi, chikin farinchiki da murna suke chin abinchin su, humairah kam baxata iya tuna when last take chikin farin chiki hakaba, ahakan ma jinta takeyi kaman ta janyo gobe tazo, danfah ta matsu ta ganta ah London bcoux upto now she can't believe shex going there, hirarsu sukeyi sosai chikin jin dad'i har dare yayi kowa ya nufi makwanchin shi.

     Washegari early 6am suka nufi airport domin kai humairah dan jirginsu na safe nerh, bayan isarsu sun zauna for like 20minutes kafin aka fara kiransu, duk zaman dasukeyi hira kawai takeyi da mashkur, shi kuwa hamza kallanta kawai yakeyi yana tunanin yanda zeyi missing sisternshi, saboda zamanta kusada shi baqaramun dad'i yakeji bah, amma idan ya tuna dole wataran zatayi aure ta barshi sai yaji ranshi yayi mishi sanyi, har yakejin gara ma ta tafi yanxu d'in, sai ya koyi rashinta akusada shi.

shex eager to leave the country amma ko kad'an batasan tafiya tabar mashkur, dan tasan dole kafin tadawo ma yayi aurenshi, haryanxu soyayyarshi yana dawainiya da zuchiyarta, kallanshi kawai takeyi chikin ido tana mishi magana, irin yanayin maganar da bata tab'a yimishi bah, shikanshi he feels uncomfortable da yanda take kallan qwayar idonshi, hakan yasa ya d'auke nashi idon daga nata dan azahiri har kunyar hakan yafara ji,,,,,

   Anfara kiransun kenan suka miqe, lokachinne ma sukayi waya da yan gidansu, harda shukuriyya saidata kirata, tamata fatan sauka lafiya da zummar chewan tana zuwa zata siya sim ta kirasu, suna gama wayar ta chireshi ah kunnenta sannan tayi switching nashi off kafin ta d'ago ta kalli mashkur wanda ke tabin movement d'inta, suna had'a ido ya sunkuyarda kanshi yana qoqarin pressing phone nashi, murmushi tayi wanda ke d'aukeda kuka, ganin tayi murmushin yasa ya d'ago ya kalleta sai shima ya mayar mata, daidai lokachin da hawaye ke zubowa ah idanunta, qoqarin magana yakeyi amma kafin yache komai hamza yaqarasu wurinsu yana chewa

   "Let's go humairah, ure ready to leave"
Basuche komai ba sukabi bayanshi, suna zuwa edd line din humairah ta juyo tayi hugging hamza sannan ta fashe da kuka, ah few seconds din taji batasan tayi tafiyar, jinta takeyi kaman ta koma gida kawai, rarrashinta yayi agurguje sannan sukayi sallama, juyowa tayi ta kalli mashkur idanunta na zubarda hawaye, so takeyi ta mishi magana amma takasa chewa komai, shima kuma yanaso yamata magana amma yanayinta yasa yakasa, ganin baxasuyi wa juna magana bah yasa hamza yayi amfanida hannushi wurin juyarda humairah ta kalli hanyar daxata bi sannan yad'an turata da wasa alamar ta tafi kawai, babu musu tasa kanta ah hanyar tafara tafiya batareda ta juyo bah, haka tayi making mind d'inta chewan ko juyowa baxayi ta kallesu bah, tayi nisa da tafiyarta harta fara 6achewa ganinsu, hakanan taji bazata iya qin juyawa bah, tanaso ta kalli kyakkyawan fuskar mashkur akaro na qarshe kafin ta tafi, hakan yasa ta juyoda fuskarta, tana juyowa taga hamza nerh kad'ai ah tsaye awurin, yana ganin ta juyo ya d'aga mata hannu, waving nashi back tayi tana wulqila idanta tana neman mashkur, kafin Allah yasa ta hangoshi ah left side d'in hamza ya juya mata baya, jitayi aranta inama ya juyo amma be juyoba har takama hanya ta tafi abunta,,,,,,
After some minutes jirginsu yatashi yakama hanyar London.....

   Komawa sukayi gidan hamza chikeda alhinin rabuwa da humairah, kwanansu d'aya ah chan mashkur yadawo Kaduna yabar hamza achan tunda daman shi achan yake aiki.....

                          🌳🌺😘

        Isar haiydar gida baqaramun farinchiki yayi ganin shukuriyya achan bah, yana shigowa itama ta tashi dukda dai jikin babu qarfi sosai amma taqarasa tamishi welcm bck hug sannan suka shigo chikin gidan, banda tambayarta lafiyarta babu abunda yakeyi, chikeda zumudi take bashi ansa, dan sosai take hamdala ga ubangiji abisa ni'imar lafiya daya mata, dan ita kanta ta tsorata da yanayin laulayin nata ainun.

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now