12

1.6K 109 7
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳


Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*  😘


1⃣2⃣

              

   "Meye dalilinki? iyye shukuriyya!" Umma ta buga mata tsawa
‘daman.….. uhm"
ta fara tunanin ta ina zata fara,
"dama me? Kaji yarinyar banza"
umma ta fada a hasale.
"dan Allah Umma kiyii haquri wallahi nakasa gane kaina ne"
ta fada murya na rawa alamun kuka zae taho mata....
  Sosae umma taji tausayin diyar tata tace
"na jinki shukuriyya, ki fad'amun matsalarki, meye amfanin uwa idan bata kula da yaranta ba"
Fashewa da kuka shukuriyya tayi dan abunda take jira kenan tasamu kuka a lokacin
"Kinyi shiru ki fadamun mana ya isa kukan"
cewar umma
"wallahi umma inason kamal, amman dalilina umma shine an cuceni, an tarwatsa mun rayuwa an gama dani, anci mutunci na, an yagan rigar mutunci, an keta mun haddi, anci zarafi na, an tafi mun da daraja tah ta ‘ya mace an mun fyade, an tafu mun da BUDURCI na, wace daraja nake da ita a idon kamal da tayi saura, da me naxo masa dashi na farin ciki, umm…….."
ae bata qarasa ba sai ta fashe da matsanancin kuka,,, Umma da jikinta ya gama yin sanyi jawo diyar tata tayi jikinta tana me lallashi, tana jin kamar tayi kukan itama, qwalla taf idonta, Amman baza tayi kuka ba, idan tayi zata karyar mata da zuciya, abun zae mata yawa.... Sai da tayi mae isarta tana lallashinta sannan ta numfasa tace
   "Shukuriyya!!! ki daina kuka Allah yana nan, kowa da tasa JARRABAR, haka taki *QADDARAR* take bamu da ikon sauyata, bakomae, Ni nasani an cutar dake har damu duka, Amman haquri shine komae, abun da nakeso dake shine wannan abun yawuce ah ranki dan Allah, kamal da kike gani baki da wani masoyi bayanshi, da baya sonki ba zai soma auranki ba, su wadanda kike gani suna qyamar mutane irinku, da kamal irinsu ne ba zai aureki ba, gudunki zai yi, saidae ki zama abar tsokana abun dariya a gunsa, amman kinga idan kika dage da yi masa biyayya kina kyautata masa kin gama masa komae, zai ga darajarki fiye da da, ki farantawa mijinki ki masa biyayya ba ruwanki da tuna baya, abunda ya faru ya riga ya faru saidae a tinkari gaba"
  Daga nan dai ta mata nasiha akan zaman aure da hukuncin mae bata ran miji, sosae ta tunasar da ita akan komae tana mae mata nasiha akan taji tsoron Allah, saida suka shafe at least 30minutes, jikin shukuriyya duk yayi sanyi tsoran Allah ya dad'a shigar ta a hankali ta bud'e baki tace
"umma kiyi haquri inshaAllahu zan gyara, nagode, hakan baza ta sake faruwa ba"
Dadi sosae umma taji har ranta tana mae godewa Allah da samun d'iya irinta tace
‘Allah yayi miki albarka shukuriyya haka nake son ji"
tana fadin hka suka ji horn, umman ta kalleta
‘kinga mashkur nan har yaxo.’
Shukuriyya ta marairaice
"daman umma ba dare zaki kai ba?"

  ‘ke kinci gidanku dare zan kai gidan d'iyata in ba so kike duniya ta zagen ba.’
‘toh umma mu ina ruwanmu da duniyar suyita yi mana, mutane ai basu rasa abun fad'a akan ka, kinga fa ko abinchi baki ci ba ko ruwa.’ shukriyya ta fada kamar zatayi kuka, umma tache
"abinchin da surukina yadafa kikeso nazauna nachinye kenan"
tafada tana dariya, itama dariyar tayi hade da rufe fuskarta, kafin su ida tuni har mashkur ya shigo da sallama, suka amsa shi, ya samu gu ya zauna suna gaisawa da shukuriyya yana mata ya gida da mae gida, suka gaisa cikin fara'a ta tashi ta d'ebo masu drinks sai anan umma itama ta zuba mata mai d'an sanyi ta jiqa bakinta itama.
  Sun d'anyi fira kadan suka tashi zasu tafi haka ba ah son ran shukriyya ba suka tafi. Umma tana tunasar da ita tayi aiki da abunda ta fada mata zata dace duniya da lahira, a haka ta rakasu suka wuce, ta koma ciki jiki a sanyaye........

  Zama tayi tana nazari gskiya bata kyauta ba, tashi tayi ta d'aura d'amarar gyara, haka ta shiga aiki ba ji ba gani, saida ta gyara gidan ko ina tsaf, tasa turare ko ina sae qamshi yake, sannan ta shiga wanka, kasancewar abnchin da kamal ya dafa na nan bata dora komae ba dan komae na nan ydda yake, tana fito wa ta shirya cikin riga da skirt na atampha purple n yellow tayi kwalliyarta ssae tayi kyau sae qamshi take, ta dawo parlour ta zauna tana dan duba wayarta....

  Horn taji alamun kamal ya dawo ta rasa ya zatayi, rashin sabo, sae tunani take tana ta addu'a a zuciyar ta Allah taimake ta, tashi tsaye tayi ta tsaya bakin qofa tana jiransa.
  Shi kuwa yana doso wajen wani qamshi ya daki hancinsa yana d'aga ido yaga parlour sae walwali yake ga qamshi bae lura da ita ba, sai ji yayi tace
" sannu da dawowa, ya hanya?"
  Ae kamal daskarewa yayi a gurin kawae yana qare mata kallo………
      
  

*MEERAH*

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now