37

1.3K 68 2
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳




Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘




3⃣7⃣

   
                     

Isar nene katsina ba qaramun jin dadin ganinta yayanta yayiba domin yana matuqar jin yar'uwar tashi achikin zuchiyarshi saboda su biyu nerh awurin mahaifiyarsu sai kuma step sisters da suke dashi, tun kafin taxo aketa zumud'in zuwanta don daman ta kirashi ta sanar dashi zuwannata, matanshi ma sai murnar ganinta sukeyi da kuma tilon d'anta haiydar, ga kuma farinchikin ganinta dasukayi d'aukeda chiki achikin jikinta....

Bayan sun gama chin abinchin rana matan yayanta suka tashi suka nufi wurinsu yayinda sukabar nene da yayan nata domin su zanta, zama sukayi suna hira irinta Yaya da qanwarshi, yana kuma jin ko akwai wata matsala achikin gidan nata, nan ta sanardashi chewar babu komi tana zaune lfy da kowa, don daman da kunya ai tafadi rashin mutunchi datake shukawa agidan mijin nata, shikuma baxe san komaiba fache abunda aka sanar dashi, to ba'a fad'a mishi bah, hakan tasa ya fahimchi tana chikin kwanchiyar hankali da jin dadi ah gidan mijinta.....

Haiydar kuwa yana chan compound d'in gidan sunata wasa da yaran gidan, sai wasa sukeyimishi na murnar ganinshi da kuma zumud'i, gashi daman su ba qananan yara nerh dasu bah, duk yaran gidan sun d'an fara girma coux babu age mate din haiydar, hakan yasa suke farinchikin ganin haiydar agidansu har sukejin inama nene tabar musu shi idan zata tafi, don haiydar akwai shiga rai matuqa, shikuma yana chikin farin chiki yaudin, banda dariya babu abunda yakeyi saboda yasamu abokanan wasa, tundashi daman shikadai yake rayuwa achikin gidansu, hakan yasa yau yakejin kamar yaxama 'yantacche.

jefi-jefi nene tana hango wulgawarshi ah tsakar gidan da kuma yanda yake dariya, hakan yasa ta zuba mishi ido tana kallanshi, sai takejinshi har chikin zuchiyarta, tanajin rashin kyautatawarta abusa abubuwa dayawa data aikata mishi, itada kanta tasan bata kyautaba kuma baxata iya fitarda kwakwaran dalili abisa abunda tayi d'inbah.
ahaka yaran suka chigaba da wasa har yamma sannan suka janyo hannun haiydar suka shigo chikin gida, don daman yaudin Friday nerh, so basa zuwa islamiyya hakan yasa suka samu lokachi me yawa na wasa.....


                       🌳🌺😘

Ah kano kuwa chikin jimamin abinda nene ta aikata na chin mutunchi kowa yakeyi, although bayau tafara bah amma nayau din harda izgilanchi da chin mutunchi tayishi, dadin abun d'ayane ummi na d'aukeda tsohon chiki if not ita kanta tayi imanin da yau sai nene tasakata zubar da hawayen rashin haihuwa,,,,,,

Bayan fitar Nene daka gidan abuu yaja d'an uwanshi suka nufi site d'in mahaifiyarsu dan yafahimchi yana chikin damuwa nerh, itama kuma goggo tabi bayansu, yarage saura ummi kawai awurin, itama ganin haka yasa taja qafarta tanufi site d'inta.

tunda tashiga takejin chiwo ajikinta, abu kamar wasa yafara mata daga baya chiwo yaqara qarfi wanda yasa tafara tunanin ko naquda nerh, amma hakanan tadunga daurewa tana chije labbanta har saida abu ya tsananta tayarda takasa controlng, kamar daga sama Allah ya hankad'o mata goggo, don tunda chikinta ya tsufa daman goggo bata barinta ta zauna na tsahon mintuna ita kad'ai fache tana gefenta, tana shigowa taganta tana naquda, don haka tayi saurin qarasawa inda take, da fari tayi niyyar zuwa ta kira abuu azo atafi asibiti, amma saita fahimchi naqudan gadan-gadan yataho ma ummi, don haka sai kawai tajira domin suga haihuwar tata, bayan gajeriyar naquda da ummi tayi Allah ya sauketa lafiya ta haifi santalelen danta namiji shima jawur dashi......


🌳🌺😘

_*some hours later*_

Bayan ummi ta kintsa kanta ta fito tsaf da ita, ga kuma babynta nan shima an shirya shi chikin towel dinshi yana hannun uncle dinshi wato abiii, sai murnar samun qaruwa sukeyi, bakin abuu kuwa yaqi rufuwa ko kad'an dazarar ya d'aqa idonshi nuurul qalbin shi kawai yake hangowa,,

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now