63

964 72 11
                                    

 🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*


6⃣3⃣

                  

         Haiydar ko bayan zuwanshi gida ya kasa bacchi gaba d'aya, yanda yake jinshi ma da jikin shukuriyya se yakejin dama ah zubar da chikin kowa ya huta, dan sosai laulayin nata ke bashi tsoro, kullum yanayin jikinnata qaruwa yakeyi, yaudata kasanche bata kusada shi ko bacchi kasawa yayi, haka ya kwana yana kaikoma achikin gidan.....

      Dasafe tun wuri yakama hanyar gidansu shukuriyya, bayan ya gaisa da iyayenta ya nufi d'akin datake, shiganshi yayi daidai da amayar da wani koren ruwa datakeyi, kaman irin tasha maganin malaria dinnan, dasauri yaqarasa ya tallafota dukda daman hanifah tana kusada ita, sannu yashiga jera mata har tagama aman sannan ya mayar da ita kan gadon ya kwantar dan ko zama bata iya yi sosai yanzu saboda yanda jikinta yake mata, kallan hanifah yayi sannan yache
   "Hanifah ya me jiki?"

  "Wallahi yaya babu sauqi, jiya ma batayi bacchi bah fah"
Hanifah tayi maganan kaman zatayi kuka

Shiru yayi for some seconds yana kallan shukuriyya sannan hanifah ta tashi tabar d'akin, banda gumi babu abunda shukuriyya takeyi saika rantse da Allah naquda takeyi, handkerchief yasaka yadunga goge mata zufar yana mata fifita, shidai wannan laulayin bemishi dad'i bah ko kad'an

  *5weeks  later*

Duk wannan weeks d'in chikin rashin lafiya shukuriyya tayishi, wani lokachin ma batasanin inda kanta yake, amma haka tayita jurewa tana fama, akwai ranar da abun ya ishi haiydar dayaje gidan se kawai ya kawomata buqatar zubarda chikin,ah nufinshi indai hakan zesa tasamu lafiya, baqaramun tashin hankali tayi dashi bah hakan daya fad'a, dukda chewar bata iyayin magana amma haka tayita mishi harsaida yabar gidan, harda kukanta wai baya santa tunda bayasan dan chikinta, shikuma yafad'i hakanne dan nemar mata mafita, sboda ba qaramun wahala takeyi bah, hakan daya fad'a mah saidatayi wurin kwana biyu bata kulashi bah, ko gidan yazo saidai tayita juya mishi baya, sedaya dunga bata haquri sannan ta haqura,,,,,,,

   
     Yaud'in takasanche ranar lahadi, ranar nerh kuma umma tache shukuriyya zata koma gidan mijinta, tunda dai tad'anji qarfin jikinta babu laifi, tunda komai tana iyayi dakanta yanzu, tas akaje aka gyara mata gidanta aka karkade qura, dukda daman haiydar yana gidan, amma de gyaran namiji da mache ba daya bane, gyara sosai umma ta mata kamar wata amarya, even though ta rame sosai saboda jinyar datasha, mashkur nerh yasakata ah mota dakanshi yamayarda ita har gidan mijinta tareda humairah, lokachin ma haiydar yana kasuwa, yasan chewar yaud'in zata dawo amma beyi tunanin zasu kaita bane, tunda sunyi magana da shukuriyya chewan zaizo ya d'auketa sutafi tare,,,,,,

  Hakan yasa yana tashi daga kasuwa ya wuche gidansu, yana zuwa suka sanar dashi ai ankaita tundaxu, da farinchikinshi ya juya ya nufi gidanshi.......

                        🌳🌺😘

Ah wannan 5weeks dinda shukuriyya tayi agidansu tana jinya humairah ta dawo daga Adamawa, harsun fito ah camp, ah wani secondary skul akayi posting d'inta anan yola, dashike sunada hanya sai sukaje tareda hamza sukayi chuku-chuku suka siya service d'inta da kud'i masu kauri, tunda daman abune na hanya da kud'i, inkana dasu babu abunda baxa'a maka bah, bayan dawowarta kaduna shine taxo ta tarar da shukuriyya tana laulayin chiki agidansu, kusan tare sukayi laulayin dan kullum tana gidansu shukuriyya,,,  ko matsawa nesa da ita bata iyayi, ah kwanakin ma kullum agidansu shukuriyya take kwana tana kula da lafiyarta, hakan yaqara kawo musu shaquwa ah tsakaninsu me qarfi, tunda daman sun kwana biyu basuyi irin wannan zaman bah.

    Ah kwanakinne abokin hamza wanda yake Santa yafito da qarfinshi kan maganar aurenta, amma fafur taqishi tache bata sanshi, babu yanda ba'ayi da itaba amma tache bataso ita karatu zata chigaba, har requesting yayi chewar zaijirata tayi karatun tagama, tunda masters bawani dad'ewa bane zata gama ta dawo, amma ta nuna mishi itafah kota gama bawai aurenshi zatayi bah danhaka ya haqura ya tafi kawai,,,,,

dukda yanayin rashin lafiya da shukuriyya take amma saidatayi qoqarin nunawa humairah aure ah wannan lokachin shiyafi dachewa da ita, tunda dai tayi karatun sannan ta samu mijin dake santa tsakani da Allah gara tayi aurenta kawai, amma ta nuna mata ita ba aurene agabanta bah, tanada unfulfilled promises d'in datayiwa kanta wanda ya kamata tayi fulfilling wanda shine karatunta, dazarar ta gama zatayi aurenta ah wannan lokachin,,,,,

Shukuriyya taso ta fahimtar da ita chewar zata iyayin karatunta agidanta, amma humairah ta kafa mata hujja da ita kanta, la'akari da laulayin da takeyi, hakan yasa tache mata yau da ache karatu kikeyi tayaya zaki iya chigaba dayinshi ah wannan halin laulayin da kike chiki, kinga kuwa sam aure da karatu ba abu bane meyuwa, dole d'aya yana dakatar da d'ayane, da wannan taqara kafa hujjarta.....

Duk abunda shukuriyya zata fad'a sai humairah tayi criticizing, daga qarshe ganin batada yanda zatayi humairah ta riga ta kafe akan bakanta yasa ta haqura ta qyaleta tareda yi mata fatan alkairi.

    Ah week d'inda shukuriyya ta chika five weeks agidansu ah week d'in nerh hamza yakawowa humairah scholarship d'inta, tunda daman ah tet fund yake aiki, sai yayi duk yanda zeyi aka sakata ah first class scholars of the year, wad'anda ake ba scholarship kenan daga wannan fund d'in, she's very lucky saboda London aka turata, haka suka dunga zarya from Kaduna to Abuja har Allah yasa suka kamalla komai sannan fah tazo tayiwa su shukuriyya sallama,,,,

     Shukuriyya tanata alhinin rabuwarsu, tunda wannan karan London ta nufa ba kamar da chan datake ah hostel bah, ranar dazata wuche abuja ranar nerh yakama shukuriyya zata koma gidan mijinta, dan haka tareda humairah suka maida ita gidan nata, sunsha kuka kamar babu gobe, irin kukan rabuwarda basu ta6ayi ba tunda suke, tunda daman tun tasowarsu daga yarinta babu wani chikinsu daya tab'a yin nisa haka, hasalima basu tab'a nisada juna ba sai bayan shukuriyya tayi aure, saikuma lokachin data koma KT, amma tun bayan wannan lokachin kullum suna manne da juna,,,,,,

Har lokachin da suka kawota gidanta bayan mashkur ya fita ya basu guri shukuriyya tanaso tayi convincing humairah chewar tafasa tafiyar, tadawo tayi zamanta tareda danginta tayi aure, ah lokachin ma abun dariya humairah tamayarda shukuriyya, saboda ayanda takejinta babu wani dalili dazaisa tafasa amfanida wannan opportunity d'in, dan tun tana yarinya yana daga chikin mafarkinta tabar Nigeria ta tafi wata qasar karatu, amma ah wanchan lokachin bata zafafa burinta bah, mafarkinta koda Sudan nerh ta tafi, amma gashi Allah yabata damar zuwa har London, bazata tab'a barin wannan damar bah,,,,,,,,

Shukuriyya dai kallanta kawai takeyi, so takeyi tayi figuring out irin yarinyar datake chin humairah haryanxu, inba yarintaba yaushe zata tafi wata qasar yin masters batareda aurenta bah, bayan gashi Allah ya kawomata miji kuma nagartacche, kallanta taqarayi ido chikin ido sannan tache

    "Humairah nakasa sanin abunda yake chin zuchiyarki, dafarko da muka taso ba haka kike bah, bakida burin daya wuche kigama secondary kiyi aure, narasa yanda akayi burinkin yachanja"

"Hmmnn,,, shukuriyya kenan, yanda kike tunani ba haka bane, ko ah wanchan lokachin fad'a kawai nakeyi ah baki, amma ba abunda yake chikin zuchiyata kenan bah, tun wanchan lokachin akwai burin hakan araina, nabarshi nerh kawai as my privacy, sai kuma Allah yasa burikan nawa sukayita yin gaba"

"Allah ya kyauta yakuma baki sa'a"
Chewan shukuriyya

   "Amen"
Humairah tafad'a chikeda fara'ah

Hirar duniya suka chigaba dayi shukuriyya tanata alhinin tafiyar humairah, har mashkur yashigo yache humairah ta taho su tafi, sannan ta tashi suka tafi gida, suna komawa ko 1hour basuyi bah suka kama hanyar Abuja, mashkur, hamza da humairah,,,,
dan mashkur chewa yayi har airpot ze rakata seyaga tafiyarta London sannan ze dawo.......

                   🌳🌺😘

     _*humairah zata tafi London fah😭 don't leave us please,,,, mashkur do somtin mana*_

   _*welcm back shukuriyya, Allah sa qarshen wahalar kenan*_

_*agurguje*_

One lurv fans❤




*MEERAH*

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now