97:

880 86 2
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳



Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH


9⃣7⃣


         Parlourn goggo chikeda yan gida sai rige-rigen d'aukar jarirai akeyi, abun seems unbelievable to them, batayi kamada wadda xata haihu ba sanda suka barta amma ache ta haihu, banda chewan basuga chiki ajikinta ba saisuche ba babynta bane, sunyi matuqar farinchiki na ganin first grandchildren na gidan, shukuriyya na gefe azaune kawai tana musu murmushin qarfin hali, da alama dae har yanxu tanajin rad'ad'in haihuwar da tayi, goggo che tayi magana tache aje asanar wada masu aiki su d'aura sanwa sannan ah tsayar da ruwan wankan me jego, ummi che taje ta sanar dasu sannan aka fito da garwar wanka, sannan ta wuche kitchen d'inta ta dafawa shukuriyya ruwan tea ta had'a mata wasu fruits ah jug sannan tasa me aikinta ta dafa tuwan dawa wa me jego, achan kuma masu aiki sunfara had'a abinchin gida.....

     Achan 6angaren Nene shukuriyya taja suka tafi apartment d'inta dan ta lura da yanda take ta gyangyad'i, ganin bacchi takeji yasa tache tazo su tafi, sai suka bar musu jariran awurinsu kawai, suna zuwa basu dadeba ummi ta kawo mata ruwan tea, Zara che dake maqale kusada ita tana mata sannu taje ta hado mata ruwan tea din sannan ta kawo mata, ahankali take sipping tana d'anna chikinta, da alama hakan yana mata dadi, dan kafin ta gama harta ji ta warware,bayan ta gama da wasu mintuna aka kai mata ruwan wanka, baquwarsu me suna hinde wadda take yar uwar goggo che daka maboyin fulanin tarda, wadda akaje aka d'aukota takanas saboda wankan me jego, itache taja shukuriyya suka tafi ta wanketa tas, sundade ah toilet d'in kafin suka fito, suna fitowa shukuriyya tayi d'akin Nene tayi kwanchiyarta, ba yanda ummi batayi ba tabari tachi abinchi sannan ta kwanta amma Sam taqi, hasalima tana bawa ummi ansa idonta yana qara rufewa nerh, ganin hakan yasa ummi ta qyaleta tayi bacchin.....

     Daqyar aka kwache baby boy din daka hannun usiii, wanka za'ayi musu, tundaxu aka kar6i baby girl din amma shi yaqi bayarwa saida goggo ta mishi magana sannan ya yarda ya bayar, hanne sai zolayar shi take tana chewa Ashe haka yake da qulafuchin yara, shidai chemata yakeyi taje ta wankesu ta dawo masa dasu, sai dariya sukeyi ah parlourn, fuskarsu kawai zaka kalla kasan suna chikin tsananin farinchiki.....

      Mashkur kam tun daxu ya sanar wada su umma chewan shukuriyya ta sauka lafiya ta samu twins, umma ji tayi kamar tayi tsuntsuwa tazo taga lafiyar yarinyarta da kuma jikokinta, amma mashkur yache ta bari gobe zai dawo inyaso jibi saisuzo gaba d'aya, daqyar dai umma ta haqura akan hakan, tundaxu take kiran waya abawa shukuriyya suyi magana amma sai ache mata bacchi takeyi hakan yasa hankalinta ya kasa kwanchiya, dashike tasan yarinyar ba wata wadatacchiyar lafiya che da ita ba sai taketa saqe-saqe achikin zuchiyarta, negative tunanin kawai takeyi tana tunanin kamar bacchin bana lafiya bane bh, if not meze kawo bacchi ah wannan lokachin, daqyar dae ta kori shaidan daga zuchiyarta sannan tayi fatan alkairi agareta, bayan ta idar da sallar maghriba sosai tayi addu'ah akan Allah ya raya shukuriyya da abunda ta haifa sannan ya qareta da lafiya da tashon rai me amfani.....

       Ba umma ko Abba kadai ba, har ummi da Nene da siblings d'in shukuriyya addu'ar da sukayi kenan bayan sun idarda sallah, addu'ah kowa yake mata, shukuriyya ta chika yar gata lol.

     Daf da maghriba ta farka hakan yasa ba'ayi mata wanka ba, adaddafe dai tana zaune tana San jiki saida takai issha azaune bata motsa ba, anan tachi tuwo da aka dafa mata sannan ta had'a da wani farfesun kaji,  sai madara data had'a tasha, ahakan ma zaman da takeyi ummi take jira ta kawo mata wasu kayan chiki tachi (trust her to do something like dis) shukuriyya qauna che me qarfi tsakaninta da abinchi, bata ta6a wasa da hakan, ummi che tache mata taje tayi wanka kafin kayan chikin ya qarasa, daqyar ta miqe har hanne tana tsokananta tana chewa Allah dai yasa kar ayi qazamar me jego, shukuriyya na dariya ta wuche toilet, dayake dare yayi sai aka zuba mata ruwan zafin akache kawai taje tayi wankan da kanta ta gasa jikinta base anyi mata ba, hakanan ta shiga ta zauna ah toilet ta dunga wankan da towel tana manna shi ajikinta, da kanta ta dunga yiwa kanta izaya, amma sosai taji dad'in wankan, harma taji tafijin dadi da qarfin jiki ynxu akan daxu da hanne tayi mata, ita hanne da ganye take mata kuma kamar ruwan baya ratsata nerh.....

     Tana fitowa babu kowa ah d'akin, ko daxun ma daga Nene sai ummi ke zirga-zirga sai kuma Zara dake zaune ah gefenta, zama tayi ah gefen gado tana jiran wani yazo ya kawo mata kayanta, Zara che ta shigo ta ganta azaune agefe tana takure jikinta da alama sanyin AC dayake d'akin nerh ya fara ratsata

    "shukuriyya ya haka?"
Zara ta fad'a tana kashe AC da fankan dayake d'akin, lokachi d'aya kuma ta bud'e Window daya dake d'akin tabar d'ayan ah kulle sannan ta janyo qofar toilet d'in

      "Thank you"
Shukuriyya ta fad'a with a cute smile

Murmushi Zara ta mata in return sannan ta 6ude wardrobe d'in dake d'akin da alama tana San d'auko wani abunne

    "Ammn Zara!"
Shukuriyya ta kirata

   'D'agowa tayi ta kalleta sannan tache
"Kina buqatan wani abunne?"

"Yeah! My clothes"

"Ohh! They're here! Am trying to pick them up"
Zara ta ansa tana janyowa shukuriyya wani armless doguwan riga daga wardrobe d'in sannan ta hado mata da wani belt wanda shukuriyya tabi da kallo, gefen gado ta ajje mata sannan tache

    "Kinasan wani abune?"

"Wait! Yaushe kayana ya dawo nan?"
Shukuriyya ta tambaya da mamaki, saboda taga duk wardrobe d'in kayanta nerh, on the other side kuma kayan babys nerh ko wanne gashinan ah kwalayenshi

    "Daxu"
Zara ta ansa in short

   Dariya kawai shukuriyya tayi sannan tache
"Meaning what?"

"You'll be staying here for 40days I think"

    "You think?"
Shukuriyya ta tambaya

   "Yeah! "

   "40days?"

   "Enhn"

Dariya kawai shukuriyya tayi sannan tache bari in shirya, har Zara tayi hanyar waje zata fita shukuriyya ta dakatar da ita

   "Zara! What's dis for?"
Ta tambaya tana d'aga belt din data gani awurin, yamata kamada belt na y'an wrestling amma shi wannan rubber nerh

    "Oh wait! You mean you've never seen it before?"

    "Like never!"
Shukuriyya ta ansa ta

    "Belt dinki nerh u tight it here everyday kafin ki saka kaya"
Zara ta fad'a tana nuna mata inda zata dunga d'aurawa wurin chikinta kenan

   "And why?"
Shukuriyya ta tambaya

   "Saboda tunbi mana, zesa wanda ya rage ya koma and baxakiyi tunbi ba, idan kika barshi bakya daurewa tunbi zakiyi wanda baki zata bah, and you'll not feel comfortable kema, kuma kinsan maza kuma ynxu basasan mache me tubi"

Tafad'a with wink sannan tabar d'akin tana dariya, dariya shukuriyya tayi tana girgiza kanta, how did she even know this, dariya tayi sosai sannan ta miqe ta shirya tasaka doguwan rigan ta fashe jikinta da duk turaren data gani akan mirror d'in, tanada wannan habit din tun tana gida, duk turaren data gani awuri idan tana shiryawa saita fesa, it sound childish lokachin amma har yanxu tanayi bata daina bah, it turns to be her habit...

ta gama shiryawa tsaf ta dauka belt din tamayar wardrobe, she's not ready to put this on, sannan ta koma ta zauna agefen gado tana tasbihi ga ubangiji, sannan ta qara gode mishi ah karo na babu adadi daya sauketa lafiya yakuma yi mata kyautar yara biyu alokachin d'aya, tana zaune anan nene ta shigo ta sameta, murmushi shukuriyya ta mata sannan tache "sannu da aiki Nene"

   "Sannu shukuriyya! Ya jikinki?"

   "Lafiya lau Alhmdulillah! Ba komi dayake damuna"

   "Allah ya qara afuwa"

   "Amin" suka ansa dukansu.

Kallanta Nene tayi kaman tanasan gane wani abun, ganin hakan yasa shukuriyya ta qara kallan kanta

   "Wai doguwan riga kika saka?"

    "Ehh"
Ta ansa ah taqaiche

    "Amma kinsan doguwar riga ba kayan me jego bane ba koh? Saboda shayarwa, yakamata ki ajjesu ah gefe for now umn!"

Murmushi kawai shukuriyya tayi me chikeda kunya



It's too short right? U manage it please
  


Meerah

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now