72: "who is he"

1.1K 91 5
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳


Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH



7⃣2⃣

                      🌳🌺😘


MORNING

          sungama yin breakfast suna zaune dukansu ah parlourn goggo, abuu nerh yache usii yaje ya kiramishi wannan baqon, babu 6ata lokachi usiii ya fiche daga parlourn yanufi boys quarters....

    Azaune yasamu mutumin akan sallaya yana lazumi, mutumin yana ganin usiii ya shigo d'akin ya miqe da sauri ya nufi inda yake

      "Yaro!! Se yau ka dawo? Ina mahaifinku yake? Se yaushe ze dawo?"

Shidai usiii tsayawa yayi kawai yana qarewa mutumin kallo, shi yanayin mutumin ma mamaki yake bashi idan ya aikata wasu abun

      "Yadawo y......"

Ko maganar be qarasa furtawa bah mutumin yayi saurin interrupting d'inshi ta hanyar chakumarsa kamar ze fad'ar dashi qasa

     "Yana ina? Ka kaini wurinshi yanxunnan"
Yafurta ah hargitse

     "Shi yachema ah kiraka ai"

Usiii yafad'a yana kwachewa daga kyakkyawan ruqon da mutumin yamishi, lokachi d'aya yana saisaita kwalar rigar shi wadda tasha chakuma

      "Muje!! Mutafi!! Yi sauri!!"
Mutumin Yafad'a yana bin hanyar qofah dan fichewa daka wurin, babu 6ata lokachi usiii ya bishi ah baya yana mamakin manufarsa.

     Parlourn goggo suka nufa tareda mutumin, suna zuwa usiii yamishi izinin shiga sannan suka shiga tare, akan kujera usiii ya zauna yayinda mutumin ya zauna agefen qafar abuu aqasa hawaye na zubo mishi

     "Kayafemin dan Allah, ka taimakeni ka gafartamun kona samu sassauchi arayuwata, na aikata maka babban laifi, laifi mafi girman zunubi, kadubi girman Allah ka yafemun"

Mutumin yafad'a yana hawaye yayinda yake riqeda qafar abuu kamar ze chire masa ita, mamaki nerh ya ishi kowa ah parlourn musamman ganin yanda mutumin yaketa kuka, shi abuu tsoro mutumin yabashi ma ganin yanda yariqe mishi kafa kamar zai chire masa, kallan fuskar mutumin ya tsaya yi sosai ko zai tunata amma yaga be ta6a ganin fuskar bah,,,,,,

    "Bawan Allah zauna nan"

Abuu Yafad'a yana nunawa mutumin gefen kujerar dayake zaune, dan sosai ya matsu mutumin yasakar mishi qafarshi saboda kyakkyawan ruqo yamasa

Qin tashi mutumin yayi saima chigaba da kukanshi dayayi yana qara qanqame qafar abuu

Bayanda basuyi mutumin yadaina kuka ba amma yaqi, saika rantse ma qara tunzurashi akeyi,, mamaki yachika kowa ah parlourn ganin yanda babban mutumi kamar wannan yake kuka da magiya haka

    "Shikenan bawan Allah kayi shiru, bansanka bah,, banta6a ganinka bah, mekamun haka dahar kake neman gafara tah?"
Abuu yayi maganar da mamaki sosai

Daqyar mutumin ya daidaita kukanshi kafin yache

    "Tabbas baka sanni ba, amma ni nasanka, dukda chewar sanin danayi maka na taqaitacchen lokachi nerh..."

Shiru mutumin ya numfasa yayin da kowa ya baza kunnenshi ah parlourn yana sauraranshi

"Shekaru ishirin baya 😭,, arugunga titin Katsina,,,, y'an fashi,,,, fashi da makami,,,, kwachen  yarinya,,,, harbinka aqafa,,, nine d'aya daga chikin wan......"

     Babu wanda be miqe tsaye achikin parlourn bah, kallan mamaki da gajen haquri sukeyiwa mutum, usiii nerh yanufi wurin mutumin ah sukwane ya chakumi wuyanshi ya miqar dashi tsaye yayinda ya shaqe mishi wuya,,, lokachi d'aya idanunshi sukayi jawur saboda furuchin mutumin, so yakeyi yamishi magana amma jiyakeyi kamar an tokare mishi maqwogaranshi,,,,

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now