🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳
Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH
8⃣5⃣
Ranar da suka dawo ranar gidan yaqara zama full home, haiydar duk hankalinshi yayi KT saboda ya qaqu yaje yaga inna yasanar da ita labarin danginshi, ranar dasuka dawo washegari yakama hanyar KT, dashi da abuu dakuma abiii sukaje, ummi da Nene ma sunso binsu saida basasan abunda zai sakasu suyi nisa da shukuriyya...
Sunje KT lafiya sannan sun sami su inna lafiya lau, sanar da su komai haiydar yayi, murna agurinsu ba'a chewa komai, chikin qanqanin lokachi malam yatafi wurin mai gari yasanar dashi wannan labarin, zuwa lokachin ma saiga su haiydar da abuu nan sun qaraso fadar mai gari, kowa awurin saida yayi farinchiki samun iyayenshi dayayi, alheri me d'unbin yawa abuu yayiwa mai gari saboda haiydar yasanar dasu duk alkairan dasuka mishi sannan yasanar dashi chewar shine ma yabayarda sadakin aurenshi,,, alherinda abuu yayiwa maigari saida ya girgiza kowa awurin, domin kud'i yabashi irin kud'inda be ta6a ganin irinshiba, sunyi godiya me matuqar gaske kafin suka koma gidansu haiydar d'in, abuu nerh yache su shirya kayansu sai suzo su tafi Kano tare domin su gana da sauran ahalin haiydar d'in, chikin qanqanin lokachi suka shirya kayansu sannan suka kama hanyar Kano,,,,,
abiii kuwa gidansu malam nerh yadunga mishi yawo akai da asalin d'akin haiydar na da kafin yayi aure, sosai yaqara tausayawa haiydar da irin rayuwar da qaddara tasaka shi achiki, tabbas yaran yagamu da rayuwa kala-kala.....Isarsu Kano tarba ta musamman suka samu achikin gidan hisham, yanda ake kaikomo agidan ma saika zata wani biki akeyi, inna da malam sakin baki kawai sukayi suna kallan tsantsar arziqi achikin gidan, yanxu Ashe wannan yaran daka irin wannan gidan yafito amma yake rayuwa tareda mu? tabbas banda Allah babu wanda ya isa yamaka haka, malam yafad'a yana qara godewa ubangiji, kwanansu malam uku ah Kano sukaso su koma amma abuu ya hanasu yache saisunyi ko wata d'aya nerh tareda su, hakanan suka haqura suka zauna, yanayin yanda ake kulawa dasu har kuka malam yakeyi saboda iya rayuwarshi beta6a tunanin ze gamuda jindad'in rayuwa kamar wanda yake chiki yanxu bah....
Azaman dasukeyi ah kano achan KT kuma abuu yasa an ruguje gidan kaka dana malam yasa ana Gina musu wani sabo, dukda chewar gidan kaka gidan bulo nerh amma saida abuu yasa aka rugujeshi aka chanja mishi fasali, hakama gidan su malam, tas aka rushe ginin qasar dake wurin aka tamfatsa musu gida nagani na fad'a daidai da yanda zasu iya amfani dashi, duk wannan abun sukansu basusan me ake chiki bah, shikuma abuu saboda ginin yaqarasa ma yasa yache su jinkirta tafiya, dayake ma anzuba kudi sosai wurin ginin gidan hakan yasa aikin yake sauri sosai.....
Kullum gaba d'ayansu suna tare ah wuri d'aya suna hira, hirar shekara da shekaru sukeyi ah tsakaninsu irin wadda basu ta6a yi bah, da rana duka tana tareda yan uwanta, da daddare kuma ad'akin ummi take kwana, ummi ko bacchi bata iya yi saita tashi tayita kallan shukuriyya, idan kuwa bacchi yaso d'aukarta saidai tayishi tana riqeda hannun shukuriyya, aranta tanajin kamar idan batayi hakan ba shukuriyya zata iya qara tafiya tabarsu......
Ranar wata Friday bayan sungama chin abinchin rana ummii tachewa yaranta dasu umma suxo suje su zagaya gidan su ganshi, kai tsaye apartment d'insu zarah suka nufa, suna zuwa bayan sun hau sama suka bud'e part din dake kallan na zarah suka shiga
"Nanne part dinki shukuriyya"
Ummi ta fad'a ( sunanda suke kiranta dashi kenan yanxu, domin sunche lallai shine sunan da ya chanchanchi sudunga kiranta ba kibdiyya kamar yanda suka saka mata bah)"Gaba d'aya shukuriyya was speechless da abunda tagani, kallan umma tayi sannan ta kalli mashkur wanda shima yake kallanta, d'akin gaba d'ayanshi achike yake da hotunan ta na yarinta, harma take ganin kamar babu wani Abu daxa'a iya sakawa ah d'akin saboda yanda aka chikashi, d'akin yayi matuqar tsaruwa kamar akwai mutum achikinshi
"Wannan shine d'akinki shukuriyya, duk gidan damuka zauna bama ta6a ginashi batareda mun ware miki muhallainki bh, saboda bamu ta6a fitarda ran chewar zamu ganki bah"
Umma tafad'a tana matsar kwallaQarasawa shukuriyya tayi kusada wani hoto ajikin d'akin sannan taga exactly sarqar da umma tabata ajikin hoton, juyowa tayi chikin kuka ta rungume umma, daqyar aka rarrasheta sannan tayi shiru, bayan sungama tattaunawarsu ah d'akin suka wuche chan baya apartment d'in haiydar, wurin babba nerh me girman gaske, mamakine ya ishesu yanda hotunan haiydar suke maqil achikin d'akin tundaga yarintarshi har zuwa sanda yabar gida, da alama daman chan mutanen gidan masu aqidar d'aukar hoto che, shi mamakin haiydar ma be wuche yanda suka killache wurin bah, sannan duk wad'annan shekaru basu fitarda ran samunsu bah, sosai abun yadunga bashi mamaki harya sakashi kuka me chikeda murna....
Bayan su malam sun chika wata d'aya agidan aka had'amusu shatara ta arziqi sannan gaba d'ayansu suka rakasu har gida tareda kaka, gidansu malam aka fara nufa, ganin yanda komai ya chanja yasa suka tabbatar da chewar su abuu nerh sukayi musu wannan aikin, godiya me tarin yawa sukayi musu harda kuka, bakomai kawai abuu yake chewa, ai sune da godiya da ake riqemusu yaro, chikin gidan suka shiga bayan sungama koke kokensu, komai an zuba musu agidan, tundaga kan sutura harzuwa kayan abinchi, sannan daxasu tafi suka d'auka kud'i me yawa suka basu, sunji dad'i sosai sannan suka qara godewa juna sukayi addu'ah sannan suka tafi gidan kaka,,,
Sosai shima suka qara mamakin chanjawar da gidan yayi, sanin chewar sune suka aikata hakan aka qara musu godiya sosai,,,, kaitsaye KD suka wuche, madadin su wuche su shiga layin gidansu Abba sai sukaga anshiga bayan layin, suna zuwa aka bud'e wani tamfatsetse gida safe content me matuqar kyau, motochi biyu nerh achikin gidan masu numfashi, chikin gidan suka shiga kai tsaye, komai na alatu an zubashi achikin gidan, furniture's masu raida lafiya aka zuba, bayan sun zauna sun huta abuu yabawa Abba mukullin gidan yache nashine har abada, shukuriyya har kuka saidata qarayi awurin na dad'i sannan taje ta qara rungume umma, murna sosai sukayi da wannan alherin sannan abuu ya kalla mashkur ya miqa mishi keys guda biyu sannan yache
"Wad'annan duka naka nerh, d'aya ah KT d'aya kuma ah kano nan kusa da mu, bansani ba ko zakaso chigaba da zama ah kusada qanwartaka, idan zaka zauna ah Kano ga keys nan idanma dai ah KT nerh ga keys nan, duka naka nerh halak malak, mashkur was speechless da abunda yaji, dukda chewar shi daxasu mayarda komai yazama labrinsu be fito ba na chewar shukuriyya ba qanwarshi bache bah haka yafiso, amma babu yanda zeyi da qaddara, hakanan ya kar6a shida shukuriyya sukayita musu godiya, sun dad'e kafin sukayi shirin tafiya, haniff da hanifah chewa sukayi baxa'a tafi musu da shukuriyya bah, hakan yasa abuu yachewa Abba kodai zai basu yaranne, abba kam chire kunya yayi yache idan yabasu yaran kuma ai shikenan bashida wasu, idan hutu yazo dai zasu dunga kawo musu ziyara, abuu yache gaskiyane wannan, itama shukuriyya dandai aure takeyi gidan mijinta zata koma nerh, amma da tabbas bazamu kar6eta daga hannunku bah.....
Dahaka sukayi sallama suna fatan sauduwar alkairi.....
Shukuriyya tariga ta sanar wada abuu yanda akayi suke zaune achikin gidan dasuke da haiydar, ta sanar mishi da chewar mashkur nerh ya bar mata gidan halak malak, sannan ta sanar dashi 6oyayyen dalilin mashkur na mallaka mata gidan dakuma dalilin daya fito musu dashi ya sanar dasu, hakan yasa abuu yakejin chewar ze iya mallakawa mashkur duk wata dukiyarsa daya mallaka domin irin gudummawar daya bawa shukuriyya.......
MEERAH
