49

881 71 4
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳





Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘



4⃣9⃣



                   

Yana tsaye ah qofar gidan, be fita ba sannan itama ya hanata fita, zanchen zuchi yayi for some minutes kafin ya tayarda motar tashi yajuya yabar qofar gidan batareda sun shiga bah, itakuwa shukuriyya baqaramun dad'i hakan yamata bah, daman tun daxu zuwa gidansu sofie yafitar mata aranta, gudu yadunga yi kamar daxu har suka iso gida sannan yafiche daga motar, itama batareda tache mishi uffan ba tafita daga motar, ko chikin gidan nasu bata shiga ba ta nufi gidansu humairah....

tanashiga taje ta gaisheda mamansu sannan ta tambayi humairah d'in, akache mata tana kitchen, batayi wani mamaki sosai ba dan daman ta fahimchi qarya tayi mata daxu, tana shiga kitchen d'in kuwa taganta tana dafa indomie ga earpiece nan ah kunnenta tanajin music, ko shigaowar shukuriyya d'in bataji bah, saikawai ji tayi an zare mata earpiece d'in, tana jiyowa taga shukuriyya, sosai tad'an ja baya ah d'an tsorache dan batayi tsammanin ganinta ah yanxu bah, duburburchewa tayi kalar tsoro da rashin gaskiya sannan ta fara kame-kame, itadai shukuriyya tsayawa tayi kawai tana kalanta, saboda tasanta in and out, ganin humairah tayi Shiru batache komai bah yasa shukuriyya qarasawa daf da ita sannan tache

"Humairah fad'amun, meke faruwa?"

Shiru humairah tayi batache mata komai ba, ganin hakan yasa shukuriyya nufar qofar kitchen d'in dan fita, dasauri humairah tariqota tajuyoda ita da sauri yayinda hawaye yake zuba ah idanunta, mamaki ne sosai afuskar shukuriyya

"Meyasaki kuka kuma, daga tambayarki?"
Shukuriyya tafurta da mamaki qarara afuskarta

"Its a long story shukuriyya, zamuyi maganan idan mun zauna, yanxu babu lokachi"

"Its OK!! Kidaina kukan"
Shukuriyya tafad'a tana goge mata hawayenta, juye indomie d'in tayi sannan suka fito parlour, babu yanda humairah batayi da shukuriyya kan ta tsaya tachi ba amma tache ta qoshi, hakanan humairah ta qyaleta, itakuma tamata sallama ta tafi, tache mata anjima zata shigo dan suqarasa shirinsu, saboda gobe ne za'ayi biki, jibi ad'aura aure akai amarya......

      Shukuriyya na shiga gidansu ta hangi mashkur ah compound yana making call, da alama da sofie yake magana, itadai tana mishi kallo d'aya ta d'auke kai tayi chikin gida abunta, tana shiga ta tarar da su kaka har sun iso da sauran yan'uwansu na katsina, dasaurinta ta qarasa ta fad'a jikin kaka tanata murnar zuwanta, kaka kuwa sai tsokanarta takeyi wai batajin kunya za'ayi aurenta tanata zumud'i, itadai sai rufe fuska takeyi kalar kunya, sannan tagaisheda kowa awurin tanufi dakinta, tana zuwa ta tarar dasu hanifah dasaura yan'uwansu dasuke sa'anninta nerh ah dakin, gaisawa tayi dasu kawai tafito, ita sam bata qaunar hayaniya ah rayuwarta, gashi duk sunchika dakin da kayayyakinsu dasuka xo dashi, dakin umma ta nufah dan taje tayi zamanta, tana shiga ta tarar da ita da baqi itama, gaishesu kawai tayi ta fito sannan ta nufi compound, daatayi tunanin komawa gidansu humairah saitaga maghriba ya kusa, sai kawai tayi zamanta achikin gidan ta wurin parking lots d'insu, motan mashkur nerh kad'ai ah wurin, sai kawai ta d'auka kujeran roba takai wurin tayi zamanta,,,,

      kiran layin haiydar tayi dan taga missed call dinshi tun daxu, waya sukasha sosai yanata zumud'in amaryarsa, saida akayi kiran maghriba sannan suka katse ta nufi chikin gida tayi sallah, tana idarda sallah humairah tashigo chikin gidan dan haka suka fito waje sukayi zamansu ah gurin data zauna daxu, planing yanda gobe xai kasanche suka fara, dasauran issues na bikin, maganan makeup daman batada Matsala dashi, dan sofie makeup artist che babba achikin garin kaduna, tanada shagon makeup dinta ah state road mai taken _*sofie AB saloon*_
Achikin shagon babu abunda batayi, makeup, saloon, heina, gyaran jiki, dasauran abubuwan dasuka shafi mata, amma ba'ita takeyi bah, tanada yaranta dasuke yi mata, just that takanje idan tana free itama tayi, amma sai manyan costumers takeyiwa, wurin upstairs nerh, ah sama nerh ake wadannan events d'in, aqasa kuma anan nerh wurin hotanta yake me taken _*sofie AB photography*_ ,,,,,,

     So already sofie tayi alqawarin yi musu komi daya shafi makeup da photo, kuma dakanta tayi alqawarin yi, hakan yasa suketa lissafin yanda zasuyi, wayar shukuriyya che tayi ringing yayin da suke hirar tasu, tana dubawa taga mashkur nerh, dagawa tayi ta kara akunnenta batareda tache komi bah, "kikawo mun abinchi" mashkur yafad'a sannan yayi hanging, miqewa tayi tareda d'aukan excuse awurin humairah sannan ta nufi chikin gida, shinkafa tasamu da miya dan haka ta d'iba mishi sannan tamishi setting ah babban tray ta d'auka ta nufi dakinshi, tana zuwa ta ganshi ah zaune ah kan gado, sallama tayi ya ansa sannan batareda tache mishi komai bah tajuya ta nufi hanyar fita

     "Are u mad at me?"
Mashkur yafad'a ah hankali, yitayi kaman bataji shi bah, qara maimaitawa yayi sannan tache mishi "ah'ah"
"Gashinan kinata d'auke mun kai"
Yafad'a yana qarasowa inda take, batache mishi komi ba tayi Shiru tana kallan qasa

Kama hannayenta yayi yana kallan idanta sannan yache
  "Its owk!! Am sorry, I don't mean what I said the other tym,,,,, sorry"
Yafad'a camly

Shiru tayi sannan tache
"its owk fah!!!, ni daman ba fushi nakeyi bah"

"Shikenan,,, xaki iya tafiya, saida safe"

     "Gued nyt"
Shukuriyya tafurta sannan takoma compound d'in, tana xuwa suka chigabada hirar su, sai wurin goma sannan humairah ta nufi gidansu, itakuma shukuriyya tayi chikin gida ta nufi dakin umma tayi kwanchiyarta, dan baxata iya kwana adakinsu bah...

     Washegari suka fara events d'in bikin, kamu akayi me rai da lafiya ah event centre, amarya shukuriyya tasha kyau kamar ba itaba, haka akayi events d'in chikin jin dad'i aka watse, ango bexo bikin ba, sai da suka koma gida sannan yaje wurinta suka gaisa sukasha hira sunata d'aukin juna,,,,,

Su mashkur kam sai shige da fiche akeyi ana auren qanwa, yakasa zaune yakasa tsaye sai zirga zirga yakeyi, saida ya tabbatar komai na buqatar gobe is safe sannan hankalinshi ya kwanta, bayan ya sallami baqinshi yanufi d'akin umma dan yanaso zasuyi magana gameda goben, yana shiga yaga bata d'akin, shukuriyya che kawai da hanifah sai haniff, duk sun zagaye shukuriyya sai alhinin tafiyarta sukeyi sunata mata hira itakuma tana tayasu, tambayrsu inda umma take yayi sai sukache tana d'akin abba, daga haka yache sutashi subashi wuri,,,,,
    Qarasawa yayi kusada shukuriyya yazauna agefenta sannan yafara tsokanarta, daga qarshe kuma yaqare da yimata wa'azi, fad'a yamata sosai irin wanda beta6a mata bah, tun tana kukan har tafara d'aukewa sannan yahaqura ya qyaleta, ya lallasheta sannan yabar dakin.....

    Washegari da safe dubban jama'a suka shaida d'aurin auren shukuriyya da haiydar, wanda aka d'aura ah kofar gidansu dake KT,,,,,
   haka akayi taro aka watse, ango da abokanshi suka shiga gidansu amarya akasha hotuna, fuskar amarya tayi jawur da ita saboda tsabar kuka da tayi, bayan sun gama hotuna suka fiche suka bar gidan, amarya dasu humairah suka koma chikin gida abunsu,,,,,,

Da daddare misalin qarfe 7 aka kai amarya gidanta, mashkur nerh da kanshi yasakata amota yakaita har d'akinta, bayan jayayya da akayi da ita kafin ta yarda ta fito daka gidan, dan kuka tadunga yi kamar ranta ze fita, sai ka rantse wannan shine aurenta na farko, daqyar aka fitar da ita daka gidan...

babu wanda ya zauna daka chikin qawayenta, ana kaita zuwa wurin 8 kowa ya watse akabar amarya shukuriyya daka ita sai halinta achikin gidan aurenta......

                      🌳🌺😘

Finally, shukuriyya anzama mallakin haiydar,,,, yan black stomach how market 😂😂😂

    Taxama, taxama, taxama,,, taxama d'auko Riga, taxama d'auko buta, taxama.......😂😂









*MEERAH*

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now