09

1.9K 116 6
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳


Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘


0⃣9⃣

Bawani biki akayi bah dan daman koda babu wannan *QADDARAR* data sameta ita ba mai san yawan bidi'ah bache, dan haka walima kawai akayi ranar juma'ah, aka daura aure asabar da safe qarfe goma kowa ya shaida auran
*MARYAM IBRAHIM AMINU* *(SHUKURIYYA)*
Da
*KAMAL YUSUF*
akan sadaki naira dubu hamsin,
da yamma umma tayi nata wunin da daddare aka dauki amarya sai gidan uncle kamal.

🌳🌺😘

(ni meerah nache wasan yar buya ta qare lolx)
Ankai amarya gidanta me raida lafiya kowa sai admiring kyan gidan yakeyi, kowa ya bude bakinshi kaji yache kamal yayi qoqari, wadanda sukaje gulma mah dae sunganewa idanunsu, haka akayita kaikawo ah gidan amarya har kowa Yakama hanyar gidansa yarage daga shukuriyya sai humaira ah gidan, humaira sai tsokanarta takeyi, itakam dai Shiru tayi mata dan takasa che mata komai, she can't believed an daura mata aure da uncle Kamal dinta, zuwa wani lokachi saiga kiran hamza yashigo wayan humaira, dan qaramun tsaki taja, shukuriyya ta kalleta tache
" ya akayi nerh?"
Tache
"ya hamza nerh wlh yake kira, nasan chewa zeyi nafito mutafi"
tanagama fadar haka ta dauki wayan ta kara ah kunnenta
"malama kifito mu tafi gida kinji koh"
abunda yafada kenan yayi hanging call din, mayafinta ta dauko tache
" toh amarya nizantafi gida"
shukuriyya tache
" ke humaira yanzu bazaki jira uncle kamal din yazo bah?"
humaira tajuyo ta kalleta tache
"wani uncle Kamal nerh zanjira yazo? Idan yazo gurina zaizo? Inache kinajin wannan dan mijin naki yakirani yache infito in tafi, da ache kinaso na zauna ai da kinkarbi wayar kin bashi ansa"
shukuriyya tache
"kedai kinshiga uku da masifah"
itakam humaira hanyar qofah tanufah tana chewa
"sai gobe zaki ganni da asuba, achi amarchi lfy"
tafada hadeda rufo mata qofar dakin, tana zuwa tashiga mota suka kama hanya sai Gida .


Yarage sai ita kadai ah gidan, wuraren qarfe tara da rabi tashiga toilet tayi wanka sannan tafito, tasa kayan barchinta masu kauri ta daura hijab har qasa sannan ta kwanta barchi.

guraren goma yashigo gidan, tuntuni yaketa so yataho amma abubuwa sun masa yawa, sai yanzu yasamu yagama clearing din komai, yana shiga gidan dakin shukuriyya yanufa, yanazuwa dakin ya tarar harta yi bacchi, zama yayi agefen gadon yana qare mata kallo, saiyaga ta chanja masa, ta qara kyau sosai, wani saban santa yaji yana fisqarsa, yanajin santa sosai ah chikin zuchiyarsa, har yanzu yarinyache ita sosoi, qwalla che tafito masa ah idanunsa, " Allah ka la'anchi Wanda ya lalata *rayuwar* matata,, ameen"
yafada azuchiyarsa, kwanchiyarta ya gyara mata ya mata addu'ah sosai ya kashe light din dakin sannan yafita daga dakin yarufo mata qofah, kitchen ya wuche kai tsaye yasaka madarar da yataho da ita ah fridge, kazar mah haka, saiya dauki wadda zaichi kawai yasa ah plate yakoma falo yazauna yanachi, zai iya chewa yafi kowa sa'a ah duniya tunda Allah ya mallaka masa shukuriyya, yagama chi ya wanke kwanan sannan yadawo yakwanta ah falo yana tunane-tunane ah chikin zuchiyarsa, har barchi yakwasheshi besani bah .

🌳🌺😘

Da asubah yafarka yakoma dakin shukuriyya yaga har yanzu barchi takeyi, aransa yache lallai tagaji dayawa, tashinta yayi sannan yanufi masallachi, ita kuwa saida ta farka mah sannan ta tuna ah ina ta kwana, gaba daya ta manta mah andaura aurenta sai yanzu data ganta ah wani gidan daba nasu bah...
(ni meerah nache kiji tsoran Allah fah lolx )

tashi tayi tayi alwala tayi sallah sannan takoma bacchi dan tayi matuqar gajiya, daman sabgar biki ta gaji haka, da uncle kamal ya dawo saiya shigo dakinta ganinta yayi tana barchi sai kawai ya koma dakinshi yazauna yanata tufka da warwara, zuwa qarfe 7 shima yafito daga dakin, kitchen yashiga ya fara ferayar dankali, yasoya shi sannan yasoya kwai yazuba su ah container, sannan yadafa tea yazuba ah flask, yadawo yajera akan dining, daman akwai set na cups da spoons akan dining table din, plates ya dauko da butter sannan yadauko madara Milo bournvita dasauran kayan tea yadaura duka ah kan dining table din, sannan yafita yasiyo bread ah kanti yadawo yadaura akan table din, sannan yakoma kitchen ya wanke duk kayan daya bata ya share kitchen din yayi mopping dinshi sannan yarufo kofar....


yakoma dakinshi yayi wanka yafito ya dauki 3quarter wando ash, sannan ya dauko red din Riga da zanen ash ajiki ya saka, ya dauki turare ya feshe jikinshi sannan yadawo parlor, ya dauko room freshener ya feshe parlorn ko ina tsaf-tsaf, Sannan yakoma yazauna yakunna TV yana kallo yana jiran fitowarta....
wuraren tara da rabi ta farka, tashiga toilet tayi wanka tafito, tasaka doguwar Riga, bata daura dan kwali bah, light make-up tayi sai tasaka qaramin baqin mayafi tadaura shi akanta yabiyo ta wuyanta sannan ta yafa shi bayanta, ta feshe jikinta da turare, har zata zauna ah dakin sai taji bara ta fita taga gidan, tana murda kofar dakin kamal ya juyo da kallansa kan qofar, tana fitowa suka hada ido batasan sanda tajuya ta banko kofar bah, tajingina da ita ta chiki tanata haki kaikache gudu tayi...

( ni meerah nache kamal din da ake so shi ake gudu yau)

dariya taso bashima ganin yanda ta rufo qofar da hanzari, ahankali yataso daga kan kujerar yazo bakin kofar yatsaya, knocking yayi sannan yatura kofar, tana tsaye agurin, murmushi yayi sannan ya qarasa daf da ita ya tsaya
"ina kwana "
yache mata ahankali, ita kanta saida taji kunya ganin yarda ya gaisheta, batache komai bah ta sunkuyarda kanta tana wasa da yan yatsunta, matsowa yaqarayi daf da ita har yanajin sautin numfashinta, hannuwanta da take wasa dasu Yakama da hannunsa, wani irin electric spark sukaji gaba dayansu, sharewa yayi yache
*you are highly welcome to your house"
tayi masa Shiru batache komai bah
" fushi kikeyi dani ne?"
yatambaya, girgiza masa kanta tayi alamar "ah'ah"
yache "to menene?"
nan ma shiru bata tanka Shiva
" nayi miki laifi?"
ta girgiza kanta
"kindaina sonane?"
nan mah tagirgiza kanta
"oh Allah"
kamal yayi exclaiming,
"kiyimun magana mana shukuriyya,, your silent is killing me"
yafada ahankali, batache dashi komai bah haryanzu, sai kawai Yakama hannunta suka fito falo, yajawo mata kujerar dining yazaunar da ita sannan ya dauki cup yahada mata tea yamiqa mata, yazuba nashi ah cup shima sannan ya dauki plate yazuba chips din da egg, ya ajje agabanta ya dauko fork ya saka mata ah plate din,,, gani yayi taqi chi sai kawai yadauka yakai mata bakinta, "haaaa" yache mata alamar ta bude bakinta, amma taqi budewa
" opeen mana"
Yaqara fada sannan ta bude bakin yasamata chips din, sannan tafara chi, haka yadunga bata harta qoshi, daya qara mata ne taqi karba, yache "kin qoshi?" ta daga masa kanta alamar eh, yache "owk!! kisha tea din"
haka tadaga cup din tadunga sha harta shanye sannan ta ajje, yache
"are u OK?"
Ta dadaga masa kanta .

( ni meerah nache kalli yanda yake treating dinta kaman wata baby)
miqe wa tayi jiki ah sanyaye tanufi dakinta, kamal yabita da kallo harta shiga dakin sannan shima yayi breakfast din, yahada kwanukan yakai kitchen yafara wankewa...
ita kuwa tunda tashiga dakin take kuka, haushin kanta takeji sosai, meyasa taqi yimasa magana? uncle kamal be yi deserving wannan abunda tayimasa bah, why? take tambayar kanta
", ba laifina bane bah, laifin wanchan mutumin ne, shiya lalata mun komai, tanajin nauyin uncle Kamal abusa abunda yafaru da ita, haka ta dunga kuka harsai da tayi mai isarta, datagama kukan ta kwanta agurin tayi barchi.

🌳🌺😘

MEERAH

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now