25

1.6K 91 4
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳





Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘






2⃣5⃣




Washe gari haka shukuriyya ta tashi fuska duk ah kumbure, kana ganinta kasan tachi kuka ta qoshi, ah takure ta dunga yin ayyukanta na chikin gidan saboda yanda takejin jikinta, tana gamawa ta koma daki tayi kwanchiyarta, saboda wani irin zazzab'i datakeji, gashi jikinta very week, ga wani irin tari datakeyi kamar zata amayar da hanjin chikinta, left arm d'inta kuwa kamar ba'a jikinta yake bah, itada kanta ta rasa gane meyake damunta.

Tarin datakeyi nerh yatashi kaka daka barchin hantsi datakeyi, fitowa tayi ta tasata agaba ganin yarda take tayin tarin, jiqe-jiqen magun-gunan gargajiya tayi mata, saida shukuriyya tasha jiqon sannan tafara jin daidai, dakanan kuma wahallalen bacchi ya dauketa.


Yau kimanin sati uku kenan raban shukuriyya da haiydar, tun bayan had'uwarshi da mashkur be qara zuwa gidan bah, abun duniya duk ya ishi shukuriyya, bata da aiki kullum chikin tunani take, tunanin kuma baya wuche na kamal da haiydar, ita kanta wani lokachin haushin kanta takeji idan tana tunanin haiydar, ah nata ganin menene abun tunaninshi, tinda mutunchi sukeyi kawai, kuma yanxu an dakatar da ita, kullum batada wani yunqurin daya wuche taga ta daina tunanin haiydar, amma sam abun ya gagara, saima abun dayayi gaba, ita aganinta basuyi sabon da har idan baya kusada ita xataji babu dad'i bah, amma saigashi ta fuskanchi akasin haka.

kaka da kanta taso ta fahimchi akwai wani abun dayake damunta tun bayan zuwan mashkur, koda ta tambayi shukuriyya chemata tayi babu komai, dan haka ta kyaleta, dan tasan yarinyar da shegen zurfin chikin tsiya.


🌳🌺😘

Ah bangaren haiydar kuwa tunda yabar qofar gidan kaka zuchiyarshi take zugi, zanchen zuchi kawai yakeyi, "shin wannan wanene?" Kodai saurayintane, qila kuma d'an uwantane tunda naaga yashiga chikin gidan, toh kuma ai ana soyayya da d'an uwa, daka gani ma saurayintane, saboda irin mugun kallon danaga yanayi mun, "mtswe" wani uban dogon tsaki yayi ah fili, saboda tuna fuskar mashkur dayayi, "wani mummuna mah dashi"

_ni meerah nache kuji fah haiydar da qarfin hali, duk kyan mashkur ache mishi mummuna_

Wani irin zafi yakeji ah chikin zuchiyarshi saboda tuna irin yarda shukuriyya tadunga rawar jiki data ganshi, "duk yanda akayi saurayintane, kuma daka gani tana sonshi, saboda yanayinta ya nuna hakan"
achikin zuchiyarshi yake wannan tunanin, ah fili kuwa wani irin huchi yakeyi saboda yanda zuchiyarshi take mishi quna, tunanin daya dunga yi kenan harya je Gida.....

Kwana haiydar yayi da tunanin shukuriyya ah ranshi, tunanin dayake yi kuwa shine daman shukuriyya bata fahimchi chewa yana santa bane bah, dahar take sauraron wannan, koda yake da alama tun tana garinsu yake santa, kaiii!!!, amma kuwa indai ta tabbata shukuriyya tanada saurayi to tawa ta qare, tabbas da guy dinnan yayimun shigo-shigo ba zurfi, anya kuwa zan jure rashinta akusa dani, kodai laifinane daban gaya mata bah, dole inje infad'amata ina santa, idan yaso komai zai faru saiya faru.

Tunanin dayake tayi kenan achikin zuchiyarshi, awani lokachin kuma haushin shukuriyya d'in yakeji ganin yarda tadunga rawar jiki dataga guy d'in.
Da wannan tunanin haiydar ya wuni, washe gari ko qofar gida bai fita bah, ah chikin gida ya wuni da tunanin shukuriyya fal ah ranshi.



Kwana uku da yin abun be qara waiwayar inda take bah, dafarko yayi tunanin yaje yasameta suyi magana, amma daga baya saiyaga babu point wurin yin hakan, saboda he is not her type, infact kwata-kwata basu dache bah, shi bekasanche daka chikin irin mazan dayakamata ache ta aura bah, saboda ita d'un ta kasanche ta fito daka gidan rufin asiri, unlike him, kuma daka ganinta y'ar boko che sosai, dukda bai san matakin karatunta bah, amma yanayinta ya nuna hakan, kuma ba lallai tayarda da soyayyarshi bah, wataqil amatsayin aboki kawai ta daukeshi, baya tunanin zata iya qaraa mai wani matsayin akan wannan, kuma koda ache ta yarda zata aureshi daxarar taji asalinshi yasan ah wurin za'ayi quiting relationship d'in, haka kurum ta tafi tabarshi da qunar santa ah zuchiyarshi, kuma koda ache gigin soyayya yasakata aminchewa da auranshi, yasan chewar gigin son zuchiya bazai sa iyayenta su yarda ta aureshi bah, da wad'annan qananun tunanin yayi making mind dinshi kan ya rabuda ita kawai, gudun kar yasaka rayuwarshi ah matsala, tunda daman bawani Santa yakeyi bah, kawai dai tana burgeshi nerh.

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now